ABUJA – Kasuwar Hannayen Jari ta Nijeriya (NGX) ta ci gaba da kasancewa cikin kasuwannin hannayen jari mafi bunƙasa a duniya, lamarin da masana tattalin arziki suka danganta da sauye-sauyen manufofin tattalin arziki da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu take aiwatarwa.
Bayanan kasuwanni na baya-bayan nan sun nuna cewa NGX ta samu gagarumin cigaba, inda ta zarce kasuwannin hannayen jari da dama na ƙasashen da suka ci gaba wajen yawan ribar da masu zuba jari suka samu a wannan lokaci.
A ƙarshen shekarar 2025, kasuwar ta samu riba da ta kai kashi 51.19 cikin ɗari, abin da ya sanya ta cikin kasuwannin hannayen jari mafi bunƙasa a duniya.
Masana tattalin arziki da masu nazarin kasuwannin kuɗi na ƙasa da ƙasa sun bayyana cewa wannan cigaba ya samo asali ne daga sauye-sauyen manufofin tattalin arziki da gwamnatin Shugaba Tinubu ta aiwatar tun bayan hawan ta mulki.
Daga cikin matakan da suka bayyana sun haɗa da sake fasalin tsarin musayar kuɗaɗen waje, cire tallafin man fetur, ƙarfafa manufofin kasafin kuɗi da kuma aiwatar da tsare-tsaren da suka ƙara wa masu zuba jari ƙwarin gwiwar zuba jari a Nalijeriya.
Masana sun ce bunƙasar kasuwar hannayen jari tana samar wa kamfanoni damar samun jarin faɗaɗa ayyukan su, ƙara samar da guraben aikin yi da kuma bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.
Sun kuma bayyana cewa wannan cigaba yana nuna yadda manufofin Gwamnatin Tarayya suke ci gaba da jawo hankalin masu zuba jari na cikin gida da na ƙasashen waje.
Sai dai, duk da cewa har yanzu ana fuskantar wasu ƙalubalen tattalin arziki, masana sun ce cigaban da aka samu alama ce da ke nuna cewa sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa sun fara haifar da sakamako mai kyau tare da sake gina amincewar masu zuba jari ga tattalin arzikin Nijeriya.






