• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Martanin Nijeriya ga Amurka: Muna nan daram, muna samun cigaba a fannin tsaro

ALI KANO by ALI KANO
April 9, 2026
in Labarai
A A
0
Martanin Nijeriya ga Amurka: Muna nan daram, muna samun cigaba a fannin tsaro
Alhaji Mohammed Idris

Alhaji Mohammed Idris

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa Nijeriya tana ci gaba da samun nasarori a fannin tsaro kuma tana nan daram, duk da matakin da Amurka ta ɗauka na janye ma’aikatan ta daga ofishin jakadancin ta da ke Abuja.

Idan kun tuna, a yau ne wata sabuwar sanarwa ta fito daga Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka kan tafiye-tafiye, inda gwamnatin ta gargaɗi ‘yan ƙasar ta da ke aikin a ofishin ta na diflomasiyya da ke Abuja da su fice daga Nijeriya.

Ta ce laifuffuka, ta’addanci, sace mutane, da rikicin cikin gida su ne dalilan ta na sabunta gargaɗin.

Ta kuma shawarci Amurkawa masu niyyar zuwa Nijeriya da su canza shawara.

A wata sanarwa da ya fitar a yau Alhamis, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce wannan matakin da Amurka ta ɗauka wata hanya ce ta kariya bisa tsarin cikin gida, wanda hakan ba ya nuna ainihin yanayin tsaro na ƙasar baki ɗaya.

Ya ce: “Duk da cewa akwai wasu ƙalubalen tsaro a wasu yankuna, babu rushewar doka da oda gaba ɗaya, kuma mafi yawan sassan ƙasar nan suna cikin kwanciyar hankali.”

A cewar sa, hukumomin tsaro suna ci gaba da samun nasarori ta hanyar haɗin gwiwar sojoji, amfani da bayanan sirri, da kuma inganta aiki tare tsakanin hukumomi, wanda ke rage barazanar tsaro a yankunan da abin ya shafa.

Ya ƙara da cewa samamen baya-bayan nan sun daƙile ayyukan ƙungiyoyin masu aikata laifi tare da rage hare-haren da ake kaiwa, musamman a yankunan da suke fuskantar barazana.

“Hukumomin tsaron mu suna ci gaba da kare rayuka da dukiyoyi, kuma sakamakon waɗannan ƙoƙari yana ƙara bayyana a fili,” inji shi.

Ministan ya jaddada cewa a buɗe Nijeriya take ga kasuwanci, yawon buɗe ido da zuba jari, yana mai cewa gyare-gyaren tattalin arziki suna ƙara ƙarfafa amincewar masu zuba jari da inganta matsayin ƙasar a idon duniya.

Ya bayyana cewa har yanzu abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa da masu zuba jari suna ci gaba da mu’amala da Nijeriya, abin da ke nuna amincewar su da kwanciyar hankali da makomar ƙasar.

Duk da amincewa cewa kowace ƙasa tana da ’yancin fitar da irin waɗannan shawarwari, Gwamnatin Tarayya ta buƙaci a riƙa ba da rahotanni masu daidaito da sababbin bayanai da ke nuna irin cigaban da ake samu.

Idris ya ce: “Muna kira ga abokan hulɗar mu na ƙasa da ƙasa da su ci gaba da tuntuɓar hukumomin Nijeriya domin samun cikakken bayani na halin da ake ciki a ƙasa,” inji shi.

Gwamnatin ta sake tabbatar da jajircewar ta wajen inganta tsaro, kare rayuka da dukiyoyi, tare da tabbatar wa da al’ummar duniya cewa Nijeriya ƙasa ce mai aminci da maraba ga kowa.

Tags: AmurkadiflomasiyyamartaniMohammed IdrisNijeriya
Previous Post

Amurka ta fara kwashe ma’aikatan ofishin jakadancin ta na Abuja

Next Post

EFCC ta kama makarantar ‘yan damfarar intanet a Abuja, ta cafke mutum 31

Related Posts

Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista
Siyasa

Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista

May 5, 2026
Ranar ’Yancin ’Yan Jarida ta Duniya: Nijeriya na neman a haɗa gwiwa a yaƙi masu yaɗa labaran ƙarya
Labarai

Ranar ’Yancin ’Yan Jarida ta Duniya: Nijeriya na neman a haɗa gwiwa a yaƙi masu yaɗa labaran ƙarya

May 4, 2026
Kwankwaso da Obi sun koma NDC
Siyasa

Kwankwaso da Obi sun koma NDC

May 3, 2026
Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi
Siyasa

Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi

May 3, 2026
Shettima ya ƙaddamar da jigilar maniyyatan Hajjin bana da kwashe alhazai 500 a Abuja
Labarai

Shettima ya ƙaddamar da jigilar maniyyatan Hajjin bana da kwashe alhazai 500 a Abuja

May 3, 2026
Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC
Siyasa

Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC

May 1, 2026
Next Post
EFCC ta kama makarantar ‘yan damfarar intanet a Abuja, ta cafke mutum 31

EFCC ta kama makarantar 'yan damfarar intanet a Abuja, ta cafke mutum 31

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!