• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Gobarar Kasuwar Singa: Tinubu ya tura tawaga ƙarƙashin Shettima domin yin jaje

* Ƙungiyar gwamnonin Arewa ta bayyana alhini

ALI KANO by ALI KANO
February 15, 2026
in Labarai
A A
0
Gobarar Kasuwar Singa: Tinubu ya tura tawaga ƙarƙashin Shettima domin yin jaje
Kashim Shettima yana hawan jirgi

Kashim Shettima yana hawan jirgi

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umurci mataimakin sa, wato Kashim Shettima, da ya jagoranci wata babbar tawagar Gwamnatin Tarayya zuwa Kano domin jajanta wa ‘yan Kasuwar Singa da gobara ta shafa tare da isar da ta’aziyya da goyon bayan gwamnati.

Sabuwar mummunar gobarar da ta tashi a jiya a kasuwar wadda tana ɗaya daga cikin manyan kasuwannin abinci a Najeriya, ta lalata kayayyaki da darajar su ta kai biliyoyin naira.

Gobarar, wadda ta tashi da yammacin Asabar, ta ci gaba har zuwa safiyar yau Lahadi.

Tinubu ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici kuma mai tayar da hankali, yana mai cewa ya damu matuƙa da yadda irin wannan masifa ke maimaituwa cikin ɗan ƙanƙanin lokaci.

A cikin wata sanarwa da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya rattaba wa hannu, Shugaban ya miƙa saƙon ta’aziyya ga ‘yan kasuwa da masu sana’o’in da suka yi asara sakamakon gobarar.

A matsayin wani ɓangare na matakan gaggawa daga Gwamnatin Tarayya, Shettima zai jagoranci tawagar da za ta tashi daga Abuja zuwa Kano domin isar da saƙon jaje daga Shugaba Tinubu da kuma sanar da matakan tallafin Gwamnatin Tarayya.

Tawagar ta ƙunshi:

  • Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas
  • Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin
  • Sanata Kawu Sumaila
  • Shugaban Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA)
  • Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Wakilai, Abubakar Kabir Bichi
  • Ministan Harkokin Jinƙai, Bernard M. Doro
  • Darakta-Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), Zubaida Umar

A yayin ziyarar, ana sa ran tawagar za ta yi alƙawarin tallafin kuɗi a madadin Gwamnatin Tarayya domin taimaka wa ‘yan kasuwa su farfaɗo da harkokin su.

Haka kuma za su tattauna da Gwamnatin Jihar Kano don hanzarta buɗe kasuwar da dawo da harkokin tattalin arziki.

Tinubu ya kuma umurci a gudanar da cikakken bincike kan musabbabin gobarar, kusa da na nesa, domin hana sake faruwar irin haka a nan gaba.

Ita ma Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) ta bayyana alhinin ta ga waɗanda gobarar Kasuwar Singa ta shafa, tana mai kiran lamarin abin takaici da tayar da hankali.

A cikin wata sanarwa da Shugaban ta kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta nuna cewa gobarar ta faru ne ‘yan makonni kaɗan bayan wata makamanciyar haka, lamarin da ya ƙara jefa ‘yan kasuwa cikin damuwa da ƙunci na tattalin arziki.

Gwamnan ya ce yawaitar gobarar kasuwanni a Arewa na ci gaba da lalata hanyoyin samun abinci da kuɗin shiga, tare da kawo cikas ga harkokin tattalin arziki da jefa iyalai cikin mawuyacin hali.

Ya jaddada buƙatar ɗaukar matakan kariya na zamani da suka haɗa da fasaha daga hukumomin tarayya da na jihohi.

Ƙungiyar ta ba da shawarar girka na’urorin gano gobara da kashe ta na zamani a manyan kasuwanni, inganta tsare-tsaren gine-gine, tsaurara bin dokokin tsaro, da kuma ci gaba da wayar da kan jama’a, musamman ‘yan kasuwa da masu gudanar da kasuwanni.

Haka kuma ta yaba da saurin kai ɗauki da Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, jami’an tsaro, NEMA da sauran masu bayar da agajin gaggawa suka yi, wanda ya taimaka wajen taƙaita yaɗuwar gobarar da hana ƙarin asara.

Tags: gobaraGwamnoninArewajajeKanoKashimShettimaKasuwarSingaMuhammadInuwaYahayaNSGFShugabaBolaTinubu
Previous Post

Tinubu ya yi wa ‘yan kasuwar Kano jaje kan gobarar Singa, ya ba da umurnin bincike

Next Post

Dalilin mu na sanya ranakun Zaɓen 2027 a watan Ramadan, amma mun lura da damuwar jama’a – INEC

Related Posts

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura
Labarai

Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura

November 25, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa
Labarai

Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa

November 24, 2026
Next Post
Dalilin mu na sanya ranakun Zaɓen 2027 a watan Ramadan, amma mun lura da damuwar jama’a – INEC

Dalilin mu na sanya ranakun Zaɓen 2027 a watan Ramadan, amma mun lura da damuwar jama'a – INEC

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!