• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya rattaba hannu kan dokar tashoshin jiragen ruwa ta 2026

WAKILIN MU by WAKILIN MU
August 14, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Cika shekara uku a mulki: Tinubu ya ce sauye-sauyen tattalin arziki sun fara haifar da ɗa mai ido
Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan Dokar Hukumar Kula da Tattalin Arzikin Tashoshin Jiragen Ruwa ta Nijeriya (NPERA) ta shekarar 2026, wanda hakan ya ba Majalisar Kula da Masu Safarar Kaya ta Nijeriya (NSC) cikakken ƙarfin doka wajen gudanar da ayyukan sa ido da daidaita harkokin tattalin arzikin tashoshin jiragen ruwa.

Babban Sakataren NSC, Dakta Pius Akutah, shi ne ya bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a soshiyal midiya, inda ya gode wa Tinubu bisa sanya hannu kan dokar.

Masana harkokin ruwa sun ce dokar ta buɗe sabon babi wajen samar da cikakkiyar hukuma mai kula da harkokin tattalin arzikin tashoshin jiragen ruwa, wanda zai samu ikon ɗaukar mataki kan masu gudanar da ayyukan tashoshin da suka karya ƙa’idoji.

Masanin harkokin ruwa, Dakta Eugene Nweke, ya ce dokar ta kasance sakamakon ƙoƙarin da aka shafe shekaru ana yi tun bayan bai wa kamfanoni damar gudanar da tashoshin jiragen ruwa na Nijeriya a shekarar 2006.

Ya ce a cikin 2014 Gwamnatin Tarayya ta bai wa NSC matsayin mai kula da harkokin tattalin arzikin tashoshin jiragen ruwa na wucin-gadi, yayin da ake jiran samar da cikakkiyar dokar da za ta ba da wannan iko.

A cewar sa, kafin sanya hannu kan sabuwar dokar, NSC tana gudanar da wasu ayyukan sa ido bisa manufofin gwamnati da kuma wata sanarwar gwamnati ta shekarar 2015.

Ya ce sabuwar dokar ta bai wa hukumar da za ta gudanar da aikin ikon kula da kuɗaɗen fito da kaya, farashi da caji, gasa tsakanin masu samar da ayyuka da kuma bayar da lasisin gudanar da ayyukan tashoshin jiragen ruwa.

Haka kuma dokar ta tanadi hanyoyin warware taƙaddamar kasuwanci da ka iya tasowa a harkokin tashoshin jiragen ruwa.

Tags: Bola Tinubudokajiragen ruwaNPERAtashoshin jiragen ruwa
Previous Post

Hukumar ilimi ta N-SUBEB za ta dasa bishiyoyi a makarantu 150 a Neja

Next Post

Tinubu na so a yi zaɓen Osun cikin lumana da adalci

Related Posts

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’

November 25, 2026
Muna samun nasarori a tsaro, ilimi da ababen more rayuwa – Tinubu 
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya ware Naira biliyan 450 domin tallafa wa manoma 500,000

November 22, 2026
Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40

November 19, 2026
CBN ya naɗa kamfanoni takwas domin kula da fitar da ɗanyen mai da iskar gas
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN da NNPCL sun ƙulla yarjejeniyar ƙarfafa tattalin arziki da samar da kuɗaɗen zuba jari a ɓangaren makamashi

November 18, 2026
CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su

November 17, 2026
Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS

November 16, 2026
Next Post
Tinubu ya umurci ICPC da ta binciki ‘hukumar bogi’, ta gabatar da rahoto cikin kwana 30

Tinubu na so a yi zaɓen Osun cikin lumana da adalci

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!