Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya, ta hanyar kamfanin Ministry of Finance Incorporated (MOFI), a yau ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da Gwamnatin Jihar Neja domin fara gwajin shirin Sustainable Integrated Productive Communities (SIPC).
Wannan shiri wata manufa ce da ke haɗa gina gidaje masu yawa, aikin noma, makamashi mai sabuntawa da bunƙasa kasuwanci a cikin tsari guda mai iya faɗaɗa domin bunƙasar tattalin arziki na kowa da kowa.
An sanya hannu kan yarjejeniyar ne a Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya da ke Abuja, inda ma’aikatar ke zama cibiyar jagora, yayin da MOFI ke bayar da tallafin inganta kadarori da kuma jawo jarin kamfanoni masu zaman kan su.
Wata sanarwa daga ma’aikatar ta ce shirin “yana wakiltar tabbataccen mataki wajen magance matsalolin samar da abinci, gidaje masu sauƙin samu, zaman lafiya a karkara da samar da ayyukan yi.”
Da take jawabi a wajen bikin, Ƙaramar Ministar Kuɗi, Daktq Doris Uzoka-Anite, ta bayyana yarjejeniyar a matsayin “lokacin aiwatarwa, ba wai bikin al’ada kawai ba,” kuma ta jaddada cewa shirin SIPC na nuna yadda manyan manufofin ƙasa za su iya zama sakamako na zahiri ta hanyar haɗin gwiwa mai ƙarfi tsakanin tarayya da jihohi.
Ta ce: “Wannan haɗin gwiwa yana nuna imanin mu cewa cigaba ya fi tasiri idan gina gidaje, aikin noma, kuɗi da shugabanci suna tafiya tare.
“Ta hanyar tsayar da manoma a cikin tsare-tsaren al’umma masu tsaro da tsari, ba wai gidaje kawai muke ginawa ba. Muna ƙarfafa hanyoyin rayuwa, samar da abinci da bunƙasa ƙasa ta dogon lokaci.”
Sanarwar ta nuna cewa a ƙarƙashin shirin, Jihar Neja za ta karɓi matakin gwaji na gonaki da gidaje masu haɗaka, waɗanda aka tsara domin bai wa manoma matsuguni masu tsaro kusa da wuraren noma, wuraren ajiya, sarrafawa da kasuwanni.
Tsarin zai magance tsofaffin matsaloli kai-tsaye kamar rashin tsaron matsugunan karkara, ƙaura daga karkara zuwa birane, asarar amfanin gona bayan girbi, da ƙarancin shigar matasa harkar noma.
Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, wanda ya halarci bikin, ya sake jaddada ƙudirin gwamnatin sa na goyon bayan shirin, yana nuna yalwar ƙasar noma, albarkatun ruwa da muhimman kayayyakin more rayuwa da jihar ke da su.
Ya bayyana cewa shirin zai taimaka wajen inganta tsaro, jurewar sauyin yanayi, da tsari mai kyau na bunƙasa al’ummomin karkara, tare da samar da ingantattun damarmakin tattalin arziki ga manoma.

Shirin SIPC yana amfani da sabon tsarin kuɗaɗen aiwatarwa da ke haɗa ƙasar gwamnati da kadarorin ta da jarin masu zaman kan su. Wannan yana bai wa gwamnati damar mai da hankali kan tsara manufofi, daidaitawa da sa ido, yayin da ake cin gajiyar ƙwarewa da girman aiki na kamfanoni masu zaman kan su.
Rawar MOFI tana da matuƙar muhimmanci a wannan tsari, wajen tabbatar da gaskiya, ɗorewa da raba haɗarin aiki tsakanin abokan hulɗa.
Manyan hukumomin Tarayya da ke cikin shirin sun haɗa da Family Homes Funds Limited, Rural Electrification Agency, da kima Niger Foods Limited, kowannen su yana bayar da ƙwarewa ta musamman a fannonin gina gidaje masu araha, hanyoyin makamashi mai sabuntawa, da bunƙasa sarkar darajar noma.
Makamashi mai sabuntawa—musamman na hasken rana don gine-ginen al’umma da ƙananan grid—zai tallafa wa sarrafa amfanin gona, ajiya da buƙatun makamashi na gidaje, yana rage farashi da ƙara yawan aiki.
Baya ga noma, ana sa ran shirin zai motsa faɗaɗɗun ayyukan tattalin arziki ta fannoni kamar gini, jigilar kaya, sarrafa amfanin gona da ayyukan al’umma, tare da samar da ayyukan yi ga injiniyoyi, masu sana’a, magina da masu samar da kayayyaki, da kuma tallafa wa masana’antu na cikin gida kamar siminti, ƙarfe da sufuri.
An tsara matsugunan ne a sarari domin su kasance masu araha da amfani, tare da hanyoyin rabon gidaje masu gaskiya da tsarin shugabanci da zai tabbatar da damar samun su ga manoma da masu ƙaramin zuwa matsakaicin ƙarfi na samun kuɗi.
Sanarwar ta ƙara da cewa: “Rattaba hannu kan yarjejeniyar ya aika da saƙo bayyananne ga magina, cibiyoyin kuɗi, asusun fansho, masu zuba jari a harkar noma da abokan cigaba cewa Jihar Neja, tare da Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya da MOFI, a buɗe take ga ingantaccen zuba jari mai tasiri.
“Tsarin SIPC an yi niyyar ya zama abin koyi na ƙasa baki ɗaya da za a iya maimaitawa wajen bunƙasa karkara da yankunan gefen birane.
“Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya ta sake jaddada ƙudirin ta na tabbatar da cewa yarjejeniyar za ta wuce matakin sa hannu zuwa aiwatarwa cikin gaggawa, tare da haɗin kai na dukkan masu ruwa da tsaki domin samar da sakamako a fannoni na gidaje, tsaron abinci, ayyukan yi da bunƙasar tattalin arziki mai haɗa kowa da kowa.”







