Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gudanar da bikin Ranar Dimokiraɗiyya ta Nijeriya ta bana da safe, inda ya karrama jaruman gwagwarmayar 12 ga Yuni, ciki har da marigayi Cif M.K.O. Abiola, Hajiya Kudirat Abiola, Cif Gani Fawehinmi, Janar Shehu Musa Yar’Adua da kuma ɗimbin masu fafutukar dimokiraɗiyya, ‘yan jarida, shugabannin ƙwadago da sojojin da suka yi gwagwarmaya domin tabbatar da mulkin dimokiraɗiyya a Nijeriya.
A cikin jawabin da ya yi wa al’ummar ƙasa a ranar Dimokiraɗiyya, Tinubu ya kuma bayyana sababbin lambobin yabo na ƙasa ga wasu ‘yan Nijeriya da suka fuskanci tsangwama, ɗaurin kurkuku, gudun hijira da sauran wahalhalu a lokacin gwagwarmayar kawar da mulkin soja. Haka kuma ya sake jaddada ƙudirin gwamnatin sa na ƙarfafa dimokiraɗiyya, tsaro da bunƙasar tattalin arziki.
Shugaban ya bayyana ranar 12 ga Yuni a matsayin rana mai tsarki a tarihin Nijeriya, yana mai tunatar da cewa tsawon shekaru 27 ba tare da katsewa ba tun daga ranar 29 ga Mayu, 1999, ‘yan Nijeriya na zaɓar shugabannin su ta hanyar zaɓe, suna shaida miƙa mulki cikin lumana tare da warware rikice-rikicen siyasa ta hanyar cibiyoyin dimokiraɗiyya maimakon amfani da tashin hankali.
A cewar sa, duk da cewa dimokiraɗiyyar Nijeriya ba ta kai matsayin kamala ba, mallakar ‘yan Nijeriya ce kuma wajibi ne a ci gaba da kare ta da ƙarfafa ta.
Tinubu ya yi magana kan zaɓen gwamnonin da za a gudanar nan gaba a jihohin Ekiti da Osun, inda ya buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kan ta ta Ƙasa (INEC), hukumomin tsaro da jam’iyyun siyasa da su tabbatar da gudanar da zaɓe cikin lumana, gaskiya da sahihanci.
Ya ce: “Dimokiraɗiyya tana gazawa idan ‘yan ƙasa sun rasa amincewa da tsarin.”
Shugaban ya yi kira ga Majalisar Dokoki ta Tarayya, ɓangaren shari’a, kafafen yaɗa labarai da ƙungiyoyin fararen hula da su ci gaba da taka rawar da suke takawa wajen kare jamhuriyar Nijeriya.
Ya ce: “Ga Majalisar Dokoki ta Ƙasa, ɓangaren shari’a, kafafen yaɗa labarai da ƙungiyoyin fararen hula: ku ne ginshiƙan kare jamhuriyar mu. Ku soke ni, ku saɓa da ni, amma kada ku daina yarda da Nijeriya.”
Da yake jawabi ga matasan Nijeriya, Tinubu ya buƙace su da su gina makomar su a ƙasar maimakon yanke ƙauna da ita.
Ya ce: “Kira ga matasan mu: Nijeriya gidan ku ce kuma makomar ku ce. Ku gina a nan, ku ƙirƙira fasahohi a nan, ku yi aiki a nan, kuma ku kaɗa ƙuri’a a nan. Duk wata babbar ƙasa mutanen da suka tsaya suka magance matsalolin ta ne suka gina ta, ba waɗanda suka yi watsi da ita ba.”
Ya kuma yaba wa jami’an rundunar soji, ‘yan sanda, hukumomin leƙen asiri, sarakunan gargajiya, shugabannin addinai da shugabannin al’umma saboda gudunmawar da suke bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya, tsaro da haɗin kan ƙasa.
Yayin da ya amince cewa bikin Ranar Dimokiraɗiyya ta bana ya zo ne a lokacin da aka yi garkuwa da ɗalibai a jihohin Oyo da Borno, Tinubu ya bayyana fatan cewa za a ceto waɗanda aka sace cikin ƙoshin lafiya.
Ya jaddada cewa dimokiraɗiyya ba za ta bunƙasa ba idan babu tsaro, yana mai bayyana matakan da gwamnatin sa take ɗauka wajen ƙarfafa tsaron ƙasa ta hanyar ƙara ɗaukar ma’aikatan tsaro da ƙara kuɗaɗen da ake warewa ga fannin.
A cewar sa, gwamnati ta amince da ɗaukar sama da sababbin ‘yan sanda 50,000 da dubban sojoji, tare da ware Naira tiriliyan 5.41 ga tsaro da harkokin kariya a kasafin kuɗin shekarar 2026, wanda ya zama mafi girman kaso da aka taɓa warewa ga tsaro a tarihin Nijeriya.
Tinubu ya ce dabarun tsaron Nijeriya sun sauya daga atisayen horaswa tare da ƙawayen ƙasa kamar Amurka da Faransa zuwa kai hare-hare na musamman kan ‘yan tawaye da ‘yan ta’adda.
Ya ambaci farmakin soji da aka kai a Arege da ke Jihar Borno, inda aka lalata cibiyar gudanarwa ta ISWAP, yana mai cewa adadin mace-macen da ke da alaƙa da ta’addanci ya ragu sosai tun daga shekarar 2015.
Ya ƙara da cewa an kashe sama da ‘yan ta’adda 13,000 a cikin shekara guda da ta gabata, yayin da sama da mayaƙa 124,000 da iyalan su suka miƙa wuya ƙarƙashin shirin Operation Safe Corridor tun daga shekarar 2023.
Shugaban ya aika da saƙo mai ƙarfi ga ‘yan bindiga, da masu garkuwa da mutane da masu ɗaukar nauyin ta’addanci.
Ya ce: “Kira ga ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da masu ɗaukar nauyin ta’addanci: Ku miƙa wuya ko kuma ku fuskanci cikakken ƙarfin gwamnatin Nijeriya. Wannan damar miƙa wuya ba za ta kasance a buɗe har abada ba. Ba za a nuna jinƙai ga waɗanda ke cinikin jinin ‘yan Nijeriya ba.”
Tinubu ya buƙaci ‘yan Nijeriya da kada su danganta laifi da ƙabila, yana mai cewa yaƙi da rashin tsaro yana buƙatar haɗin kan ƙasa baki ɗaya.
Ya ce: “Laifi ba shi da ƙabila. Dole mu haɗa kai, kuma mu tabbatar wa da kan mu cewa ba da daɗewa ba maƙiyan ƙasar mu za su zama tarihi.”
Babban ɓangaren jawabin shugaban ya mayar da hankali ne kan karrama jarumai maza da mata na gwagwarmayar dimokuraɗiyyar 12 ga Yuni.
Ya yi wa marigayi Cif M.K.O. Abiola, wanda aka fi ɗauka a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 12 ga Yuni, 1993 da aka soke, kirari da cewa alamar haɗin kan ƙasa ne, wanda nasarar sa ta zarce bambance-bambancen ƙabila da addini.
Tinubu ya kuma karrama Hajiya Kudirat Abiola da sauran fitattun jagororin fafutukar dimokiraɗiyya, ciki har da Cif Gani Fawehinmi, Cif Bola Ige, Cif Alfred Rewane, Pa Abraham Adesanya, Cif Anthony Enahoro, Alhaji Balarabe Musa, Commodore Dan Suleiman, Dakta Beko Ransome-Kuti, Frank Kokori, Arthur Nwankwo, Chima Ubani da Janar Shehu Musa Yar’Adua.
Ya ce sadaukarwar da suka yi ita ce ta aza harsashin ‘yancin da ‘yan Nijeriya suke mora a yau.
A cewar sa: “A matsayin mu na waɗanda suka amfana daga gwagwarmayar su, muna da haƙƙin ƙarfafawa da zurfafa cibiyoyin dimokiraɗiyyar da suka yi yaƙi domin samuwar su.”
Ya ƙara da cewa: “Babbar girmamawar da za mu yi musu ita ce gina Nijeriya inda ake kare ‘yanci, tabbatar da adalci, faɗaɗa damar cigaba da kuma tabbatar da gwamnati mai ɗaukar haƙƙin ayyukan ta.”
Shugaban ya bayyana cewa idan har 12 ga Yuni ya samar da ‘yancin siyasa, to alhakin ƙarni na yanzu shi ne samar da ‘yancin tattalin arziki ga ‘yan Nijeriya.
Ya ce dole ne dimokiraɗiyya ta bayyana a cikin ingantuwar rayuwar jama’a, samar da dama ga matasa, bunƙasar manoma, nasarar ‘yan kasuwa da samar da rayuwa mai daraja ga ma’aikata.
Tinubu ya kare sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin sa take aiwatarwa, yana mai cewa sun zama wajibi domin ceto kuɗaɗen gwamnati, dawo da amincewar masu zuba jari da kuma daidaita tattalin arzikin ƙasa.
Ya ce kuɗaɗen shiga na tarayya sun ƙaru tun daga shekarar 2023, lamarin da ya ba jihohi da ƙananan hukumomi ƙarin damar aiwatar da ayyukan more rayuwa, kiwon lafiya, ilimi da tsaro.
Shugaban ya ƙara da cewa an samu ƙarin gaskiya a harkokin kuɗi, an rage asarar kuɗaɗe, kuma zuba jari na ƙaruwa a fannoni daban-daban da suka haɗa da noma, makamashi, masana’antu, ma’adinai, sufuri, fasaha da masana’antar ƙirƙira.
Ya bayyana cewa ƙarfin tace man fetur a cikin gida ya ƙaru, wanda ke taimakawa wajen ƙarfafa tsaron makamashi da rage dogaro da shigo da kayayyakin man fetur daga ƙasashen waje.
Tinubu ya bayyana cewa lokacin da ya karɓi mulki a shekarar 2023, fannin wutar lantarki yana fama da ƙarancin samar da wuta, raunin hanyoyin isar da ita, ƙarancin iskar gas, asarar kuɗaɗe da kamfanonin rarraba wuta ke yi, ƙarancin mitoci sama da miliyan huɗu da kuma manyan basussuka na baya.
Domin magance waɗannan matsaloli, ya ce ya sanya hannu kan Dokar Wutar Lantarki, wadda ta bai wa jihohi damar samarwa, isarwa da rarraba wutar lantarki da kan su.
Ya kuma bayyana cewa an ba Kwamitin Musamman na Shugaban Ƙasa kan Wutar Lantarki izinin tara bashin Naira tiriliyan 4 domin biyan basussukan da aka tabbatar da su, yayin da Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Yankunan Karkara tare da tallafin Bankin Duniya da Bankin Raya Afrika ta faɗaɗa ayyukan samar da wutar lantarki ta mini-grid da off-grid a al’ummomi, jami’o’i, asibitoci da kasuwanni.
Ya ce: “Wutar lantarki ɗaya ce daga cikin ribar dimokiraɗiyyar da muke bin kowane ɗan Nijeriya bashi. Kuma muna da niyyar samar da ita.”
Tinubu ya kuma bayyana cewa ayyukan more rayuwa da ake aiwatarwa a faɗin ƙasar nan suna taimakawa wajen haɗa masu samar da kayayyaki da kasuwanni tare da samar da ayyukan yi da damar cigaba.
Ya bayyana cewa Asusun Bunƙasa Noma na Ƙasa zai samar da taraktoci 10,000 cikin shekaru biyar masu zuwa, yayin da sama da ƙananan da matsakaitan masana’antu 1,000 suka samu takardar shaidar fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje.
A cewar sa, fitar da kayayyakin da ba na man fetur ba ya ƙaru da kashi 21 cikin ɗari a cikin shekarar da ta gabata.
Sai dai duk da waɗannan nasarori, shugaban ya amince cewa har yanzu ‘yan Nijeriya da dama suna fuskantar matsin tattalin arziki, tare da yin alƙawarin ci gaba da ƙoƙarin rage hauhawar farashi, ƙara samar da abinci, samar da ayyukan yi da inganta rayuwar jama’a.
Ya ce: “Muna motsawa daga rashin tabbas zuwa daidaito. Mataki na gaba shi ne hanzarta bunƙasa tattalin arziki da tabbatar da cewa amfanin sa ya kai ga kowane gida, kowace al’umma da kowane yanki.”
Tinubu ya kuma sake jaddada goyon bayan gwamnatin sa ga cikakken ‘yancin cin gashin kan ƙananan hukumomi 774 na Nijeriya, yana mai cewa raunin shugabanci a matakin ƙasa ya taimaka wajen haifar da rashin tsaro da koma-baya a cigaba.
Daga cikin manyan sanarwar da ya yi akwai amincewar Gwamnatin Tarayya da sake farfaɗo da cibiyar nazarin harkokin man fetur da ke Kaduna tare da sauya mata suna.
Yanzu cibiyar za ta riƙa suna Jami’ar Kimiyyar Ƙasa da Fasahar Injiniya ta Janar Shehu Musa Yar’Adua, domin karrama marigayi sojan kuma mai fafutikar dimokiraɗiyya.
Tinubu ya bayyana Yar’Adua a matsayin ɗaya daga cikin manyan masu gina tubalin dimokiraɗiyyar Nijeriya ta zamani, wanda hangen nesan sa ya taimaka wajen tsara tafiyar dimokiraɗiyyar ƙasar.
Shugaban ya kuma bayyana ba da lambobin yabo na ƙasa ga ɗimbin ‘yan Nijeriya da suka taka rawa a gwagwarmayar dimokiraɗiyya, yana mai cewa za a fitar da cikakken jerin sunayen waɗanda aka karrama a cikin kwanaki masu zuwa.
A ƙarshen jawabin nasa, Tinubu ya yi tsokaci kan juriya da haƙurin al’ummar Nijeriya da kuma muhimmancin tafiyar dimokiraɗiyyar da ta samo asali daga gwagwarmayar 12 ga Yuni.
Ya ce: “Shekaru ashirin da bakwai da suka gabata, mutane da dama sun yi shakkar cewa dimokiraɗiyya za ta rayu a nan saboda bambance-bambancen mu. A yau kuwa, bambance-bambancen mu ne ke ƙarfafa dimokiraɗiyyar mu.”
Ya ƙara da cewa: “Hanyar da ke gaba tana da wahala. Amma 12 ga Yuni tana tuna mana cewa ‘yan Nijeriya ba sa karyewa. Muna lanƙwasawa, muna zubar da jini, amma ba ma karyewa.”
Daga nan ya yi kira ga ‘yan ƙasa da su sabunta alƙawarin su ga manufofin dimokiraɗiyya da haɗin kan ƙasa.
Ya ce: “Mu sabunta alkawarin mu cewa wahalhalun da jaruman mu suka sha ba za su tafi a banza ba, kuma mulkin jama’a, ta hannun jama’a, domin jama’a ba zai gushe daga wannan ƙasa ba.”
Shugaban ya rufe jawabin nasa da addu’o’i ga jaruman dimokiraɗiyya da kuma cigaba da zaman lafiya da bunƙasar Nijeriya.
Ya ce: “Allah Ya albarkaci jaruman dimokuraɗiyyarmu. Allah Ya albarkaci Tarayyar Jamhuriyar Nijeriya. Allah Ya ci gaba da albarkace mu baki ɗaya. Barka da Ranar Dimokuraɗiyya.”







