• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Thursday, May 14, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Zargin damfarar dala miliyan 13: Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan buƙatar EFCC na ƙwace kuɗi gaba ɗaya

ALI KANO by ALI KANO
January 20, 2026
in Labarai
A A
0
Zargin damfarar dala miliyan 13: Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan buƙatar EFCC na ƙwace kuɗi gaba ɗaya
Dakta Aisha Suleiman Achimugu

Dakta Aisha Suleiman Achimugu

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 25 ga Maris domin yanke hukunci kan wata buƙata da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta shigar, na neman umurni na ƙarshe na ƙwace dala miliyan 13, kuɗaɗen da ake alaƙantawa da kamfanin Oceangate Engineering Oil & Gas Ltd mallakin Dakta Aisha Achimugu.

Mai Shari’a Emeka Nwite ya saka ranar ne a yau, bayan da lauyan EFCC, Rotimi Oyedepo, SAN, da lauyan kamfanin, Darlington Ozurumba, suka amince da takardun su tare da gabatar da hujjoji na goyon baya da na ƙin amincewa da ƙarar a ranar Litinin.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa a ranar 22 ga Agusta, 2025, Mai Shari’a Nwite ya amince da buƙatar EFCC ta ex-parte ta a bayar da umurni na wucingadi na ƙwace dala miliyan 13 da ake alaƙantawa da Oceangate Ltd zuwa ga Gwamnatin Tarayya, bisa zargin cewa an samo kuɗin ne ta hanyar wasu ayyukan da ba su halatta ba.

Daga bisani alƙalin ya umurci hukumar da ta wallafa umurnin a wata babbar jarida, domin duk wanda ke da ja da ya nuna dalili cikin kwanaki 14 da ya sa ba za a ƙwace kuɗin gaba ɗaya zuwa Gwamnatin Tarayya ba.

Wani jami’in bincike na EFCC, Usman Aliyu, ya shaida cewa hukumar ta samu rahoton sirri mai inganci da ke zargin cewa wani kamfani mai suna Oceangate Engineering Limited, ba tare da bin ƙa’ida ba, ya yi amfani da kuɗaɗen da ake zargin na haramtacciyar hanya ne wajen sayen rijiyoyin mai daga Hukumar Kula da Harkar Man Fetur ta Ruwa da Ƙasa (NUPRC).

Aliyu ya ce binciken su ya nuna cewa Oceangate kamfani ne mai iyakantaccen alhaki da aka yi wa rajista a Hukumar Kula da Harkokin Kamfanoni (CAC) a ranar 25 ga Fabrairu, 2005 da lambar RC 617736.

Ya ce a shekarar 2024, Oceangate ya shiga gasar lasisin rijiyoyin mai na Deep Offshore PPL 302 da Shallow Water PPL 3007.

Ya ce bayan kammala tayin fasaha da na kasuwanci, NUPRC ta sanar da kamfanin cewa shi ne ya ci gasar, tare da bayyana sharuɗɗan da dole ne a cika su kafin a ba shi lasisi.

Aliyu ya ce an gano cewa jimillar kuɗaɗen da Oceangate Ltd ke bin gwamnati kafin bayar da Lasisi na Binciken Man Fetur (PPL) sun kai $37,223,144.00.

Ya ce kamfanin, ta asusun Bankin Zenith mai lamba 5074678281, ya riƙa tura miliyoyin daloli zuwa Gwamnatin Tarayya kashi-kashi, ciki har da $1.1m, $1.1m, $3.8m, $1.2m, $3.05m, $2.1m da $500,000.

Jami’in ya ce a ranakun 27 da 28 ga Maris, 2025, Bankin Providus, a madadin Oceangate Engineering Oil and Gas Limited, ya tura jimillar dala miliyan 7 zuwa asusun Gwamnatin Tarayya.

Ya ce sun samu shaidar cewa waɗannan mu’amaloli ne ta Bankin Providus daga Babban Bankin Nijeriya (CBN) ta wata wasiƙa mai kwanan wata 24 ga Yuni, 2025.

Ya ce tsakanin 20 ga Maris, 2025 zuwa 3 ga Afrilu, 2025, kamfanin ya biya dala miliyan 20 ga Gwamnatin Tarayya domin sayen rijiyoyin mai masu lamba PPL 302 da PPL 3007.

Jami’in ya zargi cewa domin cika buƙatun biyan kuɗin shigar ciniki (signature bonus) na PPL 302 da PPL 3007, Oceangate ta haɗa baki da ’yan canjin kuɗi marasa lasisi da wasu jami’an banki, inda aka riƙe kuma aka tura dala miliyan 13 da ake zargin an same su ta haramtacciyar hanya ne.

Ya ce an yi amfani da wani Suleiman Muhammed Chiroma, wanda Oceangate ta taimaka masa, ya karɓi dala miliyan 13 a tsabar kuɗi ta hannun abokan aikin sa a Abuja da Legas, ba tare da bi ta hanyar wata cibiyar kuɗi ba.

Ya ce Chiroma, tare da Ɗantani Abubakar Hassan na Ashrab Energy and Oil Services Limited da Tirmizi Muhammed Usman na Tripple A & Tee Oil Nigeria Limited, sun karɓi dala miliyan 9 tsabar kuɗi domin biyan kuɗin shigar ciniki na rijiyoyin man biyu.

Aliyu ya ƙara da cewa an karɓi kuɗaɗen da ake zargin an same su ta haramtacciyar hanya ne daga wajen wasu ’yan kwangila na Gwamnatin Jihar Legas, ta asusun Ashrab Energy a Bankin Zenith da Bankin Access, inda aka karɓi N855,057,560.00 da kuma N2,455,651,560.00, aka mayar da su daloli sannan aka tura su zuwa asusun Oceangate.

Ya ce dala miliyan 13 da aka yi amfani da su wajen biyan kuɗin shigar cinikin ba su fito daga wata halastacciyar harkar kasuwanci ta Oceangate ba.

A martanin sa, kamfanin Oceangate, a wata rantsuwar nuna dalili da daraktan sa Iliya Wakil ya yi, ya roƙi kotu da kada ta bayar da umurni na ƙarshe na ƙwace kuɗin, yana mai cewa kuɗin sun fito ne daga halastacciyar riba da kuma kyaututtuka da aka bai wa Babbar Shugabar kamfanin, wato Dakta Aisha Achimugu.

Kamfanin ya ƙaryata dukkan zarge-zargen EFCC, yana mai cewa Suleiman Chiroma halastaccen ɗan canji ne mai lasisi, kuma kamfanin bai san Ɗantani Hassan ko Tirmizi Usman ba.

EFCC ta roƙi kotu da ta ƙi amincewa da buƙatar Oceangate, tana mai cewa Iliya Wakil darakta ne kawai a suna, bai da hannun jari a kamfanin, kuma yana karɓar umurni kai-tsaye daga Achimugu.

Aliyu ya bayyana Oceangate a matsayin “kamfani na takarda” wanda aka ƙirƙira domin riƙe kadarorin man fetur da aka saya da kuɗaɗen da ake zargin sun fito ne daga haramtacciyar hanya.

Ya ce a maslahar adalci da manufofin jama’a ne a ƙwace dala miliyan 13 zuwa Gwamnatin Tarayya.

Kamfanin NAN ya kuma ruwaito cewa a ranar 15 ga Satumba, 2025, kotu ta riga ta bayar da umurnin ƙarshe na ƙwace dala miliyan 7 da aka samu a Bankin Providus, Ikoyi, Legas, bayan babu wanda ya fito ya ce kuɗin nasa ne.

Daga baya, kamfanin Felak Concept Group Limited ya fitar da sanarwa yana ƙaryata rahotannin da ke alaƙanta shugabar sa, wato Achimugu, da reshen kamfanin, Oceangate Engineering Oil and Gas Ltd, da mu’amalar tsabar kuɗin dala miliyan 7 da ake ce-ce-ku-ce a kai.

Tags: AishaAchimuguFelakConceptGroupMaiShari'aEmekaNwiteOceangateLtd
Previous Post

Gwamnatin Tarayya ta buƙaci haɗin kai domin ƙarfafa martabar Nijeriya a idon duniya

Next Post

Muhimman Shawarwarin Tsaro Ga Magidanta Da Iyalai

Related Posts

EFCC ta kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Nijeriya, Mustapha Abdullahi, kan zargin zambar naira biliyan 500
Labarai

EFCC ta kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Nijeriya, Mustapha Abdullahi, kan zargin zambar naira biliyan 500

May 13, 2026
Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista
Tsaro

Nijeriya ta sha alwashin sabunta rundunonin sojin ta ta hanyar haɗin gwiwa da bunƙasa ƙwarewar cikin gida – Minista

May 13, 2026
Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75
Labarai

Zambar naira biliyan 33.8: Kotu ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75

May 13, 2026
Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu
Ilimi

Za a riƙa yi wa ɗaliban makarantun sakandare gwajin tilas na ƙwayoyi daga yanzu

May 11, 2026
An kama Bello Boɗejo, shugaban Fulani Kuma ɗan takarar kujerar Sanata na APC a Taraba
Siyasa

An miƙa ɗan takarar Sanata kuma shugaban Fulani, Bello Boɗejo ga EFCC

May 10, 2026
Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka
Tsaro

Ribaɗu da JD Vance sun gana don ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka

May 9, 2026
Next Post
Muhimman Shawarwarin Tsaro Ga Magidanta Da Iyalai

Muhimman Shawarwarin Tsaro Ga Magidanta Da Iyalai

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!