• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Tinubu ya yi jimamin rasuwar limamin da ya ceci Kiristoci sama da 200 a Filato

ALI KANO by ALI KANO
January 16, 2026
in Labarai
A A
0
Tinubu ya yi jimamin rasuwar limamin da ya ceci Kiristoci sama da 200 a Filato
Babban Limamin ƙauyen Nghar da ke Ƙaramar Hukumar Barkin Ladi a Jihar Filato, Abdullahi Abubakar. (Hoto: Bayo Onanuga)

Babban Limamin ƙauyen Nghar da ke Ƙaramar Hukumar Barkin Ladi a Jihar Filato, Abdullahi Abubakar. (Hoto: Bayo Onanuga)

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bayyana matuƙar alhini kan rasuwar Limam Abdullahi Abubakar, Babban Limamin ƙauyen Nghar a Ƙaramar Hukumar Barkin Ladi ta Jihar Filato, wanda ya rasu yana da shekaru 92.

Marigayi Liman Abubakar ya samu shahara ne a cikin gida da ƙasar waje a shekarar 2018, bayan da ya bai wa Kiristoci sama da 200 mafaka a lokacin rikice-rikicen ƙabilanci da na addini da suka addabi wasu sassan Jihar Filato.

A cikin saƙon ta’aziyya da kakakin sa Bayo Onanuga ya wallafa a shafin X a yau Juma’a, Tinubu ya bayyana limamin a matsayin shugaban addini na musamman, wanda rayuwar sa ta kasance shaida mai ƙarfi ta imani, jarumtaka, da tsarkin rayuwar ɗan’adam.

Ya ce: “A irin wannan lokaci da rikicin ƙabila da addini suka kusan rinjayar hankali, Liman Abubakar ya tsaya daram a ɓangaren zaman lafiya, kyautatawa, da nagartar lamiri.”

Shugaban Ƙasar ya lura da cewa duk da babbar barazanar da ke fuskantar rayuwar sa, limamin ya zaɓi tausayi maimakon rarrabuwar kai, da ƙauna maimakon ƙiyayya.

“Ba tare da la’akari da babban haɗarin da ya jefa kan ran sa ciki ba, wannan limami mai daraja ya zaɓi jinƙai maimakon rarrabuwar kai, ƙauna maimakon ƙiyayya, da rungumar juna maimakon ƙin karɓa.

“Jarumtar da ya nuna ta fayyace ainihin ma’anar sahihin imani, wadda ta fi wa’azi ƙarfi wajen isar da saƙo mai muhimmanci ga duniya baki ɗaya,” inji Tinubu.

A cewar Shugaban Ƙasar, ayyukan Liman Abubakar sun nuna irin ɗabi’ar jinƙai da ƙarfin gwiwar ɗabi’a da ya kamata al’umma su yi koyi da su.

Ya ƙara da cewa jarumtar limamin ba ta tafi a banza ba, domin ya samu lambobin yabo na cikin gida da na ƙasar waje, sakamakon jajircewar sa wajen ƙarfafa zaman tare cikin lumana tsakanin mutane masu addinai da asali daban-daban.

Tinubu ya yi kira ga shugabannin addini da na al’umma a faɗin ƙasar nan da su yi koyi da marigayi limamin, ta hanyar inganta haƙuri, mutunta juna, da zaman lafiya.

Ya ce: “Ina kira ga shugabannin addini da na al’umma da su rungumi zaman tare da wa’azin ruhin haƙuri, mutunta juna, da zaman tare cikin lumana, kamar yadda rayuwar Liman Abubakar ta nuna.”

Shugaban Ƙasar ya yi addu’ar Allah ya jikan sa, tare da roƙon Allah ya saka masa da alheri bisa jarumtaka da kyawawan ayyukan sa.

“Allah Maɗaukakin Sarki ya ba Liman Abubakar hutu na har abada, kuma ya saka masa da alheri bisa kyawawan ayyukan sa da jarumtaka,” inji Tinubu.

Tags: BarkinLadiBayoOnanugaFilatojimamiLimanAbdullahiAbubakarNgharrasuwaShugabaBolaTinubuta'aziyya
Previous Post

Tinubu yana kafa ginshiƙin cigaba mai ɗorewa tare da inganta rayuwar jama’a, inji Ministan Yaɗa Labarai

Next Post

Gwamnatin Tarayya ta taya Super Eagles murna bisa samun lambar tagulla a gasar AFCON

Related Posts

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura
Labarai

Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura

November 25, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa
Labarai

Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa

November 24, 2026
Next Post
Gwamnatin Tarayya ta taya Super Eagles murna bisa samun lambar tagulla a gasar AFCON

Gwamnatin Tarayya ta taya Super Eagles murna bisa samun lambar tagulla a gasar AFCON

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!