Kamfanin MTN Group ya biya Sarkin Kano, Dakta Muhammadu Sanusi II, jimillar kuɗin ladar matsayin darakta na Rand ɗin Afrika ta Kudu miliyan 5.4 a shekarar kuɗi da ta ƙare a ranar 31 ga Disamba, 2025.
Kuɗin sun kama kimanin Naira miliyan 442 ko dalar Amurka 324,000.
Rahoton ShoreAfrica ya bayyana cewa an biya wannan kuɗin ne a daidai lokacin da MTN, wanda shi ne kamfanin sadarwa mafi girma a Afrika, ya ba da rahoton farfaɗowa mai ƙarfi ta fuskar kuɗi, wanda ya samo asali ne daga ingantuwar aiki a Nijeriya da Ghana, inda raguwar matsin lambar canjin kuɗi da rage kashe kuɗi suka taimaka wajen daidaita ribar kamfanin.
Kuɗin zama, halartar tarurruka da gudanar da ayyuka sun ƙara masa albashi
Sanusi, wanda ya taɓa zama gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) daga 2009 zuwa 2014, ya kasance darakta mai zaman kan sa wanda ba ya gudanar da ayyukan yau da kullum a MTN tun daga watan Yulin 2019.
Albashin sa na 2025 ya ƙaru daga Rand miliyan 5.07, wato kusan Naira miliyan 412.1 (kimanin dalar Amurka 304,000), daga shekarar da ta gabata.
A zaman sa a CBN, ya kawo manyan sauye-sauye a harkar banki, amma kuma ya shiga rikici mai ɗaukar hankali da Gwamnatin Tarayya kan ɓacewar kuɗaɗen mai, wani lamari da ya yaɗa sunan sa a matsayin mutum mai tsage gaskiya komai ɗacin ta.
Rabon ribar shekarar 2025 da MTN ya yi ya nuna cewa Sanusi ya samu Rand miliyan 1.82 (Naira miliyan 148 kenan) a matsayin kuɗin zama (retainer), da kuma Rand miliyan 1.37 (Naira miliyan 112) saboda halartar tarurrukan kwamitin gudanarwa.
Sauran kuɗaɗen sun haɗa da:
- Rand 829,000 (Naira miliyan 67.4 kenan) don ayyuka na musamman na kwamitin,
- Rand 631,000 (Naira miliyan 51.3 kenan) don zaman tsara dabaru, da kuma
- Rand 785,000 (Naira miliyan 63.8) don ayyukan gaggawa.
Wannan ya nuna irin yawan lokacin da ake buƙata daga daraktoci masu zaman kan su a manyan kamfanonin ƙasa da ƙasa.
Sarki mai tasiri yana jagorantar harkokin kasuwanci
A MTN, Sarki Sanusi a matsayin darakta mai zaman kan sa yana cikin kwamitin kula da haɗari da bin doka, kwamitin kuɗi da zuba jari, da kuma kwamitin zamantakewa, ɗabi’a da ɗorewa.
Ban da jarin da yake da shi a MTN kuma, shi ne shugaban kamfanin Black Rhino Management Services Limited, har ila yau kuma darakta ne a wasu kamfanonin daban-daban.
Sanusi, wanda aka fi sani da Muhammadu Sanusi II, yana daga cikin sarakunan gargajiya mafi tasiri a Nijeriya.
Shi ne jagoran ɗariƙar Tijjaniyya a Nijeriya.
Ya fara hawa karagar mulki a 2014, aka tuɓe shi a 2020 sakamakon saɓanin da ya samu da gwamnatin Jihar Kano, sannan aka mayar da shi kan karagar sa a ranar 23 ga Mayu, 2024—lamarin da ya ja hankalin jama’a sosai.
Kafin ya zama sarki, Sanusi ya yi suna a matsayin masanin tattalin arziki, jami’in banki kuma masani a harkokin jama’a.
Yana da digirin farko a fannin tattalin arziki da shari’ar Musulunci, sannan yana da digirin digirgir a shari’ar Musulunci, wanda hakan ya ƙarfafa tsayuwar sa wajen kira ga ladabtar da harkokin kuɗi, tsare gaskiya da gyaran al’umma.







