• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Al’ummar Kudancin Kaduna sun karrama Ministan Tsaro da sarautar Sarkin Yaƙi

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
May 30, 2026
in Tsaro
A A
0
Al’ummar Kudancin Kaduna sun karrama Ministan Tsaro da sarautar Sarkin Yaƙi
Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa (ritaya), sanye da kayan yaƙi na gargajiya lokacin da aka naɗa shi Sarkin Yaƙin Kudancin Kaduna a yau Asabar a filin wasa na garin Kafanchan, Jihar Kaduna, yayin da matar sa take tsaye a gefen sa

Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa (ritaya), sanye da kayan yaƙi na gargajiya lokacin da aka naɗa shi Sarkin Yaƙin Kudancin Kaduna a yau Asabar a filin wasa na garin Kafanchan, Jihar Kaduna, yayin da matar sa take tsaye a gefen sa

Al’ummar Kudancin Kaduna sun karrama Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya), da sarautar Sarkin Yaƙin Kudancin Kaduna (Grand Commander of Southern Kaduna, GCSK) domin girmama gudunmawar da ya bayar ga ƙasa da kuma jajircewar sa wajen tabbatar da zaman lafiya, tsaro da haɗin kan ƙasa.

An yi bikin naɗin sarautar ne ranar Asabar a wani taro da aka yi a filin wasa na garin Kafanchan, wanda ya samu halartar sarakunan gargajiya, shugabannin siyasa, masu ruwa da tsaki na al’umma, ƙungiyoyin matasa da na addini, tare da mazauna yankuna daban-daban na Kudancin Kaduna da kewaye.

Da yake karɓar wannan karramawa, Musa ya gode wa al’ummar yankin bisa wannan girmamawa, inda ya bayyana Kudancin Kaduna a matsayin yanki mai albarka da cike da kyakkyawar makoma.

Ya sadaukar da lambar yabon ga dukkan ’yan Nijeriya masu kishin ƙasa da son zaman lafiya, yana mai cewa Kudancin Kaduna ya samar da fitattun maza da mata da suka yi fice a fannoni daban-daban.

Ministan ya yi kira ga matasan yankin da su kasance masu bin doka da oda tare da guje wa duk wani aiki da zai iya haifar da rikici ko aikata laifuka.

Ya jaddada cewa tsaro nauyi ne na kowa da kowa, tare da kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su haɗa kai domin kawar da matsalar rashin tsaro.

Haka kuma, ya yaba wa shugabannin al’umma kan rawar da suke takawa wajen tattara bayanan sirri, yana mai ƙarfafa su da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai cikin lokaci game da ayyukan masu laifi.

Musa ya shawarci jama’ar yankin da su ci gaba da riƙe kyawawan ɗabi’un da Kudancin Kaduna ta yi fice da su, ciki har da ƙwazo, bin doka, sadaukarwa, hidima da tawali’u.

Ya kuma jaddada cewa zaman lafiya da haɗin kai muhimman ginshiƙai ne na cigaban ƙasa, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da bai wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu goyon baya.

Ya ce a cikin shekaru uku da suka gabata, an samu ƙarin ayyukan Gwamnatin Tarayya da shirye-shiryen samun cigaba a yankin.

Shugaban Majalisar Jagororin Kudancin Kaduna, Dattijo Akau Moses (hagu), yana musabaha da Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa, yayin da Misis Musa take kallo cike da farin ciki a lokacin bikin karramawar.

Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Majalisar Jagororin Kudancin Kaduna, Dattijo Akau Moses, ya bayyana Janar Musa a matsayin jakadan yankin nagari wanda aikin sa na soja ya kawo wa Kudancin Kaduna da Nijeriya ɗaukaka.

Ya ce sadaukarwa, ƙwarewa, jarumtaka da kishin ƙasa da Ministan ya nuna su ne suka sa ya samu karɓuwa da karramawa a matakin ƙasa da ƙasa.

Ya ƙara da cewa wannan lambar yabo wata hanya ce ta amincewa da gudunmawar da ya bayar wajen tabbatar da tsaron ƙasa da kuma kasancewar sa abin koyi ga matasan Nijeriya.

Tags: Janar Christopher Gwabin MusakarramawaKudancin KadunaSarkin Yaƙi
Previous Post

 ‘Yan bindiga sun sace tsohon kakakin rundunar tsaro Janar Rabe tare da matar sa a hanyar Katsina

Next Post

CBN ya ƙara wa’adin cika ƙa’idoji da nisan zangon amfani da PoS

Related Posts

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
EFCC ta samu nasarar hukunta mutumin da ya yi ƙoƙarin sumogar zinari mai darajar Naira biliyan 4.4 a Kano
Tsaro

EFCC ta samu nasarar hukunta mutumin da ya yi ƙoƙarin sumogar zinari mai darajar Naira biliyan 4.4 a Kano

November 17, 2026
Sojoji sun halaka ’yan ta’adda, sun ceto mutum 16, sun ƙwato babura 38 a Neja da Kebbi
Tsaro

Sojoji sun halaka ’yan ta’adda, sun ceto mutum 16, sun ƙwato babura 38 a Neja da Kebbi

November 6, 2026
Ƙungiyar Amnesty ta buƙaci bincike kan bidiyon atisayen muzaharar Izala
Tsaro

’Yan sanda sun kama matashin Izala kan bidiyon da ke tunzura rikicin addini

October 27, 2026
Ƙungiyar Amnesty ta yi tir da kisan malamin addini Sheikh Yahaya Masussuka
Tsaro

’Yan sanda a Katsina sun tabbatar da kashe Sheikh Yahaya Masussuka da abokin sa

October 26, 2026
Ƙungiyar Amnesty ta yi tir da kisan malamin addini Sheikh Yahaya Masussuka
Tsaro

Ƙungiyar Amnesty ta yi tir da kisan malamin addini Sheikh Yahaya Masussuka

October 26, 2026
Next Post
Yadda asusun kuɗaɗen waje na Nijeriya zai cika maƙil, bayan CBN ya yi wa naira allurar ƙarin ƙarfin wujijjiga dala a tsakiyar kasuwa

CBN ya ƙara wa’adin cika ƙa'idoji da nisan zangon amfani da PoS

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!