Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammad Sanusi II, ya halarci taron manyan daraktocin duniya na kamfanin sadarwa na MTN da aka yi a ƙasar Afrika ta Kudu.
Ya samu gayyatar zuwa taron ne daga Ƙaramin Ofishin Jakadancin Nijeriya da ke Johannesburg, babban birnin ƙasar Afrika ta Kudu ƙarƙashin jagorancin Ambasada (Mrs) Ninikanwa Okay-Uche.
Bayani daga Fadar Kano ya nuna cewa maƙasudin gayyatar shi ne domin Sarkin ya gana da ‘yan Nijeriya mazauna ƙasar suna kasuwanci ko aiki a can don ya ƙara ƙarfafa masu gwiwa don su gayyaci kamfanonin Afrika ta Kudu su zo su saka jari, kuma su kafa kamfanoni a Nijeriya.


Mai Martaba Sarki ya je ne tare da maiɗakin sa, Hajiya Sa’adatu Sanusi, da Galadiman Kano, Alhaji Munir Sanusi, da Jakadan Nijeriya a ƙasar Botswana kuma Kogunan Kano, Ambasada Mohammed Sani.
Sarki da jama’ar sa sun je ne a ranar Juma’a da ta gabata, 10 ga Afrilu, 2026.







