• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rancen Dare Ɗaya: Abin da CBN ke nufi da Gejin Adadin Rancen Biyan Gaggawa Tsakanin Bankunan Nijeriya (NOFR)

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
June 19, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Rancen Dare Ɗaya: Abin da CBN ke nufi da Gejin Adadin Rancen Biyan Gaggawa Tsakanin Bankunan Nijeriya (NOFR)
Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, tare da wasu manyan mahalartan taron ƙaddamar da tsarin Rancen Biyan Gaggawa Tsakanin Bankunan Nijeriya, wato Nigerian Overnight Financing Rate (NOFR)

Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, tare da wasu manyan mahalartan taron ƙaddamar da tsarin Rancen Biyan Gaggawa Tsakanin Bankunan Nijeriya, wato Nigerian Overnight Financing Rate (NOFR)

A wani sabon mataki na ci gaba da ƙirƙiro manufofi don ƙarfafa kasuwannin kuɗi na Nijeriya, Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ƙaddamar da tsarin Rancen Biyan Gaggawa Tsakanin Bankunan Nijeriya, wato Nigerian Overnight Financing Rate (NOFR).

Wannan kuwa wani ma’auni ne mai tafiya bisa tsari na gaskiya da ya dogara da ainihin mu’amaloli, wanda aka ƙirƙira domin nuna haƙiƙanin kuɗin geji da adadin kuɗin ruwa a tsarin rancen gaggawa tsakanin bankuna, a kasuwar kuɗi.

Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da shirin a Abuja, Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya bayyana ‘NOFR’ a matsayin wani babban ci gaba wajen ƙarfafa sahihanci da amincin kasuwa, inganta gano farashi yadda ya kamata, ƙarfafa tsarin tunkarar ƙalubalen da akan iya fuskanta a gaba, da kuma ƙara wa masu zuba jari ƙwarin gwiwa.

An haɓaka ‘NOFR’ ne tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar Manyan Dillalan Hadahadar Kuɗi (FMDA), tare da tallafin Bankin Bunƙasa Tattalin Arziki na Turai (EBRD). Ana sa ran wannan sabon ma’auni zai taimaka wajen zurfafa kasuwannin kuɗi na Nijeriya da kuma tallafa wa ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa.

Dalla-dalla: Me CBN ke nufi da NFOR?

NOFR na nufin rance na ɗan gajeren lokaci da cibiyoyin kuɗi, wato ke bai wa juna domin cike buƙatun ajiyar kuɗin su na yau da kullum.

Ana bayar da wannan rance ne a ƙarshen ranar aiki ko a ce bayan lokacin tashi daga aiki, sannan dole ne a a biya rancen tare da kuɗin ruwa a farkon ranar aiki ta gaba, washegari da safe kenan.

Muhimman abubuwan da suka shafi rancen gaggawa tsakanin bankuna:

1. Farashin rancen biyan gaggawa:

Wannan shi ne takamaiman kuɗin ruwa da ake caji kan irin wannan rance. Yawanci shi ne mafi ƙarancin kuɗin ruwa da ake samu a tsarin kuɗi, kuma galibi bankunan da suka fi ƙarfin biyan bashi ne kawai ke samun damar karɓar sa.

2. Tasiri ga tattalin arziki:

Babban Bankin Nijeriya (CBN) na amfani da wannan farashi a matsayin wata hanya ta sarrafa yawan kuɗin da ke zagayawa a tattalin arziki da kuma daƙile hauhawar farashi.

Duk wani canji a wannan farashi yana tasiri kai tsaye kan kuɗin ruwa da mutane da kamfanoni ke biya wajen karɓar rance ko jinginar gida.

3. Tabbatar da daidaiton kasuwa:

Wannan tsari yana taimakawa wajen hana bankuna fuskantar ƙarancin kuɗi na ɗan lokaci, wanda ke tabbatar da cewa tsarin kuɗi gaba ɗaya yana da isasshen kuɗin ruwa kuma yana aiki cikin kwanciyar hankali a kullum.

4. Hanyoyin saka jari:

Ga masu zuba jari, ko ɗaiɗaikun mutane ko manyan cibiyoyi, akwai asusun saka jari musamman na rancen biyan gaggawa dare ko ajiyar kuɗi na dare guda da ake amfani da su wajen ajiye kuɗi cikin aminci na ɗan gajeren lokaci, domin a samu riba da kuɗin, maimakon a danƙare su wuri guda ba tare da amfani da su ba.

Fahimtar farashin rancen dare guda ko a ce rancen gaggawa tsakanin bankuna da tasirin sa ga tattalin arziki:

Farashin rancen gaggawa a tsakanin bankuna shi ne kuɗin ruwan da bankuna ke cajar juna idan suna ba da rance domin cika buƙatun ajiyar kuɗin su. Wannan shi ne mafi ƙarancin kuɗin ruwa da ake samu a tsarin kuɗi.

A tsari na harkar musayar kuɗaɗen ƙasashen waje kuwa, wannan tsarin rancen gaggawa na dare guda yana nufin saye da sayar da kuɗaɗe tsakanin ƙarfe 9 na dare zuwa ƙarfe 8 na safe na agogon ƙasa.

Kasuwar dare guda wani ɓangare ne da bankuna ke hulɗa da junan su ta hanyar karɓar rance mafi gajeren lokaci, inda masu ba da rance ke samar da kuɗi na dare guda kawai, washegari da safe a biya kuɗin tare da yin ƙarin riba kan adadin da aka karɓa rancen.

A taƙaice, Nigerian Overnight Financing Rate (NOFR) wani ma’auni ne da ke nuna ainihin farashin kuɗin rancen dare guda tsakanin cibiyoyin kuɗi a Nijeriya, kuma yana taimakawa wajen ƙara gaskiya, inganci da kwanciyar hankali a kasuwar kuɗin ƙasar.

Tags: CBNNigerian Overnight Financing Rate (NOFR)Olayemi Cardoso
Previous Post

Ƙasar Ƙatar da jakadun Afrika 13 sun tarbi sabon Jakaden Nijeriya Mahmood Yakubu a Doha

Next Post

Lauya ta rasu saboda ɗokin nasarar Ghana a kan Panama a gasar Kofin Duniya

Related Posts

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’

November 25, 2026
Muna samun nasarori a tsaro, ilimi da ababen more rayuwa – Tinubu 
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya ware Naira biliyan 450 domin tallafa wa manoma 500,000

November 22, 2026
Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40

November 19, 2026
CBN ya naɗa kamfanoni takwas domin kula da fitar da ɗanyen mai da iskar gas
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN da NNPCL sun ƙulla yarjejeniyar ƙarfafa tattalin arziki da samar da kuɗaɗen zuba jari a ɓangaren makamashi

November 18, 2026
CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su

November 17, 2026
Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS

November 16, 2026
Next Post
Lauya ta rasu saboda ɗokin nasarar Ghana a kan Panama a gasar Kofin Duniya

Lauya ta rasu saboda ɗokin nasarar Ghana a kan Panama a gasar Kofin Duniya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!