• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Ƙasar Ƙatar da jakadun Afrika 13 sun tarbi sabon Jakaden Nijeriya Mahmood Yakubu a Doha

Fati Abdul by Fati Abdul
June 18, 2026
in Labarai
A A
0
Ƙasar Ƙatar da jakadun Afrika 13 sun tarbi sabon Jakaden Nijeriya Mahmood Yakubu a Doha
Jakaden Nijeriya a Ƙatar, Ambasada Mahmood Yakubu, yana gaisawa da jami'an diflomasiyya bayan saukar sa a birnin Doha

Jakaden Nijeriya a Ƙatar, Ambasada Mahmood Yakubu, yana gaisawa da jami'an diflomasiyya bayan saukar sa a birnin Doha

Tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kan ta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya fara aiki a matsayin Jakaden Tarayyar Nijeriya a ƙasar Ƙatar.

Jakada Yakubu ya isa babban birnin ƙasar, Doha a ranar Laraba, inda Daraktan Sashen Ladabi na Ma’aikatar Harkokin Wajen Ƙatar, Jakada Ibrahim Yousif Abdullah Fakhro, ya tarbe shi cikin girmamawa a filin jirgin sama.

Haka kuma, jakadun ƙasashen Afrika 13 ne suka yi masa maraba tare da Babban Sakataren Ƙungiyar Ƙasashe Masu Fitar da Iskar Gas (GECF), Dakta Philip Mshelbila, da Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Nijeriya Mazauna Ƙasashen Waje (NIDO) reshen Ƙatar, Mista Michael Ndukaihe Ihekwaba.

Yakubu ya tafi wannan sabon aiki na diflomasiyya da tarihin nagartaccen aikin gwamnati. A matsayin sa na Shugaban INEC daga shekarar 2015 zuwa 2025, ya jagoranci manyan sauye-sauye a tsarin zaɓen Nijeriya, waɗanda suka ƙarfafa tsarin gudanar da zaɓe, suka inganta amfani da fasaha a harkokin zaɓe, suka bunƙasa tsarin tantance masu kaɗa ƙuri’a, tare da ƙara amincewar jama’a ga cibiyoyin dimokiraɗiyya.

Ana girmama Ambasada Yakubu sosai saboda jajircewar sa wajen tabbatar da gaskiya, ƙwarewa, da kuma kyakkyawan shugabanci na dimokiraɗiyya.

A lokacin jagorancin sa, ya taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da zaɓuɓɓukan ƙasa da na cike gurbi cikin nasara.

Naɗin sa a matsayin Jakaden Nijeriya a Ƙatar yana nuna irin amincewar da Gwamnatin Tarayya take da ita ga jagorancin sa, gogewar sa da kuma ƙwarewar sa wajen inganta muradun Nijeriya na diflomasiyya, tattalin arziki da dangantakar ƙasashe a ɗaya daga cikin muhimman ƙasashen Gabas ta Tsakiya.

Ana sa ran zai ƙara ƙarfafa dangantaka tsakanin Nijeriya da Ƙatar, musamman a fannoni kamar kasuwanci, zuba jari, makamashi, ilimi da kuma hulɗar al’ummomin ƙasashen biyu.

Previous Post

Minista na so kafofin yaɗa labarai da hukumomin tsaro su ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa domin kare zaman lafiya

Next Post

Rancen Dare Ɗaya: Abin da CBN ke nufi da Gejin Adadin Rancen Biyan Gaggawa Tsakanin Bankunan Nijeriya (NOFR)

Related Posts

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura
Labarai

Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura

November 25, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa
Labarai

Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa

November 24, 2026
Next Post
Rancen Dare Ɗaya: Abin da CBN ke nufi da Gejin Adadin Rancen Biyan Gaggawa Tsakanin Bankunan Nijeriya (NOFR)

Rancen Dare Ɗaya: Abin da CBN ke nufi da Gejin Adadin Rancen Biyan Gaggawa Tsakanin Bankunan Nijeriya (NOFR)

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!