Gwamnatin Tarayya, ta hannun Asusun Bunƙasa Noma na Ƙasa (NADF), ta ƙaddamar da kashi na farko na Shirin Tallafin Kayan Aikin Noma (Fertilizer Intervention Support Programme – FISP) a yankin Arewa-maso-yamma, inda ta raba buhunan taki 100,800 ga ƙananan manoma 25,200 a jihohin Katsina, Kano, Kaduna, Kebbi da Jigawa.
Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da shirin a Jihar Katsina, Ministan Noma da Samar da Abinci, Sanata Abubakar Kyari, ya bayyana shirin a matsayin wani muhimmin mataki na ƙarfafa samar da wadataccen abinci da kuma bunƙasa tattalin arzikin karkara, daidai da manufofin Renewed Hope Agenda na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ministan ya ce kowace daga cikin jihohin biyar da suka ci gajiyar shirin ta samu buhuna 20,160, waɗanda za a raba wa manoma 5,040 da aka tantance tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar Manoma ta Ƙasa (AFAN).
A cewar sa, manufar shirin ita ce rage giɓin da ke tsakanin ƙananan manoma da manyan manoma ta fuskar yawan amfanin gona, tare da ƙarfafa masana’antun taki na cikin gida domin ƙara samar da taki, samar da guraben ayyukan yi da kuma gina ingantaccen tsarin samar da abinci a ƙasar nan.
Sanata Kyari ya tunatar da cewa a baya-bayan nan Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin AgGrow-1, wanda ya haɗa manoma da masu sarrafa kayan amfanin gona domin samar masu da tabbatacciyar kasuwa tare da ƙara darajar kayayyakin amfanin gona.
Ya jaddada cewa gwamnatin Tinubu tana ci gaba da aiwatar da tsare-tsare da shirye-shiryen da suka shafi samar da wadataccen abinci, waɗanda ke taimakawa wajen daidaita farashin kayan masarufi, rage matsin hauhawar farashi da kuma kawo sauyi mai ɗorewa a fannin noma da tattalin arzikin Nijeriya.
Ya ce: “Ba a samun nasarar samar da wadataccen abinci a rana ɗaya. Ana cimma hakan ne a hankali, a kowace kaka, ta hannun kowane manomi da kuma ta hanyar kowane tallafin noma da aka samar. Yau yankin Arewa maso Yamma ne ya samu wannan gagarumar dama.”
Shirin FISP yana daga cikin manyan matakan da Gwamnatin Tarayya take ɗauka domin ƙara yawan amfanin gona, tallafa wa manoma, da tabbatar da wadatar abinci a faɗin Nijeriya, yayin da ake ƙoƙarin bunƙasa tattalin arzikin ƙasa ta hanyar noma.







