Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya Alhaji Murtala Sule Garo murnar rantsar da shi a matsayin sabon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, wanda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi a yau Talata.
Gwamnan ya naɗa Garo ne domin cike gurbin da Comrade Aminu Abdulsalam ya bari, bayan murabus ɗin da ya yi biyo bayan sauya sheƙar gwamnan zuwa jam’iyyar APC.
Murtala Garo, mai shekara 48, gogaggen ɗan siyasa ne wanda ya riƙe muƙamai daban-daban, ciki har da Shugaban Ƙaramar Hukumar Kabo, Kwamishinan Ma’aikatar Ƙananan Hukumomi da Al’amuran Masarautu a ƙarƙashin gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, kuma ɗan takarar Mataimakin Gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen 2023.
Shugaban Ƙasa ya jinjina wa Gwamna Yusuf bisa wannan naɗin, yana mai bayyana cewa matakin zai ƙarfafa haɗin kan da ake buƙata a cikin sahu da jerin membobin jam’iyyar APC a Jihar Kano.
Haka kuma Shugaban ya yi kira ga ɗaukacin masu ruwa da tsaki da su mara wa gwamnan da mataimakin sa baya domin ciyar da jihar gaba.
Ya buƙaci sabon mataimakin gwamnan da ya yi aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamna domin samar da shugabanci na gari da zai bunƙasa jihar.
A ƙarshe, Tinubu ya yi wa Garo fatan alheri a wannan sabon nauyi da aka dora masa.







