• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Sojoji sun yi galaba kan ’yan ta’adda tare da ƙwato dabbobi 529 a Katsina

Wakilin Mu by Wakilin Mu
February 8, 2026
in Tsaro
A A
0
Sojoji sun yi galaba kan ’yan ta’adda tare da ƙwato dabbobi 529 a Katsina
Wani soja tare da shanun da aka ƙwato

Wani soja tare da shanun da aka ƙwato

Dakarun sojojin Nijeriya da ke ƙarƙashin Birged ta 17 da ke Katsina sun samu nasarar ƙwato dabbobi 529 da ’yan ta’adda suka sace, bayan gumurzu da aka yi da su a Ƙafur, Jihar Katsina.

Rundunar ta ce samamen ya samo asali ne daga sahihan bayanan sirri da suka nuna motsin ’yan ta’adda a yankin Kasuwar Sabo.

A cewar Muƙaddashin Daraktan Hulɗa da Jama’a na rundunar, Kyaftin Abayomi Adisa, dakarun FOB Malumfashi ƙarƙashin jagorancin Kwamandan sansanin, Laftanar Kanar M.M. Isa, sun kai samamen a ranar 7 ga Fabrairu, 2026, kan wasu ’yan ta’adda da ake zargin sun shigo yankin daga Jihar Zamfara.

Rahotanni sun nuna cewa an danganta jagorancin gungun ‘yan ta’addan da Idi A-ba-su Aiki, wanda ake zargin ɗan’uwan fitaccen jagoran ’yan bindiga Ado Aliero ne.

Da sojojin suka iso, ’yan ta’addan sun buɗe wuta, amma dakarun sun mayar da martani da ƙarfi, lamarin da ya tilasta wa maharan tserewa zuwa dazuzzuka tare da barin wasu daga cikin dabbobin da suka sace.

Sojojin sun ci gaba da bin su tsakanin Burdugau da Unguwar Matau a Malumfashi, inda ’yan ta’addan suka ƙara watsar da sauran dabbobin.

Jimilla, an ƙwato shanu 290, tumaki 238, jaki 1, da kuma babur 1, duk da cewa shanu 14 sun mutu yayin musayar wuta bayan da ’yan ta’addan suka yi amfani da su a matsayin garkuwa.

Rundunar ta ce babu wani soja da ya jikkata.

Dandazon shanun da aka ƙwato daga hannun ‘yan ta’addan

An miƙa dabbobin ga hukumomin da abin ya shafa domin tantancewa da mayar da su ga masu su.

Kwamandan Dibijin na 8, Manjo-Janar Paul Koughna, ya yabi jarumtaka da ƙwarewar dakarun, kuma ya tabbatar da ci gaba da tsaurara farmaki domin tabbatar da tsaro a yankin.

Tags: KatsinaPaulKoughnashanusojojita'addanci
Previous Post

IPOB ta soke umurnin zama a gida na duk Litinin a Kudu-maso-Gabas

Next Post

Tarayyar Turai ta bi sahun Hukumar FATF, ta cire Nijeriya daga jerin ƙasashen da ke da haɗarin safarar kuɗi

Related Posts

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
EFCC ta samu nasarar hukunta mutumin da ya yi ƙoƙarin sumogar zinari mai darajar Naira biliyan 4.4 a Kano
Tsaro

EFCC ta samu nasarar hukunta mutumin da ya yi ƙoƙarin sumogar zinari mai darajar Naira biliyan 4.4 a Kano

November 17, 2026
Sojoji sun halaka ’yan ta’adda, sun ceto mutum 16, sun ƙwato babura 38 a Neja da Kebbi
Tsaro

Sojoji sun halaka ’yan ta’adda, sun ceto mutum 16, sun ƙwato babura 38 a Neja da Kebbi

November 6, 2026
Ƙungiyar Amnesty ta buƙaci bincike kan bidiyon atisayen muzaharar Izala
Tsaro

’Yan sanda sun kama matashin Izala kan bidiyon da ke tunzura rikicin addini

October 27, 2026
Ƙungiyar Amnesty ta yi tir da kisan malamin addini Sheikh Yahaya Masussuka
Tsaro

’Yan sanda a Katsina sun tabbatar da kashe Sheikh Yahaya Masussuka da abokin sa

October 26, 2026
Ƙungiyar Amnesty ta yi tir da kisan malamin addini Sheikh Yahaya Masussuka
Tsaro

Ƙungiyar Amnesty ta yi tir da kisan malamin addini Sheikh Yahaya Masussuka

October 26, 2026
Next Post
Tarayyar Turai ta bi sahun Hukumar FATF, ta cire Nijeriya daga jerin ƙasashen da ke da haɗarin safarar kuɗi

Tarayyar Turai ta bi sahun Hukumar FATF, ta cire Nijeriya daga jerin ƙasashen da ke da haɗarin safarar kuɗi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!