• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Yadda CBN ke ta ƙoƙarin daƙile malejin hauhawar farashi zuwa ƙasa da kashi 10 bisa 100

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
April 29, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Yadda asusun kuɗaɗen waje na Nijeriya zai cika maƙil, bayan CBN ya yi wa naira allurar ƙarin ƙarfin wujijjiga dala a tsakiyar kasuwa
Hedikwatar CBN a Abuja

Hedikwatar CBN a Abuja

Ƙudirin Nijeriya na daƙile hauhawar farashi zuwa ƙasa da kashi 10 bisa 100, yana nan daram duk da ɗan ƙarin da aka samu a alƙaluman watan Maris sakamakon rikicin Gabas ta Tsakiya da sauran ƙalubalen tattalin arziki.

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, (CBN), Olayemi Cardoso, ya bayyana cewa Nijeriya za ta cimma mafi ƙanƙantar malejin hauhawar farashin da bai kai ma’aunin kashi 10 bisa ba, duk da cewa hauhawar farashin kayayyaki ya tashi zuwa kashi 15.38 cikin ɗari a watan Maris daga kashi 15.06 cikin ɗari a watan Fabrairu.

Hasashen ci gaban tattalin arziki da juriyar fuskantar girgizar tattalin arzikin duniya duk da ƙalubale na daga cikin sakamakon gyaran fuskar harkokin kuɗi da CBN ke jagoranta domin gina tattalin arziki mai ƙarfi.

A duniya baki ɗaya, an amince cewa hauhawar farashi na a sahun gaba wajen haifar da cikas ga ci gaba, sannan kuma jibadau ne, wato babban nauyi ga talakawa.

A Nijeriya kuwa, gyare-gyaren tattalin arziki na sama da shekaru biyu da CBN ke yi, sun ƙarfafa tattalin arzikin ƙasar, tare da shirya shi don jurewa girgiza da kuma bunƙasa duk da matsaloli iri-iri.

Yanzu Nijeriya tana cikin matsayi mai kyau wajen jure wa matsin tattalin arziki daga ƙasashen waje. Akwai fahimta da yabo mai ƙarfi cewa gyare-gyaren tattalin arzikin Nijeriya sun ƙara wa masu zuba jari na gida da na ƙasashen waje ƙwarin gwiwa.

Da yake jawabi yayin taron Bankin Bada Lamuni na Duniya, ‘International Monetary Fund’ (IMF) da Bankin Duniya a Amurka, Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya ce tasirin rikicin Gabas ta Tsakiya wanda ya jawo ɗan tashin hauhawar farashi a watan Maris, ya kasance cikin wani ɗan lokaci mai iyaka.

Ya ce ikon tattalin arzikin Nijeriya wajen shawo kan matsalolin da rikicin ya haifar yana nuna kyakkyawan sakamakon gyare-gyare, ciki har da daidaituwar canjin kuɗi, ƙaruwar adadin ajiyar kuɗaɗen waje da kuma ingantaccen tsarin manufofin kuɗi.

Cardoso ya ce: “Ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba wajen ƙara ƙarfin tattalin arziki da kuma ci gaba da tafiya kan manufar mu ta rage hauhawar farashi zuwa matakin da tsananin sa bai kai kashi 10 bisa ɗari ba. Duk da duk abin da ke faruwa, za mu ci gaba da bin wannan hanya.”

Tuni dai Hukumar Kididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa (NBS), ƙarƙashin jagorancin Babban Mai Kididdiga na Ƙasa, Adeyemi Adeniran, ya bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ta kai kashi 15.38 cikin ɗari a watan Maris 2026 daga kashi 15.06 cikin ɗari a watan Fabrairu.

Wannan shi ne karo na farko cikin watanni 12 da aka samu ƙaruwa tun bayan da hauhawar farashi ta fara raguwa tun daga watan Afrilu 2025.

NBS ta ce hauhawar farashin a watan Maris 2026 ya kai kashi 15.38 cikin ɗari idan aka kwatanta da kashi 27.35 cikin ɗari a watan Maris 2025.

Hukumar ta bayyana cewa hauhawar farashin ya ƙaru da ɗigo 0.32 idan aka kwatanta da watan Fabrairu 2026.

A wata-wata kuwa, hauhawar farashi a watan Maris 2026 ta kai kashi 4.18 cikin ɗari, wanda ya fi na watan Fabrairu 2026 da kashi 2.17.

Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya kuma umurci masu kula da harkokin tattalin arziki su samar da manufofi da za su rage tasirin rikicin Gabas ta Tsakiya ga talakawa.

Matakan CBN Don Rage Hauhawar Farashi:

CBN ya ce gyare-gyaren tsarin tattalin arziki sun fara yin tasiri a faɗin tattalin arziki, suna taimakawa wajen daidaita darajar naira da rage adadin ladar kuɗin rance yayin da hauhawar farashi ke sauka a hankali.

A cewar CBN, matakan manufofin kuɗi da aka ɗauka wani ɓangare ne na dabarar dawo da daidaiton tattalin arziki bayan shekaru na matsin tattalin arziki da ƙalubalen kuɗaɗen gwamnati.

Waɗannan ci gaba suna nuna jajircewar shugabancin bankin wajen dawo da kwanciyar hankali a tsarin kuɗi, yayin da rage kuɗin ruwa na rance ke zama ɗaya daga cikin sakamakon manufofin CBN.

CBN ya ce haɗa manufofin kuɗi da na kasafin gwamnati abu ne mai muhimmanci musamman a lokacin da fasahar zamani da harkokin kuɗi ta dijital ke canza tsarin kuɗi.

A ƙarƙashin jagorancin Cardoso, CBN na ƙoƙarin samar da hanyoyi daban-daban na samun dala domin ƙara shigar kuɗin waje, samar da damar samun dala ga masana’antu da masu amfani na buƙatun yau da kullum na dole.

CBN ya kuma hanyoyin shigar dala a cikin ƙasa, ta hanyoyin inganta adadin kuɗaɗen da ’yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje ke aikowa gida, zuwa bayar da lasisi ga sababbin kamfanonin canja kuɗi na duniya (IMTOs), da aiwatar da tsarin kasuwar canjin kuɗi tsakanin mai siya da mai sayarwa.

Wannan ya taimaka wajen ƙara yawan adadin ajiyar kuɗin waje da kuma tabbatar da nagartar naira.

Saboda muhimmancin shigar kuɗin waje wajen tabbatar da daidaiton manufofin kuɗi da kasafi, CBN na ƙara ƙoƙarin jawo ƙarin kuɗin shiga ga tattalin arziki.

Kuɗin da ’yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje ke aikowa gida, wanda ake kiyasta ya kai dala biliyan 23 a shekara, na ci gaba da zama muhimmiyar hanyar samun kuɗin waje.

Cardoso ya ce Nijeriya na samun kusan dala miliyan 600 a kowane wata daga waɗannan kuɗaɗen.

Ya ce raguwar hauhawar farashi, kwanciyar hankali a kasuwar canjin kuɗi da ƙaruwar ajiya sun ƙara wa masu zuba jari ƙwarin gwiwa.

IMF ta yaba wa manufofin tattalin arzikin Nijeriya, yana mai cewa gyare-gyaren cikin gida sun fara nuna sakamako.

Tags: CBNfarashi
Previous Post

Rikicin shugabanci a ADC: Ɓangaren David Mark ya rubuta wa CJN takarda, ya roƙi a gaggauta yanke hukunci

Next Post

Hajjin 2026: Gwamnatin Tarayya na nazarin hanyoyin rage tsadar man jiragen sama, ta kuma ba da tabbacin za a yi jigilar maniyyata ba tare da tangarɗa ba

Related Posts

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’

November 25, 2026
Muna samun nasarori a tsaro, ilimi da ababen more rayuwa – Tinubu 
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya ware Naira biliyan 450 domin tallafa wa manoma 500,000

November 22, 2026
Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40

November 19, 2026
CBN ya naɗa kamfanoni takwas domin kula da fitar da ɗanyen mai da iskar gas
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN da NNPCL sun ƙulla yarjejeniyar ƙarfafa tattalin arziki da samar da kuɗaɗen zuba jari a ɓangaren makamashi

November 18, 2026
CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su

November 17, 2026
Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS

November 16, 2026
Next Post
Hajjin 2026: Gwamnatin Tarayya na nazarin hanyoyin rage tsadar man jiragen sama, ta kuma ba da tabbacin za a yi jigilar maniyyata ba tare da tangarɗa ba

Hajjin 2026: Gwamnatin Tarayya na nazarin hanyoyin rage tsadar man jiragen sama, ta kuma ba da tabbacin za a yi jigilar maniyyata ba tare da tangarɗa ba

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!