Matar tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kan ta ta Kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega, wato Hajiya Hadiza Attahiru Jega, ta rasu.
A cikin wata sanarwa da iyalan ta suka fitar a yau Lahadi, sun tabbatar da rasuwar ta tare da bayyana cewa za a yi sallar jana’izar ta bayan sallar Azahar da misalin ƙarfe 1:30 na rana a Masallacin Ƙasa da ke Abuja.
A halin yanzu, Farfesa Jega yana aiki a matsayin Mataimakin Shugaban Kwamitin aiwatar da gyaran harkokin kiwo na Shugaban Ƙasa (PLRIC), mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan bunƙasa harkokin kiwo, sannan kuma shi ne Shugaba (Pro-Chancellor) na Jami’ar Jihar Nasarawa da kuma Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Marigayiya Hajiya Hadiza Jega ta shahara wajen tallafa wa harkokin ilimi da cigaban al’umma, musamman a Arewacin Nijeriya.
Iyalan ta sun yi addu’ar Allah ya jiƙan ta da rahama, ya saka mata da gidan Aljannar Firdausi, tare da roƙon abokai da ‘yan’uwa da masu fatan alheri da su riƙa tunawa da su cikin addu’o’i a wannan lokaci na jimami.
Jami’ar Bayero, Kano, inda Farfesa Jega ya taɓa zama Mataimakin Shugaban Jami’a, ita ma ta ba da sanarwar rasuwar tare da jajanta wa Farfesan.
Jami’ar ta ce a cikin sanarwar: “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Cikin cikakkimen miƙa wuya ga nufin Allah, muna ba da sanarwar rasuwar matar tsohon Mataimakin Shugaban Jami’armu, Farfesa Attahiru Jega, OFR.
“Za a yi sallar jana’izar ta nan take bayan sallar Azahar a Masallacin Ƙasa da ke Abuja a yau Lahadi, 5 ga Afrilu, 2026.
“Muna roƙon Allah ya gafarta mata kurakuran ta, ya kuma sanya ta a Aljannatul Firdausi. Allah ya ba iyalan ta haƙuri da juriyar wannan rashi. Amin.”







