Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan sabon Umurnin Zartarwa da ya shafi yadda kuɗaɗen man fetur da iskar gas za su rika shiga asusun gwamnati kai-tsaye.

Manufar wannan doka ita ce:
👉 rage satar kuɗi,
👉 tabbatar da gaskiya,
👉 tabbatar da cewa kowane mataki na gwamnati ya samu haƙƙin sa.
Ga abubuwa 10 da kowa ya kamata ya fahimta:
1. Shigar Kuɗi Kai-tsaye Zuwa Asusun Gwamnati:
Daga yanzu, kuɗin man fetur da gas ba za su riƙa bi ta asusu daban-daban ba. Za su shiga Asusun Tarayya kai-tsaye, don kada kuɗi su ɓace a hanya, ko a yi habzi da wani kaso.
2. Jihohi da Ƙananan Hukumomi Za Su Fi Amfana:
Za a koma tsarin da Kundin Tsarin Mulki ya tanada, inda gwamnatocin Tarayya, Jihohi da Ƙananan Hukumomi za su riƙa samun rabon kuɗin da ya dace da su.
3. An Rage Kuɗin da NNPCL ke Riƙewa na Gudanarwa:
Kamfanin NNPCL ba zai ƙara ɗaukar kashi 30% ba. Zai riƙe kashi 20% ne a matsayin kuɗin gudanarwa daga ribar gas da fetur, sauran kuɗin su tafi asusun tarayya domin raba shi ga matakan gwamnati uku (wato Tarayya, Jiha da Ƙaramar Hukuma).
4. An Soke Asusun Binciken “Frontier”:
Kuɗin da ake warewa don binciken mai a wasu yankuna an dakatar da su. Yanzu duk kuɗin za su shiga Asusun Tarayya a raba su.
5. NNPCL Ya Zama Kamfanin Kasuwanci:
Kamfanin NNPCL ba zai ƙara amfani da matsayin sa ta rinjayi farashi ko kashe kuɗi yadda yake so ba. Zai yi aiki kamar sauran kamfanoni na kasuwanci.
6. Kuɗin Tara na Ƙona Gas (Flaring) Zai je Asusun Tarayya Kai tsaye:
Kuɗin tara da ake karɓa idan aka ƙona gas a banza, yanzu za su shiga Asusun Tarayya ne kai-tsaye.
7. ‘Yan Kwangila Za Su Biya Haraji Kai-tsaye (Daga 13 Fabrairu, 2026) Zuwa ga Asusun Tarayya:
Duk wanda ke aiki a ɓangaren mai da gas zai riƙa biyan harajin sa kai-tsaye zuwa asusun gwamnati.
8. Kafa Ƙungiya Ta Musamman Don Kula da Ayyukan Mai:
An kafa ƙungiya da za ta sa ido kan ayyukan man fetur, domin rage rikice-rikice da saurin warware matsaloli.
9. An Gyara Rikice-Rikicen da ke Cikin Dokoki:
An daidaita dokokin PIA da tsarin NNPCL don a samu sauƙin aiki da fahimta.
10. An Daƙile Ɓarnar Kuɗi:
Ba za a ƙara kashe kuɗi a ayyukan da ba su da amfani ko tasiri ba.
A TAƘAICE:
Wannan sabon umurni yana nufin:
✔ kuɗin ƙasa su riƙa zuwa inda ya dace,
✔ Jihohi da Ƙananan Hukumomi su fi samun kuɗi,
✔ za a rage satar kuɗi da almubazzaranci,
✔ za a ƙarfafa tattalin arzikin Nijeriya.
Idan aka aiwatar da wannan tsarin yadda ya kamata, sauyi ne da kowa zai amfana.
Menene ra’ayin ku? Kuna ganin wannan mataki zai inganta tattalin arzikin ƙasa?
Ku yi mana sharhi a ƙasa.






