• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Al-Mustapha ya ƙaryata iƙirarin tsohon jami’in DSS kan mutuwar Abacha

ALI KANO by ALI KANO
July 25, 2026
in Labarai
A A
0
Gaskiyar yadda Abacha ya rasu, cewar tsohon jami’in DSS
Sabon littafin (a hagu), da kuma Janar Abacha

Sabon littafin (a hagu), da kuma Janar Abacha

Tsohon Babban Jami’in Tsaron marigayi Shugaban Mulkin Soja, Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha (mai ritaya), ya yi watsi da iƙirarin da tsohon jami’in Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), Dennis Amachree, ya yi game da yadda marigayin ya rasu.

Al-Mustapha ya bayyana iƙirarin a matsayin ƙarya, tare da yin kira ga ‘yan Nijeriya da kada su gaskata shi.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a gefen Taro na Uku na Tunawa da Janar Hassan Usman Katsina, wanda aka gudanar a Arewa House da ke Kaduna a yau Asabar.

Martanin nasa ya biyo bayan sake ɗaukar hankalin jama’a da littafin tarihin Amachree mai suna The Shadow Warrior ya yi. A cikin littafin, tsohon jami’in DSS ɗin ya gabatar da nasa bayanin kan abubuwan da suka faru kafin mutuwar Abacha a ranar 8 ga Yuni, 1998.

Da yake ƙaryata labarin, Al-Mustapha ya ce an ƙirƙiri labarin ne kuma bai yi daidai da abin da ya faru ba. Ya ce yana da hotunan bidiyon CCTV da suka ɗauki abin da ya faru, waɗanda a cewar sa za su iya ƙaryata bayanan da ke cikin littafin.

Sai dai bai yi ƙarin bayani kan bidiyon ba, haka kuma bai bayyana ko yana da niyyar fitar da su ga jama’a ba.

Ya kuma buƙaci ‘yan Nijeriya da su yi watsi da iƙirarin, yana mai cewa bai dace a yi zarge-zarge kan mutumin da ya rasu ba, domin ba zai iya kare kan sa ba.

Marigayi Janar Sani Abacha dai ya karɓi mulki bayan juyin mulki da ya yi a ranar 17 ga Nuwamba, 1993, kuma ya jagoranci Nijeriya har zuwa rasuwar sa kwatsam a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar 8 ga Yuni, 1998.

A lokacin, Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa shugaban mulkin sojan ya rasu ne sakamakon rashin lafiya da ta kama shi ba zato ba tsammani. Sai dai har yanzu yadda mutuwar sa ta faru na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin batutuwan da suka fi jawo ce-ce-ku-ce a tarihin siyasar Nijeriya.

A tsawon shekaru, tsofaffin hafsoshin soji, jami’an tsaro, jami’an diflomasiyya da ‘yan siyasa sun gabatar da mabambantan bayanai kan abubuwan da suka faru a sa’o’in ƙarshe na rayuwar Abacha, ta hanyar littattafai, hirarraki da sauran wallafe-wallafe.

Amachree, wanda tsohon Mataimakin Darakta ne a DSS kuma ya yi aiki a zamanin gwamnatin Abacha, ya sake tayar da wannan muhawara ne ta hanyar littafin sa, inda ya gabatar da nasa bayanin kan awannin ƙarshe na rayuwar marigayin.

Amachree ya yi iƙirarin cewa Abacha ya rasu ne lokacin da yake tarawa da wata budurwar ‘yar ƙabilar Ibo.

Littafin ya haifar da sababbin martani daga wasu tsofaffin jami’an gwamnatin Abacha, ciki har da Al-Mustapha, wanda ya sha bayyana cewa yana ƙaryata duk wani bayani da yake ganin ya karkatar da gaskiya game da marigayi shugaban mulkin sojan ko kuma abubuwan da suka faru a wancan lokaci.

Shi kan sa Al-Mustapha na daga cikin fitattun mutane masu jawo muhawara a tarihin siyasar Nijeriya.

Bayan rasuwar Abacha, an kama shi a shekarar 1999, sannan aka gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargin yunƙurin kashe fitaccen mawallafi Alex Ibru da kuma kisan Kudirat Abiola, matar marigayi Cif Moshood Kashimawo Olawale (MKO) Abiola, wanda ake ɗauka a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga Yuni, 1993.

Ya shafe fiye da shekara goma a tsare kafin Kotun Ɗaukaka Ƙara ta wanke shi tare da sake shi a shekarar 2013.

Tun bayan samun ‘yancin sa, Al-Mustapha ya ci gaba da kare gwamnatin Abacha, yana mai cewa yawancin zarge-zargen da ake yi wa marigayin da jami’an gwamnatin sa sun samo asali ne daga siyasa ko kuma ba su da hujjoji masu ƙarfi.

Tags: Dennis AmachreeJanar Sani AbachalittafiManjo Hamza Al-Mustapharasuwa
Previous Post

Gwamna Bago ya gana da ‘yan takarar APC da waɗanda suka faɗi zaɓen fidda gwani a Neja

Next Post

Related Posts

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura
Labarai

Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura

November 25, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa
Labarai

Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa

November 24, 2026
Next Post

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!