• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya haramta wa manyan masu taurin bashi ci gaba da cin moriyar mu’amala da bankuna

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
March 28, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Kamfanonin ‘yan canji 82 kaɗai CBN ya ba lasin canjin kuɗin ƙasashen waje
Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, tare da bankin

Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, tare da bankin

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya fitar da kakkausar sanarwar taƙaita ayyukan banki ga “masu taurin bashin dindindin” da kuma manyan masu karɓar bashi da bashin su ya daɗe ba su fara biya ba.

A wani mataki mai faɗi da nufin ƙarfafa ladabtar da masu taurin bashi da kuma kare tsarin kuɗin ƙasa, CBN ya fitar da wannan sanarwar manufofi a ranar Laraba, bayan jawabin Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, a taron koli na shugabanni karo na huɗu na IMF/AFRITAC West 2 da aka gudanar a Abuja.

Gwamnan ya bayyana a fili cewa zamanin sassauci daga masu kula da harkokin banki ga masu ƙin biyan bashi ya ƙare.

Ya jaddada cewa yanzu CBN yana komawa ga tsauraran matakai wajen tabbatar da kyakkyawan tsarin gudanar bankuna da kamfanoni, domin kare sabon jarin da ya kai Naira tiriliyan 4.61 da aka samu a fannin shirin ƙarfafa yawan jarin bankuna daga duk wata barazana ko amfani da shi ba daidai ba.

“Ra’ayinmu kan tsarin gudanar da bankuna a bayyane yake: babu sassauci ga duk wani laifin da ya kauce daga bin tsarin da aka gindaya. Ta hanyar kawo ƙarshen sassaucin da aka dade ana yi, mun ƙarfafa ɗaukar alhaki, mun tsaurara sa-ido, kuma mun ɗaga matakan bin doka a duk fannin,” inji gwamnan.

Sabuwar dokar ta fi shafar “manyan masu karɓar bashi”, wato mutane ko kamfanoni da ke da manyan basussuka da aka riga aka ayyana a matsayin marasa aiki a tsarin kula da haɗarin bashi (Credit Risk Management System). A ƙarƙashin sabbin ƙa’idojin, za a hana waɗannan masu taurin bashi samun sabbin rance, da kuma wasu muhimman ayyukan banki kamar takardun ciniki da garanti.

“Mun aiwatar da taƙaita ayyukan banki ga manyan masu bashi da bashin su ya zama alaƙaƙai. Wannan mataki mai ƙarfi yana nuna ƙudirin mu na tabbatar da ladabtar da bashi, gaskiya a harkokin kuɗi, da ɗaukar alhaki,” inji sanarwar.

A cewar CBN, an ɗauki wannan mataki ne domin gina “al’adar biyan bashi” wadda a baya ba ta da ƙarfi musamman a tsakanin manyan masu karbar bashi. Ta hanyar hana su amfani da kayan aiki kamar wasikun lamuni (letters of credit) da takardun garanti (performance bonds), ana son hana abin da ake kira “tsalle daga banki zuwa banki” domin ƙara karɓar bashi.

“Ta hanyar taƙaita ayyukan banki ga masu kin biyan bashi na dindindin, muna ƙarfafa tsarin biyan bashi, muna kare masu ajiya, kuma muna tabbatar da daidaiton tsarin kuɗi,” inji CBN.

Baya ga wannan matakin, Cardoso ya sake jaddada cewa CBN na ci gaba da bin tsarin manufofin kuɗi na game-gari.

Wannan tsari yana maida hankali kan daidaita farashi da kuma amfani da game-garin hanyoyi domin rage hauhawar farashi, tare da kauce wa hanyoyin da ba na yau da kullum ba domin dawo da amincewa da Naira.

“CBN na tsayawa daram kan tsarin manufofin kuɗi na gargajiya, tare da maida hankali kan dawo da daidaiton farashi, ƙarfafa sahihancin manufofi, da daidaita hasashen tattalin arziki ta hanyar tsari da daidaito,” inji sanarwar.

Shekaru da dama, fannin bankin Nijeriya na fama da matsalar “masu kin biyan bashi na dindindin”, wato attajirai ko manyan kamfanoni da ke karɓar biliyoyin naira amma su kasa biya.

Ana kiran irin waɗannan masu bashi da suna “manyan masu taurin bashi”. Idan irin waɗannan basussuka suka lalace, suna barazana ga ƙarfafa bankuna da kuma tsaron ajiyar kuɗin talakawa.

A ƙarƙashin jagorancin Cardoso, CBN na komawa ga tsarin “manufofin kuɗi na yau da kullum”. Wannan yana nufin barin tsohon tsarin bayar da rance kai tsaye ga fannoni kamar noma, tare da maida hankali kan babban aikin sa, wato tabbatar da daidaiton farashi da kuma kula da tsarin banki.

Tags: bankunaCBNOlayemiCardoso
Previous Post

Allah ya kyauta a ce wai Peter Obi ya zama Shugaban Nijeriya, inji Fani-Kayode

Next Post

Kwankwaso ya yi murabus daga NNPP

Related Posts

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’

November 25, 2026
Muna samun nasarori a tsaro, ilimi da ababen more rayuwa – Tinubu 
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya ware Naira biliyan 450 domin tallafa wa manoma 500,000

November 22, 2026
Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40

November 19, 2026
CBN ya naɗa kamfanoni takwas domin kula da fitar da ɗanyen mai da iskar gas
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN da NNPCL sun ƙulla yarjejeniyar ƙarfafa tattalin arziki da samar da kuɗaɗen zuba jari a ɓangaren makamashi

November 18, 2026
CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su

November 17, 2026
Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS

November 16, 2026
Next Post
Amfani da ‘yan sa-kai a harkar tsaro yana ƙara yawaitar yaɗuwar ƙananan makamai a Nijeriya, cewar Kwankwaso

Kwankwaso ya yi murabus daga NNPP

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!