Babban ɗan siyasa Peter Obi ya bayyana aniyar sa ta ficewa daga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), yana mai danganta hakan da ƙarin rikice-rikicen cikin gida, gurɓataccen yanayin siyasa da kuma maimaituwar matsalolin da suka addabe shi a lokacin da yake cikin Labour Party Nigeria.
A cikin wata sanarwa da ya sanya hannu da kan sa kuma ya wallafa ta a shafukan sa na soshiyal midiya a yau Lahadi, tsohon gwamnan na Jihar Anambra ya ce ya yanke wannan shawara mai wahala ne bayan zurfin tunani, yana mai jaddada cewa matakin ya zama dole duk da abin da ya kira “duk wata takura.”
“Na farka yau da safe bayan na dawo daga coci da zuciya mai cike da tunani… kuma na ji dole in bayyana wannan tunani,” inji Obi.
Ya ce da yawa daga cikin ’yan Nijeriya ba sa fahimtar “raɗaɗin shiru” da kuma ƙalubalen sirri da waɗanda ke ƙoƙarin yi wa ƙasa hidima a fagen siyasa suke fuskanta.
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar ya zayyana hoto mai duhu na halin siyasar Nijeriya a yanzu, yana mai cewa tana ƙara zama mai tsauri, mai sanyaya gwiwa kuma mai gurɓata yanayi.
A cewar sa, tsarin da ya kamata ya kare ’yan ƙasa da samar masu da dama, sau da yawa yana aiki ne a kan su maimakon taimaka masu.
Ya ce: “Yanzu muna rayuwa a cikin yanayi mai ƙara gurɓacewa, inda tsarin da ya kamata ya kare da samar da dama… sau da yawa yana aiki a kan jama’a.”
Obi ya nuna tsoratarwa, rashin tsaro da kuma tsananin sa ido daga jama’a a matsayin wasu daga cikin siffofin yanayin siyasar da ake ciki yanzu.
Ya kuma nuna takaicin sa kan abin da ya kira rashin haɗin kai na gaskiya, har ma a tsakanin wasu da ke bayyana goyon bayan su gare shi a fili.
“Wasu da ke nuna suna tare da kai a fili, a ɓoye suna nesanta kan su ne ko su shiga cikin sukar da ba ta dace ba,” inji shi.
Tsohon gwamnan ya ƙara da cewa sau da yawa ana fassara tawali’u a matsayin rauni, yayin da ake kallon jinƙai da tsare gaskiya a matsayin wawanci a siyasar Nijeriya.
Duk da waɗannan ƙalubale, Obi ya bayyana cewa ficewar sa daga ADC ba ta samo asali daga wata ƙiyayya ta kai-tsaye da shugabannin jam’iyyar ba.
Ya wanke David Mark da kuma Atiku Abubakar, yana mai cewa babu wanda ya yi masa wani rashin adalci.
Ya ce: “Ina so in fayyace: shawarar da na yanke ta barin ADC ba saboda shugaban mu mai girma ya yi mini wani abu mara kyau ba, haka kuma ba saboda Atiku Abubakar ko wani daga cikin shugabanni masu daraja sun yi mini laifi ba ne.”
Maimakon haka, Obi ya danganta ficewar sa da maimaituwar matsalolin da suka addabi jam’iyyar Labour a lokacin da yake cikin ta.
A cewar sa, ADC na ƙara nutsewa cikin rarrabuwar kai, shari’o’i marasa iyaka da kuma katsalandan ɗin wasu daga waje.
“Wannan tsarin Nijeriya da wakilan sa da suka haifar da rikice-rikice marasa amfani… yanzu suna ƙoƙarin shiga ADC, tare da shari’o’i marasa iyaka, rikice-rikice na cikin gida, zargi da rarrabuwa,” inji shi.
Tsohon gwamnan ya yi kuka da cewa sau da yawa ba a daraja gudunmawar gaskiya da sadaukarwa a cikin tsarin siyasa.
Ya ce: “Ko a wuraren da mutum yake aiki da gaskiya, wani lokaci ana mu’amala da shi kamar baƙo… kamar dai gudunmawar gaskiya wata alfarma ce da ake jurewa maimakon a yaba mata.”
Obi ya jaddada cewa duk da shawarar da ya yanke na barin ADC, har yanzu yana fuskantar suka, hare-hare da tambayoyi kan halayyar sa, duk da ƙoƙarin sa na tsare gaskiya wajen cigaban ƙasa.
Yayin da ya duba halin da ƙasar nan take ciki gaba ɗaya, Obi ya tambayi irin ƙimomin da ke tasiri kan yadda jama’a ke fahimta a Nijeriya, yana tambayar dalilin da ya sa gaskiya da kulawa da dukiyar ƙasa ba sa samun daraja.
Ya ce: “Me ya sa yin abin da ya dace ake ɗauka a matsayin kuskure ne a ƙasar mu? Me ya sa ba a daraja gaskiya?”
Obi ya sake jaddada cewa burin sa na siyasa ba wai saboda kwaɗayin mulki ko muƙami ba ne, sai don ganin Nijeriya mai kyau da jinƙai.
“Ba na ɗokin zama Shugaban Ƙasa… ina ɗokin ganin al’umma da za ta iya ta’azantar da uwa da aka sace ko aka kashe ɗan ta,” inji shi.
Ya yi nuni da matsalolin tsaro, talauci da gudun hijira da ke ƙara tsananta a ƙasa, yana mai cewa wahalar talakawa ita ce babban abin damuwar sa.
Duk da takaici da ƙalubalen siyasa, Obi ya kammala saƙon sa da kyakkyawar fata, yana mai cewa har yanzu yana da yaƙinin cewa Nijeriya za ta iya shawo kan matsalolin ta ta hanyar shugabanci nagari da ya ginu kan adalci, jinƙai da samar da daidaito ga kowa.
Ya ce: “Duk da abubuwan da suka faru, ina nan daram. Ina da cikakken imani cewa Nijeriya za ta iya zama ƙasa mai shugabanci nagari bisa adalci, jinƙai da damar daidaito ga kowa.
“Sabuwar Nijeriya mai yiwuwa ce.”







