• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Gwamna Buni ya ɗauki nauyin tawagar Yobe zuwa Taron Manema Labarai na Arewa

Wakilin Mu by Wakilin Mu
July 2, 2026
in Labarai
A A
0
Gwamna Buni ya ɗauki nauyin tawagar Yobe zuwa Taron Manema Labarai na Arewa
Gwamna Buni, da hatimin taron

Gwamna Buni, da hatimin taron

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da ɗaukar cikakken nauyin tawagar jihar da za ta halarci Taron Manema Labarai na Arewa (Arewa Media Summit), wanda za a gudanar a ranar Litinin, 6 ga Yuli, 2026, a Kano.

A cikin wata sanarwa da mai kula da harkokin sadarwar zamani da dabarun yaɗa labarai na ofishin gwamnan, Yusuf Ali, ya fitar, an bayyana cewa tallafin ya haɗa da kuɗin sufuri, masauki a otal, abinci da kuma alawus na tafiya ga mahalarta 50 daga Jihar Yobe.

Sanarwar ta ce mahalartan sun haɗa da membobin kwamitocin shirya taron da masu gudanarwa (coordinators) masu wakiltar jihar.

Sakataren Kwamitin Mahalarta na Jihar Yobe, Farfesa Sheriff Almuhajir, ya bayyana cewa kowace daga cikin ƙananan hukumomi 17 na jihar za ta samu wakilai biyu, yayin da sauran mahalarta za su fito daga shiyyoyin sanatoci uku da hedikwatar jihar domin tabbatar da cikakken wakilci da haɗin kai.

Ya ce bayan amincewar da gwamnan ya bayar, shugaban kwamitin, Malam Abdulaziz Abdulaziz, tare da sauran membobin kwamitin ba sa buƙatar damuwa da shirye-shiryen tafiyar tawagar, domin gwamnatin jihar ta riga ta tanadi dukkan abubuwan da ake buƙata.

Almuhajir ya kuma yaba wa Sakataren Gwamnatin Jihar Yobe, Dakta Mohammed Goje, bisa goyon baya da jajircewar sa wajen tabbatar da halartar matasa a taron.

Haka kuma, ya yaba wa Shugaban Matasan APC na Jihar Yobe, Mohammed Musa Gulani, saboda gudunmawar da ya bayar wajen tattara mahalarta da kuma tabbatar da nasarar shirye-shiryen tafiyar.

Ya bayyana matakin da Gwamna Buni ya ɗauka a matsayin wata alama ta ƙudirin gwamnatin sa na ci gaba da bunƙasa matasa, ƙarfafa harkokin yaɗa labarai da inganta ƙwarewar jama’a.

Almuhajir ya jaddada cewa tawagar Jihar Yobe za ta wakilci jihar yadda ya kamata a taron na Arewa Media Summit.

Tags: Arewa Media SummitGwamna Mai Mala Bunimanema labaraitawagaYobe
Previous Post

Sojojin mu sun kashe ’yan ta’adda 1,597, sun ceto mutane 1,516 – Hedikwatar Tsaro

Next Post

D.O. Fagunwa: Gogaggen Jigo A Adabin Afrika

Related Posts

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura
Labarai

Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura

November 25, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa
Labarai

Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa

November 24, 2026
Next Post
D.O. Fagunwa: Gogaggen Jigo A Adabin Afrika

D.O. Fagunwa: Gogaggen Jigo A Adabin Afrika

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!