• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Monday, September 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Sojoji sun kama ɗan Sudan da ake zargi da ta’addanci, sun cafke masu haɗa kai da ISWAP uku a Arewa

Wakilin Mu by Wakilin Mu
July 20, 2026
in Tsaro
A A
0
Sojoji sun kama ɗan Sudan da ake zargi da ta’addanci, sun cafke masu haɗa kai da ISWAP uku a Arewa
Sojoji sun tasa ƙeyar wanda ake zargi

Sojoji sun tasa ƙeyar wanda ake zargi

Dakarun Operation HAƊIN KAI sun kama wani ɗan ƙasar Sudan da ake zargi da kasancewa da alaƙa da ƙungiyoyin ta’addanci, tare da cafke wasu mutum uku da ake zargin masu haɗa kai ne da ƙungiyar ISWAP da kuma samar mata da kayan aiki a jihohin Borno da Yobe.

Rahotannin ayyukan soji da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya samu a ranar Litinin sun nuna cewa kamen ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da suka kai ga gudanar da samame a wurare daban-daban na yankin Arewa maso Gabas.

A cewar rahoton, dakarun Bataliya ta 115 sun kama wani ɗan Sudan mai suna Musa Fashir, mai shekara 32, a yankin Lassa-Dille da ke ƙaramar hukumar Askira/Uba ta jihar Borno.

Binciken farko ya nuna cewa ana zargin Fashir na da alaƙa da wasu ƙungiyoyin ta’addanci, lamarin da ya ƙara nuna yiwuwar shigowar mayaƙan ƙasashen waje domin tallafa wa ayyukan ta’addanci a yankin.

Haka kuma, dakarun sun kama wata mata mai suna Mary Florence, mai shekara 36, wadda ta bayyana cewa ita baƙuwa ce daga ƙasar Ghana kuma ba ta da takardun izinin zama. Hukumomin tsaro sun ce ana ci gaba da bincike domin tabbatar da asalinta da kuma ko tana da wata alaƙa da ayyukan ta’addanci ko wasu laifuka.

A wani samame na daban, dakarun Brigade ta 27 tare da haɗin gwiwar Civilian Joint Task Force (CJTF) sun kama wani mutum da ake zargin mai haɗa kai ne da ƙungiyar ISWAP a yankin Shishiwaji da ke ƙaramar hukumar Gulani ta jihar Yobe.

Rahoton ya ce ana zargin mutumin na gudanar da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, kuma yana da alaƙa da ISWAP. An kuma kama shi da wayoyin hannu guda uku.

Haka zalika, yayin sintirin kare manoma a yankin Kasabalari da ke ƙaramar hukumar Damboa ta jihar Borno, dakaru sun kama wasu mutum biyu da ake zargin suna samar wa ISWAP kayan aiki.

Kayan da aka ƙwato daga hannunsu sun haɗa da kekuna biyu, wayar hannu guda ɗaya, katin shaida, magungunan kashe ƙwari, magunguna, kayan gyaran keke, faifan ɗauko hasken rana (solar panel), fitilar hannu da kuma wuƙaƙe.

Jami’an sojin sun ce nasarorin da aka samu sun nuna muhimmancin amfani da bayanan sirri wajen daƙile shigowar mayaƙan ƙasashen waje, rushe hanyoyin samar wa ‘yan ta’adda kayan aiki da kuma karya cibiyoyin masu mara musu baya a yankin Arewa-Maso-Gabas.

Previous Post

Nijeriya ta taya Ibietan murnar sake zama Sakatare Janar na APRA

Next Post

Da umurnin Ofishin Akanta-Janar muka buɗe wa PFIPC asusu, amma ba mu saka ko ƙwandala a ciki ba saboda mun gano mai asusun ya ɓoye lauje cikin naɗi – CBN

Related Posts

Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Ministan Yaɗa Labarai ya taya Kiristoci murnar bikin Ista
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta jajanta wa al’ummar Neja kan rasuwar mutane a Wushishi, ta bayar da umarnin bincike

September 18, 2026
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja

September 18, 2026
Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa
Tsaro

Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa

September 9, 2026
Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam

September 1, 2026
Next Post
Badaƙalar Adeyemi Mathew: CBN bai saka wa PFIPC ko ƙwandala ba, saboda ya gano akwai lauje cikin naɗin asusun da aka yi ƙoƙarin buɗe wa hukumar – Akanta Janar

Da umurnin Ofishin Akanta-Janar muka buɗe wa PFIPC asusu, amma ba mu saka ko ƙwandala a ciki ba saboda mun gano mai asusun ya ɓoye lauje cikin naɗi – CBN

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!