Mai ba Shugaban Ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya ce ‘yan sanda sun kama Ifechukwu Dennis, wanda ake zargi da ƙirƙirar saƙon murya na bogi na Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta hanyar amfani da fasahar basirar zamani (AI).
A wani saƙo da ya wallafa a shafin sa na X ranar Alhamis, Onanuga ya bayyana cewa an kama Dennis ne a Birnin Benin da ke Jihar Edo, ta hannun wata ƙwararriyar tawaga daga ofishin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (IGP).
Mai magana da yawun shugaban ƙasar ya rubuta cewa: “Tawagar musamman ta IGP ta kama Ifechukwu Dennis, wanda ya ƙirƙiri muryar bogin da ya riƙa yaɗawa ga mutanen da suka yarda da ita a matsayin muryar Shugaba Tinubu.
“An kama Dennis a Benin. ‘Yan sanda za su fitar da sanarwa a hukumance.”
Kamen na zuwa ne bayan wani sautin murya mai cike da ce-ce-ku-ce da aka ƙirƙira ta amfani da AI domin ya yi kama da muryar Tinubu ya bazu sosai a soshiyal midiya.
Saƙon muryar ya ƙunshi wasu maganganu masu tayar da hankali, ciki har da zargin cewa matsalar rashin tsaro a yankin Kudu-maso-gabas an yi ta ne da gangan, cewa Tinubu ya matsa wa Peter Obi lamba ya janye takarar sa kafin babban zaɓen da ya gabata, da kuma cewa bai damu da wahalhalun da ‘yan Nijeriya suke ciki ba.
A cikin saƙon muryar an yi iƙirarin cewa: “Na roƙi Peter Obi ya janye min hanya. Ya ƙi. Yanzu zan tabbatar da cewa rashin tsaro ya shafi Kudu-maso-gabas kawai.”
Saƙon ya ƙara samun karɓuwa bayan an saka shi a cikin wani bidiyo da aka wallafa ranar 27 ga Mayu daga hannun Martins Otse, fitaccen mai fafutuka a kafafen sada zumunta wanda aka fi sani da VeryDarkMan (VDM).
Da yake mayar da martani ga bidiyon a lokacin, Onanuga ya buƙaci a kama VDM, yana zargin sa da yaɗa bayanan ƙarya.
Ya ce: “Dole ne VDM ya fuskanci hukunci saboda ya kasance mai isarwa da yaɗa sautin murya na bogi da aka danganta ga Shugaba Tinubu.
“Wannan babban misali ne na rashin amfani da soshiyal midiya yadda ya kamata.”
Ya zuwa yanzu dai rundunar ‘yan sanda ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan kamen ba, kuma ba ta bayyana irin tuhume-tuhumen da za a iya gurfanar da wanda ake zargin da su ba.







