• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu a London: Yadda Gwamnan CBN ya bayyana inganci, ƙarfi da juriyar sauye-sauyen manufofin kuɗi a Nijeriya, a taron masu zuba jari a Afrika

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
March 21, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Tinubu a London: Yadda Gwamnan CBN ya bayyana inganci, ƙarfi da juriyar sauye-sauyen manufofin kuɗi a Nijeriya, a taron masu zuba jari a Afrika
Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, yana jawabi a taron masu zuba jari a Afrika (Africa Capital Forum) da aka gudanar a birnin London a ranar Talata

Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, yana jawabi a taron masu zuba jari a Afrika (Africa Capital Forum) da aka gudanar a birnin London a ranar Talata

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, ya jaddada cewa sauye-sauyen manufofin kuɗi a Nijeriya sun ƙarfafa juriya ga girgizar tattalin arziki, sun kuma dawo da amincewar masu zuba jari a cikin Nijeriya, tun bayan hawa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Cardoso ya ce sabbin sauye-sauyen manufofin kuɗi da na fannin banki da aka aiwatar a Nijeriya sun ƙarfafa ikon ƙasar na jure wa girgizar tattalin arziki daga waje tare da dawo da amincewa a tattalin arzikin ƙasar.

Da yake jawabi a taron masu zuba jari a Afrika (Africa Capital Forum) da aka gudanar a birnin Landan a ranar Talata, a gefen ziyarar aiki ta Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zuwa ƙasar Birtaniya, Cardoso ya shaida wa masu zuba jari da abokan hulɗar raya ƙasa cewa Babban Bankin ya “gina tsari mai ɗorewa na jure girgiza” ta hanyar tsauraran manufofi da gyare-gyaren hukumomi.

A cewar sa, kasuwar canjin kuɗaɗen waje ta Nijeriya yanzu tana da ƙarin gaskiya da wadataccen ruwa, inda sabon tsarin musayar kuɗaɗen waje ya kawar da yawancin tsofaffin takunkuman sarrafa kuɗaɗen waje tare da sauƙaƙa harkokin kasuwanci da zuba jari.

Cardoso ya ci gaba da bayyana cewa an samu gagarumin ci gaba a shirin ƙara ƙarfin jarin bankuna , inda sama da bankuna 30 suka riga suka cika sabbin ƙa’idojin jarin, yayin da ake ci gaba da tantance sauran. Ya ce, “kimanin kashi 28 cikin 100 na jarin da aka samu a wannan shiri ya fito ne daga ƙasashen waje,” ya ƙara da cewa hakan alama ce ta sabuwar amincewa da daidaiton tsarin kuɗi na Nijeriya.

Ya kuma bayyana cewa kuɗaɗen da ‘yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje ke aikowa gida sun ƙaru sosai, lamarin da ya taimaka wajen faɗaɗa hanyoyin samun kuɗaɗen waje, tare da ƙarfafa ajiyar kuɗin ƙasar domin jure sauye-sauyen tattalin arzikin duniya.

Ya ce, “abin da muka sa a gaba shi ne kare wannan daidaito da muka samu da wahala domin masu zuba jari da masu ruwa da tsaki su samu damar tsara harkokin su cikin kwanciyar hankali.”

Ya ƙara da cewa a ƙarƙashin jagorancin sa, CBN zai ci gaba da kasancewa, mai buɗe ido da gaskiya, yana bayar da bayanai akai-akai, tare da ɗaga matakin tsammanin jama’a domin kauce wa kurakuran da suka gabata.

Cardoso ya tabbatar da cewa hauhawar farashin kayayyaki ya ragu sosai, kwanciyar hankali a farashin canjin kuɗi ya inganta, kuma sauye-sauyen da aka yi sun sanya tattalin arzikin Nijeriya “a hanya mai kyau ta samun babban ci gaba wanda zuba jari na cikin gida, gyare-gyaren fannin mai, da kuma sabuwar amincewa daga duniya za su jagoranta.”

Ya ce, “Za mu ci gaba da tabbatar da daidaito, ba kawai wajen rage hauhawar farashi ba, har ma a kasuwar canjin kuɗi, tare da ƙarin gaskiya da rahotanni masu ɗorewa.”

Tags: CardosoCBN
Previous Post

Mu APGA ba za mu tsaida ɗan takarar shugaban ƙasa a 2027 ba, Tinubu za mu yi — Soludo

Next Post

Yarjejeniya kan hijira da Birtaniya: A daina yaɗa labaran ƙarya, inji gwamnatin Nijeriya

Related Posts

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gangamin CBN a Kano: A daina wulaƙanta takardun naira, a riƙe su cikin inganci da nagarta – CBN

September 29, 2026
Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Next Post
Yarjejeniya kan hijira da Birtaniya: A daina yaɗa labaran ƙarya, inji gwamnatin Nijeriya

Yarjejeniya kan hijira da Birtaniya: A daina yaɗa labaran ƙarya, inji gwamnatin Nijeriya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!