• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Yadda na ji da aka tuɓe ni daga sarautar Kano – Sarki Sanusi

ALI KANO by ALI KANO
March 16, 2026
in Labarai
A A
0
Yadda na ji da aka tuɓe ni daga sarautar Kano – Sarki Sanusi
Mai Martaba Sarkin Kano, Dakta Muhammadu Sanusi II (Hoto: Majeeda Studios)

Mai Martaba Sarkin Kano, Dakta Muhammadu Sanusi II (Hoto: Majeeda Studios)

Mai Martaba Sarkin Kano, Dakta Muhammadu Sanusi II, ya bayyana yadda zurfin imanin sa da Allah ya taimaka masa ya kwantar da hankalin sa bayan rasa manyan muƙamai biyu — na farko a matsayin Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) a shekarar 2014, sannan daga baya a matsayin Sarki a shekarar 2020.

Sarkin yana magana a wajen Laccar Azumin Ramadan ta shekara-shekara da Fola Adeola ke shiryawa, inda ya ce: “Sau da yawa a rayuwar mu muna danganta abubuwa ga mutane, alhali duk halittu ne kawai… Tuna cewa yanayi ba na dindindin ba ne, kuma Allah ne ke sauya halin da kake ciki, yana taimaka maka ka jure kuma ka tafiyar da kan ka yadda ya kamata.”

Sanusi ya ba da labarin tafiyar sa da cewa: “An dakatar da ni daga muƙamin gwamnan babban banki. Bayan wata uku, sai na zama Sarki… Shekaru da dama da suka wuce an tuɓe ni daga sarauta; bayan shekaru huɗu, na dawo. Yanzu ina cikin wannan fada, ina kan karagar mulki na.”

Ya ƙara da cewa zaman sa a wajen Kano na wani lokaci ya ba shi damar kauce wa wulaƙanci tare da neman digirin digirgir: “Allah Ya kasance Mai yawan rahama, Mai yawan alheri. Ya cire ni daga wannan hali. Ya ba ni dama, na je na yi digirin digirgir, kuma na dawo.”

Sarki Sanusi ya buƙaci mutane da su kasance masu juriya da riƙo da aƙida, inda ya ce: “Idan an cire ni daga muƙamai, ba wani babban abu ba ne. A ƙarshe dai, abin da nake tambayar kai na shi ne, shin na yi wani abu da zai ɓata wa Allah rai ne?

“Gara ka bar wurin nan ka tsaya a kan aƙidojin ka fiye da ka zauna a can kana jawo wa kan ka fushin Allah.”

Sanusi ya riƙe muƙamin Gwamnan CBN daga 2009 zuwa 2014.

A cikin 2020 Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya tsige shi daga sarautar Kano, sai kuma gwamna mai ci yanzu, Abba Kabir Yusuf, ya dawo da shi kan karagar a cikin 2024.

Shi dai Fola Adeola, wanda cikakken sunan sa Alhaji Tajudeen Afolabi Adeola, yana daga cikin waɗanda suka assasa bankin Guaranty Trust (wato GTBank Plc) shi ne ciyaman na FATE Foundation.

Tags: aƙidaCBNFolaAdeolaImaniKanolaccaRamadanSanusisarautasarkiSarkin
Previous Post

Garambawul da Tinubu yake yi yana ƙarfafa amincewar ƙasashen duniya ga Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

Next Post

Tinubu zai bar Abuja ranar Talata domin ziyarar tarihi ta ƙasa zuwa Birtaniya

Related Posts

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura
Labarai

Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura

November 25, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa
Labarai

Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa

November 24, 2026
Next Post
Tinubu ya taya APC murnar nasara a zaɓuɓɓukan Birnin Tarayya, Kano da Ribas

Tinubu zai bar Abuja ranar Talata domin ziyarar tarihi ta ƙasa zuwa Birtaniya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!