• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Tinubu ya sauka Abu Dhabi don halartar taron ADSW 2026

Wakilin Mu by Wakilin Mu
January 11, 2026
in Labarai
A A
0
Tinubu ya sauka Abu Dhabi don halartar taron ADSW 2026
Ministan Harkokin Wajen UAE, Sheikh Shakhboot Nahyan Al Nahyan, tare da sauran jami'ai suna tarbar Shugaban Ƙasa Tinubu a filin jirgin sama na Abu Dhabi a daren yau

Ministan Harkokin Wajen UAE, Sheikh Shakhboot Nahyan Al Nahyan, tare da sauran jami'ai suna tarbar Shugaban Ƙasa Tinubu a filin jirgin sama na Abu Dhabi a daren yau

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya isa birnin Abu Dhabi na ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) a daren yau Lahadi domin halartar taron Abu Dhabi Sustainability Week (ADSW) na 2026, wanda zai fara gobe.

Jirgin Shugaban Ƙasar ya sauka a Sashen Shugaban Ƙasa na Filin Jirgin Sama na Zayed da misalin ƙarfe 11:30 na dare agogon Dubai.

Ministan Harkokin Wajen UAE, Sheikh Shakhboot Nahyan Al Nahyan, tare da Jakaden UAE a Nijeriya, Salem Saeed Al-Shamsi, da Ministan Harkokin Wajen Nijeriya, Jakada Yusuf Maitama Tuggar, da kuma jami’an ofishin jakadancin Nijeriya a Abu Dhabi su ne suka tarbe shi.

Haka kuma, wasu ministoci da suka haɗa da Ministan Kasafi da Tsare-tsare, Atiku Bagudu; Ministan Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari, Dakta Jumoke Oduwole, da Darakta-Janar na Hukumar Leƙen Asiri ta Ƙasa (NIA), Jakada Muhammed Muhammed, sun tarbi Shugaban Ƙasar a otal ɗin sa.

Shugaba Tinubu tare da jami’an UAE bayan saukar sa a ƙasar

Kafin isar sa Abu Dhabi, Tinubu ya shafe wani ɓangare na hutun ƙarshen shekara a Turai, inda ya yi muhimman tattaunawa da Shugaban Ruwanda, Paul Kagame, da Shugaban Faransa, Emmanuel Macron.

Taron ADSW 2026, mai taken “The Nexus of Next, All Systems Go”, dandali ne na duniya da ke haɗa shugabanni, masu tsara manufofi, masu zuba jari da ƙwararru domin tattaunawa da ɗaukar matakai kan cigaba mai ɗorewa, yaƙi da sauyin yanayi, sauya tsarin makamashi da bunƙasa tattalin arziki da ya haɗa kowa da kowa.

Ziyarar ta ƙara jaddada kyakkyawar alaƙar diflomasiyya da tattalin arziki da ke tsakanin Nijeriya da UAE, tare da nuna matsayar Nijeriya a matsayin ƙasa mai taka rawa a tattaunawar duniya kan cigaba mai ɗorewa.

Tags: Abu DhabiADSW 2026Sheikh Shakhboot Nahyan Al NahyanShugaba Bola Ahmed TinubuUAE
Previous Post

‘Harajin Hajji’: Gwamnatin Tarayya za ta iya samun ₦5.4bn daga alhazai a bana

Next Post

Shari’ar cin hanci ta Malami ta fara ne tun kafin a naɗa ni shugaban EFCC, inji Olukoyede

Related Posts

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura
Labarai

Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura

November 25, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa
Labarai

Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa

November 24, 2026
Next Post
Shari’ar cin hanci ta Malami ta fara ne tun kafin a naɗa ni shugaban EFCC, inji Olukoyede

Shari’ar cin hanci ta Malami ta fara ne tun kafin a naɗa ni shugaban EFCC, inji Olukoyede

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!