• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

An kusa kammala dokar kafa ’yan sandan jihohi a bisa tsarin mulki — Fadar Shugaban Ƙasa

Wakilin Mu by Wakilin Mu
June 5, 2026
in Tsaro
A A
0
An kusa kammala dokar kafa ’yan sandan jihohi a bisa tsarin mulki — Fadar Shugaban Ƙasa
Daga hagu: Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Tunji Disu; Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin; Shugaban Ma’aikata a Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila; Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu, da Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Tarayya, Lateef Fagbemi, bayan kammala taron

Daga hagu: Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Tunji Disu; Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin; Shugaban Ma’aikata a Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila; Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu, da Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Tarayya, Lateef Fagbemi, bayan kammala taron

Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa an samu gagarumin cigaba a tattaunawar kafa rundunar ’yan sandan jihohi, inda ake sa ran gabatar da gyaran kundin tsarin mulki nan ba da jimawa ba domin ba da damar aiwatar da shirin.

Shugaban Ma’aikata a Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, shi ne ya bayyana hakan bayan wata ganawa da aka yi a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja ranar Alhamis, wadda ta haɗa manyan jami’an gwamnati da shugabannin majalisun dokoki kan batun kafa ’yan sandan jihohi.

Gbajabiamila ya ce an fara nazari da tattaunawa kan yadda za a kafa rundunar tun watanni uku zuwa huɗu da suka gabata bisa umurnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kuma an samu cigaba mai yawa a aikin.

Ya bayyana cewa kafa ’yan sandan jihohi ba abu ne da za a yi cikin gaggawa ba, domin akwai batutuwan kundin tsarin mulki da dokoki da dole ne a tantance su sosai kafin aiwatarwa.

A cewar sa, yanzu hankalin masu ruwa da tsaki ya karkata ne kan yadda za a yi gyaran kundin tsarin mulki, sannan daga baya a samar da dokokin da za su ba da cikakken iko da tsarin gudanar da rundunar.

Ya ƙara da cewa yawancin ’yan Nijeriya da masu ruwa da tsaki sun amince da buƙatar kafa ’yan sandan jihohi, inda muhawarar yanzu ba ta kan ko a kafa su ko a’a ba, sai dai yadda za a samar da ingantaccen tsarin doka da gudanarwa domin su yi aiki yadda ya kamata.

Gbajabiamila ya ce za a gabatar wa da Shugaba Tinubu cikakken rahoto kan sakamakon ganawar domin ci gaba da matakan da suka dace.

A cewar sa, manufar kafa ’yan sandan jihohi ita ce ƙarfafa tsaron cikin gida, inganta tattara bayanan sirri daga matakin ƙasa da kuma bai wa gwamnatocin jihohi damar magance matsalolin tsaro cikin sauri da inganci.

Shugaba Tinubu ya sha bayyana cewa tsarin ’yan sandan jihohi yana daga cikin hanyoyin da za su taimaka wajen fuskantar ƙalubalen tsaro da ke addabar ƙasar nan, tare da ƙara kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ganawar ta samu halartar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin; Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu; Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Tarayya, Lateef Fagbemi; da Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Tunji Disu, tare da sauran manyan jami’an gwamnati.

Tags: 'yan sandan jihohiBarau JibrinFemi Gbajabiamilakundin tsarin mulki
Previous Post

‘Yan sanda sun kama wanda ake zargi da ƙirƙirar saƙon muryar Tinubu na bogi

Next Post

Isra’ila ta tura dakaru da jami’an leƙen asiri zuwa Azabaijan yayin yaƙi da Iran – CNN

Related Posts

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
EFCC ta samu nasarar hukunta mutumin da ya yi ƙoƙarin sumogar zinari mai darajar Naira biliyan 4.4 a Kano
Tsaro

EFCC ta samu nasarar hukunta mutumin da ya yi ƙoƙarin sumogar zinari mai darajar Naira biliyan 4.4 a Kano

November 17, 2026
Sojoji sun halaka ’yan ta’adda, sun ceto mutum 16, sun ƙwato babura 38 a Neja da Kebbi
Tsaro

Sojoji sun halaka ’yan ta’adda, sun ceto mutum 16, sun ƙwato babura 38 a Neja da Kebbi

November 6, 2026
Ƙungiyar Amnesty ta buƙaci bincike kan bidiyon atisayen muzaharar Izala
Tsaro

’Yan sanda sun kama matashin Izala kan bidiyon da ke tunzura rikicin addini

October 27, 2026
Ƙungiyar Amnesty ta yi tir da kisan malamin addini Sheikh Yahaya Masussuka
Tsaro

’Yan sanda a Katsina sun tabbatar da kashe Sheikh Yahaya Masussuka da abokin sa

October 26, 2026
Ƙungiyar Amnesty ta yi tir da kisan malamin addini Sheikh Yahaya Masussuka
Tsaro

Ƙungiyar Amnesty ta yi tir da kisan malamin addini Sheikh Yahaya Masussuka

October 26, 2026
Next Post
Isra’ila ta tura dakaru da jami’an leƙen asiri zuwa Azabaijan yayin yaƙi da Iran – CNN

Isra'ila ta tura dakaru da jami’an leƙen asiri zuwa Azabaijan yayin yaƙi da Iran - CNN

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!