• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Da umurnin Ofishin Akanta-Janar muka buɗe wa PFIPC asusu, amma ba mu saka ko ƙwandala a ciki ba saboda mun gano mai asusun ya ɓoye lauje cikin naɗi – CBN

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
July 21, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Badaƙalar Adeyemi Mathew: CBN bai saka wa PFIPC ko ƙwandala ba, saboda ya gano akwai lauje cikin naɗin asusun da aka yi ƙoƙarin buɗe wa hukumar – Akanta Janar
Mista Matthew Adeyemi

Mista Matthew Adeyemi

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana cewa ya buɗe asusun ajiyar kuɗaɗen waje guda biyu na ‘hukumar’ PFIPC wadda Matthew Adeyemi ya ƙirƙira ne bisa umurnin da ya samu daga Ofishin Akanta-Janar na Tarayya, ba bisa wata hulɗa kai-tsaye da ‘hukumar’ ba.

Daraktan Ayyukan Banki na CBN, Hamisu Ibrahim, ya bayyana hakan yayin da yake bayar da shaida a gaban Kwamitin Musamman na Majalisar Wakilai da ke binciken ayyukan PFIPC.

Ya ce CBN ya karɓi wasiƙar umurni mai kwanan wata 29 ga Yuli, 2025, daga Ofishin Akanta-Janar a ranar 30 ga Yuli, 2025, wadda ta ba shi izinin buɗe asusun dala da na fam sterling ga PFIPC.

Sai dai ya jaddada cewa duk da yake an buɗe asusun, ba a taɓa amfani da su ba, domin babu wani jami’in hukumar da ya gabatar da takardun izinin gudanar da asusun kamar yadda doka ta tanada. Saboda haka, asusun sun kasance ba su taɓa aiki ba, ba su da ko sisin kwabo a ciki, kuma ba a taɓa yin wata mu’amala ta kuɗi da su ba.

Hamisu Ibrahim ya bayyana cewa CBN ba ya buɗe ko rufe asusun wata ma’aikata kai-tsaye, duk irin waɗannan matakai sai ta hannun Ofishin Akanta-Janar na Tarayya.

Ya ce bayan buɗe asusun, ana sa ran hukumar ta gabatar da katin sa hannun masu izini, wasiƙun tabbatar da naɗin su, katin shaidar aiki, hotunan fasfo da sauran takardun da ake buƙata kafin a fara gudanar da asusun. Amma hakan bai taɓa faruwa ba.

A yayin binciken, an gano cewa PFIPC ta samu ware Naira biliyan 1.3 a kasafin kuɗin shekarar 2026, ta buɗe asusu a CBN, tana aiki daga wani ofishi a Babbar Sakatariyar Tarayya, kuma an yi iƙirarin cewa tana da ma’aikata 300.

Sai dai Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Didi Walson-Jack, ta musanta cewa ofishin ta ya tura ma’aikata zuwa PFIPC ko ya ba ita ‘hukumar’ ofishi.

Ta bayyana cewa ofishin da PFIPC ke amfani da shi a Babbar Sakatariyar Tarayya, mallakin Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF) ne.

Ta ƙara da cewa a lokacin tantance buƙatar ma’aikata ta shekarar 2025, wata mata da ta gabatar da kanta a matsayin mataimakiyar darakta ta PFIPC ta nemi a amince da ma’aikata 300, kuma an amince da buƙatar tare da buƙatun wasu hukumomi. Amma hakan ba yana nufin an tura ma’aikata zuwa hukumar ba.

Walson-Jack ta ce yayin da ta duba takardun da aka gabatar daga baya, ta fahimci akwai matsala, saboda haka ta umurci a ƙara matakan tantance sahihancin takardu tare da sanya lauya cikin tsarin, duba da irin waɗannan bayanai domin hana sake faruwar irin wannan kuskure.

Tun da farko, Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya ce an kafa kwamitin binciken ne domin gano gaskiya kan matsayin PFIPC a doka, aikin ‘hukumar’, yadda ta samu shiga cikin kasafin kuɗi da kuma alaƙar ta da hukumomin gwamnati.

Ya jaddada cewa manufar binciken ba siyasa ba ce, illa tabbatar da gaskiya, ƙarfafa gaskiya da kuma tabbatar da ɗaukar alhaki a harkokin gwamnati.

Idan ba a manta ba, makonni biyu da suka gabata, wannan jarida ta buga labarin yadda ofishin Akanta-Janar ya wanke CBN daga duk wani zargi, inda ya tabbatar da cewa CBN bai ma kammala tsare-tsaren buɗe wa PFIPC asusu ba, saboda waɗanda ya kamata su sa hannu daga ‘hukumar’ ba su bayyana kan su ba.

Tags: CBNMatthew Adeyemi
Previous Post

Sojoji sun kama ɗan Sudan da ake zargi da ta’addanci, sun cafke masu haɗa kai da ISWAP uku a Arewa

Next Post

Illolin Kallon Finafinan Batsa A Addini Da Kimiyya

Related Posts

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya ƙara ba da fifikon sa-ido wajen daƙile hadahadar kuɗaɗen ɗaukar nauyin ta’addanci

September 9, 2026
Next Post
Illolin Kallon Finafinan Batsa A Addini Da Kimiyya

Illolin Kallon Finafinan Batsa A Addini Da Kimiyya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!