• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Amurka ta fara kwashe ma’aikatan ofishin jakadancin ta na Abuja

ALI KANO by ALI KANO
April 9, 2026
in Labarai
A A
0
Tsaro: Nijeriya da Amurka sun ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa don kare ’yancin addini da rayukan jama’a
Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Shugaba Donald Trump

Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Shugaba Donald Trump

Gwamnatin Amurka ta umurci ma’aikatan ofishin jakadancin ta da ke Abuja waɗanda ba su taka wata muhimmiyar rawa da su fice daga Nijeriya tare da iyalan su, tana mai gargaɗin cewa su ma duk wasu ‘yan ƙasar ta masu niyyar zuwa Nijeriya su canza shawara saboda abin da ta kira “taɓarɓarewar yanayin tsaro” a faɗin ƙasar.

Umurnin yana ƙunshe ne cikin wata sabuwar sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar kan tafiye-tafiye.

A cikin sanarwar, gwamnatin Amurka ta bayyana laifuffuka, ta’addanci, sace mutane, da rikicin cikin gida a matsayin manyan dalilan sabunta gargaɗin.

Wannan mataki, wanda ya fara aiki daga ranar 8 ga Afrilu, 2026, ya sanya Nijeriya a matakin “Level 3: A sake nazarin tafiya,” yayin da aka ware wasu jihohi a matsayin “Level 4: Kada a yi tafiya,” wato matakin haɗari mafi girma.

Sabunta sanarwar ta ƙara jerin jihohin da ake ganin suna da haɗari, inda aka haɗo da Filato, Jigawa, Kwara, Neja, da Taraba, wanda ya kai adadin jihohin “Kada a yi tafiya” zuwa 23.

Jihohin da aka lissafa a Arewa sun haɗa da Borno, Yobe, Adamawa (arewacin jihar), Bauchi, Gombe, Kaduna, Kano, Katsina, Sokoto, Zamfara, Kogi, Kwara, Niger, Filato, Taraba, da Jigawa, inda sanarwar ta ambaci ta’addanci, fashi da makami, sace mutane, da rikicin cikin gida.

A Kudu da Kudu maso Gabas kuma, jihohin Abiya, Anambra, Bayelsa, Delta, Inugu, Imo, da Ribas — ban da Fatakwal — an kuma yi musu alama saboda laifuka, sace mutane, da tashin hankali.

Gwamnatin Amurka ta yi gargaɗin cewa laifuffuka masu tsanani kamar fashi da makami, ƙwacen mota, da satar mutane don karɓar kuɗin fansa har yanzu suna yawaita, tare da cewa baƙi, musamman ‘yan ƙasar Amurka, sukan zama abin kai wa hari.

Ta kuma yi kashedin cewa hare-haren ‘yan ta’adda na iya faruwa a wuraren jama’a kamar kasuwanni, otal-otal, wuraren ibada, da manyan taruka.

Sanarwar ta nuna damuwa kan harkokin kiwon lafiya, inda ta bayyana su a matsayin masu rauni kuma marasa daidaito idan aka kwatanta da ƙa’idojin ƙasa da ƙasa.

Sai dai Ma’aikatar Harkokin Wajen ta shawarci ‘yan ƙasar Amurka da dole su yi tafiya zuwa Nijeriya da su shiga shirin Smart Traveler Enrollment Program, su guji manyan taruka, su ƙara kula da tsaro, kuma su tsara hanyoyin kare kan su.

Wannan sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da ake fama da tashin hankali a duniya, kuma ta jawo muhawara a tsakanin masu lura da al’amura a Nijeriya, inda wasu ke nuna damuwa kan lokacin da aka fitar da ita da kuma yiwuwar tasirin ta ga martabar ƙasar a idon duniya da kuma hangen tsaro.

Sanarwar ta fito ne ƙasa da sa’o’i 24 bayan Amurka da Isra’ila sun amince da buƙatar tsagaita wuta na makonni biyu a yaƙin da suke fafatawa.

Haka kuma sanarwar ta biyo bayan jerin kalamai masu tada hankali da Shugaban Amurka Donald Trump ya furta waɗanda suka shafi shugabancin Nijeriya.

A baya, Trump ya yi zargin ana kisan kiyashin Kiristoci a Nijeriya ba tare da ya kawo wata hujja ba, kalaman da suka gabaci hare-haren sama na Amurka a Jihar Sokoto a daren Kirsimeti.

A baya-bayan nan kuma, bayan Amurka ta tsagaita wuta tsakanin ta da Iran, Trump ya ambaci Nijeriya dangane da abin da ya kira rahotannin ƙarya da aka miƙa wa gidan talbijin na CNN.

Masu lura da harkokin siyasa suna tambayar ko wannan gargaɗin tsaro ya samo asali ne daga ainihin tantance barazana ko kuma wani matsin lamba ne na diflomasiyya gabanin babban zaɓen 2027 na Nijeriya, inda ake sa ran Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai nemi wa’adi na biyu.

Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, babu wata amsa ta hukuma daga mahukuntan Nijeriya, amma masana suna cewa wannan ci gaba na iya shafar hulɗar diflomasiyya, yanke shawarar tafiye-tafiye, da kuma amincewar masu zuba jari yayin da ƙasar ke shirin manyan harkokin siyasa da tattalin arziki a nan gaba.

* Tare da rahoton PRNigeria

Previous Post

ADC ta yi da zanga-zanga kan ƙin amincewar da INEC ta yi da shugabancin Mark

Next Post

Martanin Nijeriya ga Amurka: Muna nan daram, muna samun cigaba a fannin tsaro

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Martanin Nijeriya ga Amurka: Muna nan daram, muna samun cigaba a fannin tsaro

Martanin Nijeriya ga Amurka: Muna nan daram, muna samun cigaba a fannin tsaro

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!