Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da Ministan Abuja, Nyesom Wike, suna ƙaddamar da titin Kuje zuwa filin jirgin sama yau a Abuja
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da titin Kuje wanda ya haɗe da babbar hanyar zuwa filin jirgin sama a Abuja, inda ya ce gwamnatin sa ba ta yi watsi da ayyukan da ta gada ba, sai dai ƙara ƙarfafa su.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, wanda ya wakilce shi, ya ce kammala titin mai layuka shida wata alama ce ta cika alƙawurran Ajandar Sabuwar Fata ta gwamnati.
Tinubu ya bayyana cewa titin, wanda aka fara a 2022 aka watsar da shi, ya janyo cunkoso, ƙura da ambaliya, amma yanzu zai rage lokacin tafiya, tare da bunƙasa tattalin arziki da sauƙaƙa harkokin kasuwanci.

A nasa jawabin, Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce aikin ya kasance mai wahala amma an kammala shi domin dawo da fata ga mazauna yankin.
Ita ma Ƙaramar Ministan Abuja, Dakta Mariya Mahmoud, ta ce aikin wata babbar nasara ce wajen inganta rayuwar al’umma a Abuja.







