Rundunar Kwankwasiyya ta umurci membobin ta da su shiga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Asabar, mai magana da yawun ƙungiyar, Dakta Habibu Sale Mohammed, ya bayyana cewa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, jagoran Kwankwasiyya na ƙasa, ya kammala dukkan shirye-shiryen shiga haɗakar da ke neman kifar da Shugaba Bola Tinubu.
Ya ce: “Kungiyar Kwankwasiyya na sanar da dukkan membobin ta a faɗin Nijeriya da kuma al’umma baki ɗaya cewa Jagoran mu na ƙoli, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya kammala dukkan matakan da suka dace domin shiga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).
“Dangane da wannan mataki, zai yi rajista a hukumance da jam’iyyar a ranar Litinin, 30 ga Maris, 2026, a gidan sa, Gidan Kwankwasiyya, Miller Road, Kano, da ƙarfe 12 na rana.”







