Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da a fara ayyukan haƙo man fetur a Tsibirin Tongeji da ke Ƙaramar Hukumar Ipokia a Jihar Ogun.
Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun, shi ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin da yake karɓar Kwamandan Rundunar Sojan Ruwa ta Yankin Yamma (Flag Officer Commanding, Western Naval Command), Riya Admiral Abubakar Abdullahi Mustapha, tare da manyan jami’an rundunar, a wata ziyarar girmamawa da suka kai masa a ofishin sa da ke Oke-Mosan, Abekuta.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa Shugaban Ƙasar ya amince da a fara aiki nan take kan gina tashar jirgin ruwa ta Olokola Deep Seaport da ke Ƙaramar Hukumar Ogun Waterside, inda ya bayyana wannan mataki a matsayin babbar nasara bayan shekaru da dama ana jira game da aikin tashar jiragen ruwan da za a kashe biliyoyin daloli.
Abiodun ya ce duka ayyukan biyu na da muhimmanci matuƙa ga Shugaba Tinubu, inda ya lura da cewa tashar Olokola Deep Seaport za ta taimaka ƙwarai wajen rage cunkoso a tashoshin jiragen ruwa na Legas, yayin da haƙo man fetur a Tsibirin Tongeji zai ƙarfafa haɗin kai da bunƙasa tattalin arziki tare da ba da dama ga mazauna al’ummomin bakin teku.
Abiodun ya ce: “Bari in sanar da ku cewa Shugaban Ƙasa ya amince da a fara ayyukan haƙo man fetur na kasuwanci a Tsibirin Tongeji, kuma daga yanzu za ku fara ganin ayyuka da dama a can.
“Tashar jirgin ruwan Olokola da muke shirin ginawa, wadda ta daɗe tana kan tebur na tsare-tsare tsawon shekaru, yanzu ta dawo kan tebur.
“Ina so in miƙa godiya ta gaskiya ga Shugaban Ƙasa saboda wannan cikakkiyar manufar sa ce. A cikin makonni biyu da suka gabata kaɗai, mun gudanar da tarurruka da dama kan Olokola, kuma Shugaban Ƙasa ya bayyana ƙudirin sa na ganin an aiwatar da tashar jiragen ruwan.”
Gwamnan ya ƙara da cewa Shugaban Ƙasar ya ba da umurni kai-tsaye cewa aikin gina tashar jiragen ruwan ya yi nisa sosai tsakanin yanzu zuwa shekara mai zuwa, yana mai jaddada cewa aikin na da babbar damar rage cunkoso a tashoshin jiragen ruwa na Legas, musamman kasancewar titin bakin teku zai samar da wata sabuwar hanyar sufuri da jigilar kaya.
Ya kuma bayyana cewa sabuwar tashar jiragen ruwan za a san ta da suna Blue Marine Economic Zone, suna da ke nuna muhimmancin wurin ta na bakin teku da kuma babbar damar tattalin arzikin da take da ita.







