Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta bayyana aniyar ta ta ci gaba da gudanar da tarurrukan ta na ƙasa da na yankuna, inda ta yi watsi da gargaɗin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kan ta ta Ƙasa (INEC) da shugaban ta, Farfesa Joash Amupitan, suka bayar.
Wannan sabon labarin ya nuna yadda rikici ya tsananta tsakanin jam’iyyar adawa da hukumar zaɓe kan yadda ake fassara umurnin kotu da ke aiki, da kuma iyakar ikon INEC na sa ido da kula da harkokin jam’iyyu.
Shugaban INEC, Amupitan, ya bayyana a wata hira da ya yi a gidan talbijin na Arise News cewa ya kamata jam’iyyar ta dakatar da shirye-shiryen ta, yana mai gargaɗin cewa ci gaba da su na iya saɓa wa umurnin da kotu ta bayar, kuma hakan na iya sa a soke sakamakon da zai fito daga irin waɗannan tarurruka.
Sai dai ADC ta yi gaggawar ƙin amincewa da wannan gargaɗi, tana mai cewa an yi kuskuren fassara doka da kuma hukuncin kotu.
A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na ƙasa na jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya fitar, jam’iyyar ta jaddada cewa za ta ci gaba da gudanar da taron ta cikin cikakken bin doka, tana zargin INEC da wuce iyakar ikon da kundin tsarin mulki ya ba ta.
“ADC za ta ci gaba da ayyukan ta cikin cikakken bin doka,” inji sanarwar, ta ƙara da cewa babu wani umurnin kotu da ya hana jam’iyyar gudanar da babban taro ko ƙaramin taro.
Babban abin da ke jawo saɓani shi ne yadda ake fassara umurnin Kotun Ɗaukaka Ƙara na ci gaba da riƙe halin da ake ciki kafin rikici — wata ƙa’ida ta doka da ke buƙatar a bar al’amura yadda suke kafin rikicin ya taso.
Yayin da INEC ke ganin wannan umurnin na nufin dakatar da duk wani aiki na jam’iyya da zai iya shafar shari’ar da ke gaban kotu, ADC na ganin wannan fassara kuskure ce kuma ba ta da tushe a doka.
A cewar Abdullahi, irin wannan umurni na kariya ana yi ne domin hana ɗaukar matakan da ba za a iya gyarawa ba kan shari’a, ba wai domin hana jam’iyya gudanar da harkokin ta na cikin gida ba.
“Ƙoƙarin faɗaɗa ma’anar ‘status quo’ ya zama kamar haramta duk wata harkar gudanar da jam’iyya gaba ɗaya, abu ne da aka zaɓa aka karkatar kuma ba daidai ba ne a doka,” inji shi.
Jam’iyyar ta kuma zargi INEC da yunƙurin tsoma baki cikin harkokin ta na cikin gida da sunan sa-ido, tana mai gargaɗin cewa irin wannan mataki na iya raunana tsarin dimokiraɗiyyar Nijeriya.
Ta ƙara da cewa kasancewar jam’iyyu da yawa kawai ba ya nufin akwai dimokiraɗiyya mai ƙarfi idan jam’iyyun adawa ba su da damar gudanar da ayyukan su cikin ‘yanci.
“Batun ba wai ko Nijeriya na da jam’iyyu da yawa a ƙa’ida ba ne, amma ko waɗannan jam’iyyu na iya aiki ba tare da tsoma bakin da bai dace ba a aikace,” inji sanarwar.
ADC ta kuma ƙi amincewa da kwatancen da INEC ta yi da wasu rikice-rikicen zaɓe a jihohi kamar Zamfara, tana mai cewa waɗannan shari’o’in sun shafi karya dokokin zaɓe kai-tsaye, saɓanin halin da ake ciki yanzu.
Jam’iyyar ta soki gargaɗin INEC cewa ci gaba da babban taro yana iya haifar da soke sakamako daga baya a kotu, tana mai cewa wannan zato ne kawai da ba ya da tushe a doka.
Ta jaddada cewa hukumomin gudanarwa ba su da ikon taƙaita haƙƙin da kundin tsarin mulki ya bayar bisa zato kawai.
“Doka ba ta ba hukumomin sa ido damar hana halastattun ayyukan siyasa bisa hasashe ba,” inji sanarwar.
Wannan rikici na ƙara dagula dangantaka tsakanin ADC da INEC, musamman a daidai lokacin da jam’iyyar ke fama da rikicin shugabanci a ciki da kuma shirye-shiryen zaɓe masu zuwa.
ADC ta sake jaddada cewa ci gaba da tsarin dimokiraɗiyya a cikin jam’iyya yana da kariya a doka, sai dai idan kotu mai iko ta haramta hakan a fili.
“Babu irin wannan umarni a fili,” inji jam’iyyar.
Jam’iyyar ta buƙaci INEC da ta tsaya kan iyakokin aikin ta na kundin tsarin mulki, ta guji duk wani abu da za a iya fassara a matsayin tsoma baki cikin harkokin jam’iyya.
Ta kuma yi gargaɗin cewa faɗaɗa ikon sa ido fiye da abin da doka ta tanada na iya zama haɗari ga dimokiraɗiyyar Nijeriya.







