Fagen siyasar adawa a Nijeriya ya ɗauki sabon salo mai cike da muhimmanci a ranar Asabar, yayin da wata babbar gamayyar jam’iyyu ta yanke shawarar binne duk wani tsohon saɓani da je tsakanin su tare da haɗa kai domin goyon bayan ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya domin ƙalubalantar jam’iyyar APC mai mulki a babban zaɓen 2027.
Wannan matsaya, wadda aka sanya wa suna “Sanarwar Ibadan”, ita ce babban sakamakon taron ƙasa mai muhimmanci na jam’iyyun adawa da aka gudanar a yau Asabar, 25 ga Afrilu, 2026, a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, abin da mahalarta suka bayyana a matsayin muhimmin mataki a cigaban dimokuraɗiyyar ƙasar nan.
Jam’iyyun da suka halarci taron sun haɗa da Peoples Democratic Party (PDP), African Democratic Congress (ADC), Peoples Redemption Party (PRP), New Nigeria Peoples Party (NNPP), National Democratic Coalition (NDC), Labour Party (LP), Action Peoples Party (APP), Accord Party, Allied Peoples Movement (APM), Action Alliance (AA), Democratic Labour Party (DLA), Young Progressives Party (YPP), Action Democratic Party (ADP), Zenith Labour Party (ZLP), da sauran su.
Da yake gabatar da sanarwar a madadin jagororin gamayyar, Shugaban PDP na Ƙasa, Taminu Turaki (SAN), ya bayyana cewa tsaida ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya ba dabara ce kawai ba, wata wajabciyar hanya ce ta ceto Nijeriya daga abin da ya kira ƙara ƙamfar shugabanci ta APC.
A cewar sanarwar, babban burin gamayyar shi ne dakatar da abin da take gani a matsayin yunƙurin mayar da ƙasar ƙarƙashin jam’iyya ɗaya.
Ƙungiyar adawar ta zargi APC da shirin tsayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takara shi kaɗai a zaɓen 2027, lamarin da ta ce za ta fuskanta da tsayayyen haɗin kai na siyasa.
“Za mu yi aiki domin tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya a zaɓen 2027, wanda duk jam’iyyun adawa da suka shiga wannan gamayya za su amince da shi kuma su mara masa baya, domin ceto ƙasar mu da talakawan mu masu jure wahala,” inji sanarwar.
Baya ga dabarun zaɓe, taron ya yi kakkausan suka ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kan ta ta Ƙasa (INEC), inda ya nuna rashin amincewa da shugaban ta, Farfesa Joash Amupitan. Gamayyar ta zarge shi da nuna son kai a fili ga jam’iyya mai mulki, tana mai gargaɗin cewa ci gaba da jagorancin sa na iya raunana sahihancin tsarin zaɓe tare da jefa ƙasa cikin rikici.
Sanarwar ta buƙaci a maye gurbin sa da mutum ɗan ba-ruwan-mu kuma mai adalci wanda zai dawo da amincewar jama’a ga hukumar zaɓe.
A cikin bayyana faɗaɗɗen ajandar gyaran ta, Sanarwar Ibadan ta buƙaci Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta gaggauta duba tare da yi wa wasu tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2026 gyara, waɗanda ‘yan adawar ke ganin suna barazana ga sahihancin zaɓe.
Gamayyar ta kuma soki sababbin ƙa’idojin da INEC ta fitar, tana mai cewa an tsara su ne domin hana jam’iyyun adawa samun damar takara yadda ya kamata. Ta buƙaci a tsawaita wa’adin gudanar da zaɓen fidda gwani na jam’iyyu zuwa ƙarshen Yuli 2026 domin bai wa kowa damar shiga da kuma ƙarfafa dimokiraɗiyya cikin gida.
Sanarwar ta kuma buƙaci a saki fitattun ‘yan siyasa da ake zargin ana muzgunawa ko tsare su kan laifukan da ake iya bayar da beli, tana mai kallon irin waɗannan matakai a matsayin take haƙƙin ɗan’amdam da ƙa’idojin dimokiraɗiyya.
Duk da matsalolin da aka bayyana, shugabannin adawa sun yaba wa ‘yan Nijeriya bisa juriyar su duk da ƙarin matsin siyasa da tattalin arziki.
Sun sake jaddada aniyar su ta ci gaba da kare dimokiraɗiyyar jam’iyyu masu yawa tare da yin tir da duk wani yunƙuri na murƙushe gasa ta siyasa.
Taron ya kuma yaba wa Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, bisa karɓar baƙuncin taron, inda ya bayyana Ibadan a matsayin dandalin wani taro na tarihi gabanin zaɓen 2027.







