Rundunar Operation Haɗin Kai ta bayyana cewa ta wanke wani mutum da a baya aka ruwaito a matsayin wanda ake zargi da alaƙa da ’yan ta’adda, bayan bincike ya tabbatar da cewa ba shi da wata alaƙa da kowace ƙungiyar ta’addanci.
A cikin wata sanarwa da Muƙaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na Rundunar, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar a yau Alhamis, rundunar ta ce mutumin, mai suna Aboubakar Muhammad Zein-Nur, wanda aka fi sani da Houdairi, sojojin Bataliya ta 68 sun kama shi ne yayin wani samame na bibiyar bayanai bayan harin da aka kai a Cross Kauwa.
Sanarwar ta bayyana cewa an tsare shi ne bisa ƙa’idojin aiki na rundunar saboda halin rashin tsaro da ake ciki a yankin Arewa-maso-gabas da kuma yadda ’yan ta’adda ke amfani da hanyoyin kan iyaka wajen zirga-zirga da safarar kayayyakin aikin su.
Ta ce cikakken binciken sirri da sauran matakan bincike sun tabbatar da cewa Zein-Nur ba shi da wata alaƙa da kowace sananniyar ƙungiyar ta’addanci.
Binciken ya kuma nuna cewa shi mazaunin ƙauyen Shattu Anguba da ke Bosso a Jamhuriyar Nijar ne, kuma yana sana’ar kiwon raƙuma a yankin da ke ƙetaren Kogin Komadougou.

Bayan kammala binciken, Operation Haɗin Kai ta bayyana cewa ta wanke mutumin daga duk wani zargi na alaƙa da ’yan ta’adda.
Rundunar ta jaddada cewa duk mutanen da ake kamawa bisa zargi a lokacin ayyukan soja ana bi da su ne bisa tanadin doka da kuma tsauraran matakan tantancewa domin bambance fararen hula marasa laifi da ’yan ta’adda.
Ta kuma sake tabbatar da aniyar ta ta ci gaba da hana ’yan ta’adda samun damar gudanar da ayyukan su, tare da kiyaye ƙa’idojin ƙwarewar aiki, mutunta haƙƙin ɗan’adam da bin doka.






