• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gwamnatin Tarayya ta buɗe rajistar CAC kyauta ga ƙananan masana’antu 250,000

New Citizen Hausa by New Citizen Hausa
July 14, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Gwamnatin Tarayya ta buɗe rajistar CAC kyauta ga ƙananan masana’antu 250,000
Wata ƙaramar masana'anta

Wata ƙaramar masana'anta

Gwamnatin Tarayya ta buɗe shirin rajistar kasuwanci kyauta ta Hukumar Rajistar Kamfanoni ta Ƙasa (Corporate Affairs Commission – CAC) ga ƙananan ‘yan kasuwa da masana’antu 250,000 a faɗin ƙasar nan, ƙarƙashin haɗin gwiwar Hukumar Bunƙasa Ƙananan da Matsakaitan Masana’antu ta Nijeriya (SMEDAN) da CAC.

Manufar shirin, wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da shi, shi ne rage wa masu ƙananan sana’o’i nauyin kuɗin rajistar kasuwanci tare da ƙara shigar da su cikin tsarin kasuwanci na hukuma.

Masu cin gajiyar shirin za su samu rajistar Business Name a CAC ba tare da biyan kuɗin rajista ba, domin Gwamnatin Tarayya ce za ta ɗauki nauyin dukkan kuɗaɗen rajistar.

An bayyana ƙaddamar da shirin ne a yayin bikin karrama fitattun ƙananan, matsakaitan da manyan masana’antu (MSMEs) karo na takwas, wanda aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar 27 ga Yuni, 2026.

Baya ga rajistar CAC kyauta, waɗanda aka zaɓa za su kuma amfana da horaswa kan gudanar da kasuwanci, tallafin bunƙasa sana’o’i, da kuma samun damar shiga wasu shirye-shiryen da za su taimaka wajen faɗaɗa kasuwancin su.

Yadda ake neman shiga shirin

Masu kasuwancin da ke son cin gajiyar shirin su bi waɗannan matakai:

  •  Su shiga gidan yanar SMEDAN domin yin rajista: portal.smedan.gov.ng.
  •  Su buɗe sabon asusu ta hanyar cike sunan su, adireshin imel, lambar waya da kalmar sirri.
  • Su cika bayanan kasuwancin su yadda ya kamata.
  •  Idan an tambaye su ko kasuwancin su na da lambar rajistar CAC, su zaɓi “No” idan ba su da ita.
  •  Su sake duba bayanan da suka cika domin tabbatar da daidaiton su kafin su tura buƙatar.
  •  Daga nan su jira saƙon tabbatarwa daga SMEDAN idan an amince da buƙatar su.

Haka kuma, waɗanda suka riga suka yi rajista a bayanan SMEDAN amma ba su da rajistar CAC na iya samun cancantar shiga shirin kai-tsaye.

SMEDAN za ta tuntuɓi duk wanda aka amince da shi domin sanar da shi matakan da zai bi wajen kammala rajistar Business Name kyauta a CAC.

Shirin ya biyo bayan yarjejeniyar haɗin gwiwa da CAC da SMEDAN suka ƙulla domin yi wa ƙananan sana’o’i da masana’antu 250,000 rajista a hukumance a faɗin Nijeriya.

A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, manufar shirin ita ce rage wa ƙananan ‘yan kasuwa nauyin kuɗin rajista, tare da ba su damar shiga tsarin bankuna da sauran tsare-tsaren kasuwanci na hukuma, domin bunƙasa harkokin kasuwanci da ƙarfafa tattalin arzikin ƙasa.

Tags: CACkamfanonirajistaSMEDANtallafiƙananan masana'antu
Previous Post

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin ƙara kuɗin rajistar jarabawar WAEC da NECO

Next Post

Gwamnatin Tinubu ta kashe Naira biliyan 758 kan basussukan fansho, ta ƙara kuɗin masu ritaya

Related Posts

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gangamin CBN a Kano: A daina wulaƙanta takardun naira, a riƙe su cikin inganci da nagarta – CBN

September 29, 2026
Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Next Post
Gwamnatin Tinubu ta kashe Naira biliyan 758 kan basussukan fansho, ta ƙara kuɗin masu ritaya

Gwamnatin Tinubu ta kashe Naira biliyan 758 kan basussukan fansho, ta ƙara kuɗin masu ritaya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!