Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su fifita gaskiya, sahihancin bayanai da ƙa’idojin aikin jarida, maimakon jan hankali da neman yawan masu kallo ko mabiyan su a soshiyal midiya.
Shugaban ya bayyana hakan ne a jawabin sa wajen liyafar farko ta dare da ya shirya wa wakilan kafafen yaɗa labarai na Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja a jiya Alhamis.
Tinubu ya ce aikin jarida na ƙwarai ya zama wajibi a wannan zamani da ake fama da yaɗuwar labaran ƙarya, bayanan bogi, amfani da fasahar kwaikwayon murya da fuska da kuma ƙirƙirar bidiyoyin bogi ta hanyar fasahar zamani.
Ya ce: “Dole ne kafafen yaɗa labarai su zaɓi gaskiya a kan ƙarya, su zaɓi muhimman bayanai a kan jan hankali, su kuma fifita mutunci da amincewar jama’a a kan neman yawan masu kallo da mabiya a intanet.”
Ya jaddada cewa ’yancin faɗar albarkacin baki da ’yancin aikin jarida ginshiƙai ne na dimokiraɗiyya, amma waɗannan haƙƙoƙi suna tafiya tare da nauyin tabbatar da cewa an yaɗa bayanai cikin adalci da gaskiya ba tare da jefa al’umma cikin rikici ba.
Shugaban ya bayyana kan sa a matsayin mai goyon bayan kafafen yaɗa labarai tun shekaru da dama, yana mai cewa ba za a iya samun ingantacciyar dimokiraɗiyya ba tare da kafafen yaɗa labarai masu ’yanci ba.
Sai dai ya ja hankalin ’yan jarida da kada su zama hanyoyin yaɗa bayanan da ba a tantance ba, musamman waɗanda ka iya yin illa ga tsaron ƙasa da zaman lafiyar al’umma.
“’Yancin faɗar albarkacin baki ba yana nufin ’yancin ɓata suna ba. Haka kuma, ’yancin aikin jarida ba yana nufin ’yancin yaudarar jama’a da gangan ba,” inji shi.
Tinubu ya ce dangantaka tsakanin gwamnati da kafafen yaɗa labarai tana tattare da haɗin gwiwa mai karfi, domin gwamnati tana jagoranci da aiwatar da manufofi, yayin da kafafen yaɗa labarai suke sa ido tare da yi mata tambayoyi masu wahala domin tabbatar da gaskiya da riƙon amana.
Ya ce, “Mu abokan hamayya ne a ma’anar dimokiraɗiyya, amma kuma abokan hulɗa ne wajen gina ƙasa.”
Shugaban ya tabbatar da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da kare ’yancin aikin jarida kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasa ya tanada, musamman sassa na 22 da 39, tare da ci gaba da aiwatar da dokar samun bayanai domin ƙarfafa gaskiya da buɗaɗɗiyar gwamnati.
Dangane da tattalin arziki, Tinubu ya ce sauye-sauyen da gwamnatin sa ta aiwatar sun fara haifar da sakamako mai kyau, inda ya ce tattalin arziki yana samun daidaito, kuɗaɗen shiga na gwamnati sun ƙaru, jarin masu zuba hannun jari yana dawowa, sannan kasuwar hannayen jari da ajiyar kuɗaɗen waje suna inganta.
A fannin tsaro kuwa, shugaban ya ce sojoji da sauran hukumomin tsaro sun ƙara kai hare-hare kan ’yan ta’adda da masu aikata laifuka, lamarin da ya kai ga kashe dubban miyagu da ceto mutane da dama da aka yi garkuwa da su.
Ya amince cewa har yanzu akwai ƙalubalen tsaro, amma gwamnati ta fara sauyawa daga mayar da martani zuwa karya ƙarfin barazanar da ake fuskanta a sassa daban-daban na ƙasar nan.
A ƙarshe, Tinubu ya yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su maye gurbin neman tayar da hankali da ƙwarewa, tare da gina al’umma bisa gaskiya, riƙon amana da haɗin kai.
Ya ce: “Mu maye gurbin neman tayar da hankali da neman gaskiya, mu ƙarfafa dimokiraɗiyya, kuma mu ba kowane ɗan Nijeriya dalilin yin imani da makomar ƙasar mu.”






