A ci gaba da rangadin ‘Gani Ya Kori Ji’ na manyan ayyukan Gwamnatin Tarayya a arewacin Nijeriya, tawagar ‘yan jarida da ke rangadi tare da Babban Mai Taimakawa Shugaban Ƙasa kan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Malam Abdulaziz Abdulaziz, ta kai ziyara wurin aikin gina layin dogo na zamani na Kano zuwa Maraɗi domin duba yadda aikin yake gudana tare da samun cikakken bayani daga jami’an da ke kula da shi.
A yayin ziyarar, Manajan Wurin Aikin ya bayyana wa tawagar cewa aikin yana tafiya yadda aka tsara, yana mai nuna amannar cewa idan aka ci gaba da aiki a wannan mataki, ana sa ran kammala shi kafin ƙarshen shekarar nan.
Ya ce layin dogon na daga cikin manyan ayyukan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da aka tsara domin inganta hanyoyin sufuri, bunƙasa kasuwanci da haɗa tattalin arzikin Nijeriya da na Jamhuriyar Nijar.
An bayyana wa mahalarta rangadin cewa babban layin dogon zai tashi daga Kano zuwa Maraɗi mai tsawon kusan kilomita 285, yayin da wani reshe mai tsawon kusan kilomita 108 zai haɗa Kano da Dutse a Jihar Jigawa. Da zarar an kammala aikin, zai sauƙaƙa zirga-zirgar fasinjoji da kayayyaki, rage cunkoson manyan tituna, da kuma ƙarfafa harkokin kasuwanci tsakanin Nijeriya da Nijar tare da buɗe sababbin damarmaki ga jihohin Kano, Jigawa, Katsina da sauran yankunan da ke maƙwabtaka da su.
Jami’an aikin sun kuma bayyana cewa layin dogon zai haifar da dubban guraben ayyukan yi kai-tsaye da kuma a kaikaice ga injiniyoyi, masu sana’o’in hannu, ma’aikatan sufuri, ‘yan kasuwa, kamfanoni da sauran masu ruwa da tsaki.
Haka kuma zai ƙara ƙarfafa masana’antu, jawo masu zuba jari, bunƙasa darajar noma tare da bai wa manoma damar kai amfanin su zuwa manyan kasuwanni cikin sauƙi.
Masu aikin jaridar da ke cikin shirin ‘Gani Ya Kori Ji’ sun bayyana cewa irin wannan rangadi yana ba su damar gani da ido kan yadda manyan ayyukan Gwamnatin Tarayya suke gudana maimakon dogaro da ji-ta- ji-ta. Sun ce aikin layin dogo na Kano–Maraɗi wata muhimmiyar shaida ce ta ƙudirin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na aiwatar da Ajandar Sabunta Fata (Renewed Hope Agenda) ta hanyar gina ingantattun ababen more rayuwa, ƙarfafa haɗin kan yankuna da bunƙasa tattalin arzikin arewacin Nijeriya da ƙasar baki ɗaya.







