Hedikwatar Tsaro ta bayyana cewa dakarun soji sun kashe ’yan ta’adda da masu tayar da ƙayar baya 1,597, tare da kuɓutar da mutane 1,516 daga hannun masu garkuwa da mutane a cikin ayyuka 14,221 da aka gudanar tsakanin Janairu da Yuni 2026.
Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro, Manjo Janar Samaila Uba, wanda Guruf Kyaftin Kabiru Ali ya wakilta, ya ce an gudanar da ayyukan ne ta sama, ta ƙasa da ruwa a sassa daban-daban na ƙasar nan.
Ya ce dakarun sun kuma ƙwato bindigogi 451, harsasai 16,726 da bama-bamai da na’urorin fashewa 161, lamarin da ya hana masu aikata laifuka ci gaba da gudanar da ayyukan su.
A cewar sa, an gudanar da ayyukan a jihohin Borno, Yobe, Taraba, Katsina, Kwara, Zamfara, Sokoto, Filato, Binuwai, Neja, Oyo da Kaduna.
Sojojin sun kashe mayaƙan Boko Haram da ISWAP 412, sun kama mutum 332, sannan mutum 132 daga cikin mayaƙan ƙungiyoyin sun miƙa wuya sakamakon matsin lambar da ake musu.
Har ila yau, an lalata na’urorin fashewa 31 cikin nasara tare da gudanar da shirye-shiryen zaman lafiya 33 da wayar da kai guda 13 a faɗin ƙasar nan.







