Hukumar Ilimin Bai-Ɗaya ta Jihar Neja (N-SUBEB) ta ce za ta dasa bishiyoyi a makarantu 150 da ke faɗin jihar, a wani mataki na rage illolin sauyin yanayi da zaizayar ƙasa da ke barazana ga wasu makarantu.
Shugaban hukumar, Dakta Liman Alhaji Ibrahim, ya bayyana hakan ne yayin wani horo na matakin jiha kan shirin Greening Schools and Climate Change Initiatives (GSCCI) da aka gudanar a zauren taro na N-SUBEB da ke Minna.
Dakta Ibrahim, wanda Babban Memba na II a hukumar, Hon. Muhammad Mudi, ya wakilta, ya ce nufin shirin shi ne samar da makarantu masu aminci da tsafta, tare da inganta yanayin koyo da koyarwa da kuma rage matsalolin muhalli da al’ummomi ke fuskanta.
Ya ce makarantu da dama a jihar suna fuskantar barazanar guguwar iska, zaizayar ƙasa da tsananin zafi, waɗanda ke kawo cikas ga harkokin ilimi tare da lalata gine-ginen makarantu.
Shugaban ya bayyana cewa shirin GSCCI bai taƙaita ga dasa bishiyoyi kawai ba, domin ya kuma ƙunshi shigar da ilimin sauyin yanayi cikin tsarin koyarwa a makarantun firamare.
Ya ce an shirya horon ne domin bai wa jami’an ilimi, shugabannin makarantu da jami’an kula da muhalli ilimi da dabarun da za su taimaka wajen aiwatar da shirin yadda ya kamata a matakin ƙananan hukumomi.

Ya buƙaci mahalarta horon da su ɗauki shirin da muhimmanci, tare da tabbatar da cewa an kula da bishiyoyin da za a dasa a makarantu har sai sun yi ƙarfi kuma sun girma yadda ya kamata.
Dakta Ibrahim ya ƙara da cewa hukumar ta N-SUBEB za ta ci gaba da haɗin gwiwa da Ma’aikatar Muhalli ta Jihar Neja, Ma’aikatar Aikin Gona, abokan hulɗar cigaba da sauran hukumomin da abin ya shafa domin tabbatar da nasarar shirin.
Tun da farko, sai da Sakatariyar Zartarwa ta Hukumar Ilimin Bai-Ɗaya ta Ƙasa (UBEC), Dakta Aisha Garba, ta bayyana horon a matsayin wani muhimmin mataki na sauye-sauyen da Gwamnatin Tarayya take aiwatarwa a fannin ilimi domin sake fasalin makarantu yadda za su iya fuskantar ƙalubalen muhalli da sauyin yanayi.
Dakta Aisha Garba, wadda Ko’odinetan UBEC na Jihar Kebbi, Dakta Aliyu Cheche, ya wakilta, ta ce tsarin ilimi ya kamata ya samar wa ɗalibai ilimi, ƙwarewa, ɗabi’u da halayen da za su taimaka wajen gina makoma mai ɗorewa da kuma jure wa illolin sauyin yanayi.
Ta buƙaci jami’an ilimi na jihohi da ƙananan hukumomi, masu kula da shirin a jihohi, shugabannin makarantu da masu horaswa da su yi aiki kafaɗa da kafaɗa da UBEC da tawagar fasaha domin tabbatar da nasarar aiwatar da shirin a faɗin ƙasa.
Horarwar ta samu halartar jami’an da ke kula da shirin daga ƙananan hukumomi 25 na Jihar Neja.
A yayin horon, an koyar da mahalarta dabarun dasa bishiyoyi da kula da su, hanyoyin daidaitawa da sauyin yanayi, da kuma dabarun tabbatar da ɗorewar muhalli a makarantu.







