• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Sunday, November 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ba mu da shirin ƙara kuɗin wutar lantarki – Minista

FATI ABDUL by FATI ABDUL
August 1, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Ba mu da shirin ƙara kuɗin wutar lantarki – Minista
Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe

Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe

Gwamnatin Tarayya ta musanta rahotannin da ke cewa tana shirin ƙara kuɗin wutar lantarki, tana mai jaddada cewa babu wani shiri na sauya kuɗin lantarki fiye da yadda yake a halin yanzu.

Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, shi ne ya bayyana hakan, inda ya ce gwamnatin Tinubu ta fi mayar da hankali kan inganta samar da wutar lantarki da kuma tabbatar da cewa masu amfani da wuta suna samun ingantacciyar hidima.

A cewar sa, daga cikin manyan manufofin gwamnati akwai tabbatar da cewa kowane mai amfani da wutar lantarki ya samu na’urar auna amfani da wuta (meter), tare da tabbatar da cewa ‘yan Najeriya suna biyan kuɗin wutar da suka yi amfani da ita kaɗai.

Ministan ya ce Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da duba hanyoyin da za su kare masu ƙaramin ƙarfi da marasa galihu daga duk wani nauyin da zai iya tasowa, tare da samar da tsarin kuɗaɗen da zai tabbatar da ɗorewar ɓangaren wutar lantarki.

Ya bayyana cewa gyaran da ake aiwatarwa a fannin wutar lantarki ba ya da alaƙa da siyasa ko yaƙin neman zaɓe, sai dai wani tsari ne da ake gudanarwa cikin haɗin gwiwa, tare da auna sakamakon da ake samu domin tabbatar da cimma manufofin da aka sanya a gaba.

Tegbe ya ƙara da cewa za a auna nasarar gyaran ne da irin sauye-sauyen da ‘yan Najeriya za su gani a rayuwar su ta yau da kullum.

Ya ce babban burin Gwamnatin Tarayya shi ne samar da ingantacciyar wutar lantarki da za ta wadatar da gidaje, ta bunƙasa masana’antu, ta jawo masu zuba jari, tare da tabbatar da cewa kowane ɗan Nijeriya ya amfana da ingantaccen tsarin samar da wutar lantarki.

Tags: farashiJoseph Tegbelantarki
Previous Post

Next Post

CBN ya ci tarar bankuna naira biliyan 1.69 saboda wasa da ƙorafe-ƙorafen kwastomomi

Related Posts

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’

November 25, 2026
Muna samun nasarori a tsaro, ilimi da ababen more rayuwa – Tinubu 
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya ware Naira biliyan 450 domin tallafa wa manoma 500,000

November 22, 2026
Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40

November 19, 2026
CBN ya naɗa kamfanoni takwas domin kula da fitar da ɗanyen mai da iskar gas
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN da NNPCL sun ƙulla yarjejeniyar ƙarfafa tattalin arziki da samar da kuɗaɗen zuba jari a ɓangaren makamashi

November 18, 2026
CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su

November 17, 2026
Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS

November 16, 2026
Next Post
Cikar wa’adin ƙarfafa jari: Yadda bankunan Nijeriya suka bazama tara Naira tiriliyan 4.6 a ƙoƙarin cika sharuɗɗan CBN

CBN ya ci tarar bankuna naira biliyan 1.69 saboda wasa da ƙorafe-ƙorafen kwastomomi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!