• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Ƙungiyar Tarayyar Afrika ta yi Allah-wadai da harin ta’addanci a Borno

Wakilin Mu by Wakilin Mu
March 18, 2026
in Labarai
A A
0
Ƙungiyar Tarayyar Afrika ta yi Allah-wadai da harin ta’addanci a Borno
Wurin da aka aikata ta'addanci a Borno

Wurin da aka aikata ta'addanci a Borno

Shugaban Hukumar Tarayyar Afrika (AU), Mahmoud Youssouf, ya yi kakkausar suka kan hare-haren ƙunar baƙin wake da suka auku a Maiduguri, Jihar Borno, a ranar 16 ga Maris, 2026, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu.

A cikin wata sanarwa ga manema labarai, ƙungiyar ta bayyana cewa tana “cikin cikakken goyon baya” ga gwamnati da al’ummar Nijeriya a wannan lokaci mai wahala, tare da miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukan su, tare da yi wa waɗanda suka jikkata fatan samun sauƙin warkewa cikin gaggawa.

Ta ƙara da cewa: “Shugaban Hukumar ya sake jaddada ƙin amincewa da kuma Allah-wadai da Tarayyar Afrika ke yi ga duk wani nau’i na tashin hankali da ƙungiyoyin ta’addanci da masu tsattsauran ra’ayi ke aikatawa kan fararen hula da jami’an tsaro. Irin waɗannan ayyuka suna take haƙƙin ɗan’adam kuma suna tauye zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali a cikin al’umma.

“Shugaban Hukumar ya yaba wa Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da kuma hukumomin Jihar Borno bisa ci gaba da ƙoƙarin su na bai-ɗaya wajen yaƙar ta’addanci da inganta tsaro a Maiduguri da kewaye a cikin shekarun baya-bayan nan.

“Wannan mummunan lamari ya sake nuna barazanar da ta’addanci ke ci gaba da haifarwa da kuma buƙatar ƙara yin taka-tsantsan da juriya.”

Shugaban ya kuma yi kira ga ƙasashen duniya da su ƙara ƙaimi wajen tallafa wa Nijeriya da yankin Tafkin Chadi baki ɗaya, ciki har da ƙara agajin jinƙai, gina ƙwarewa, musayar bayanan sirri, da kuma ci gaba da zuba jari a shirye-shiryen tabbatar da zaman lafiya da cigaba domin magance tushen matsalolin tsattsauran ra’ayi.

Ƙungiyar ta sake jaddada cewa sai ta hanyar haɗin kan al’umma gaba ɗaya, tsaro na bai-ɗaya da matakan aiki tare, ƙarfafa haɗin gwiwa, da jajircewa mai ɗorewa ne za a iya murƙushe barazanar ta’addanci yadda ya kamata tare da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa, bisa tsarin dokoki da manufofin Tarayyar Afrika kan rigakafin rikice-rikice, yaƙar ta’addanci da gina zaman lafiya.

“Shugaban Hukumar ya sake tabbatar da cikakken goyon baya da haɗin kan Tarayyar Afrika ga Gwamnati da al’ummar Nijeriya wajen inganta zaman lafiya mai ɗorewa da kwanciyar hankali,” inji sanarwar.

Previous Post

Kamfanin MTN ya biya Sarkin Kano Lamiɗo Sanusi naira miliyan 442 ladar matsayin darakta

Next Post

Sarkin Musulmi ya ayyana Juma’a a matsayin ranar Sallah saboda rashin ganin watan Shawwal a ranar Laraba

Related Posts

Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya
Labarai

Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya

September 29, 2026
Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
Next Post
Kotunan Nijeriya sun zama cibiyoyin hada-hadar shari’u – Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi ya ayyana Juma’a a matsayin ranar Sallah saboda rashin ganin watan Shawwal a ranar Laraba

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!