• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Za mu zurfafa haɗin gwiwa da ƙasashen duniya domin murƙushe barazanar tsaro a 2026 – Tinubu

Wakilin Mu by Wakilin Mu
January 1, 2026
in Labarai
A A
0
Za mu zurfafa haɗin gwiwa da ƙasashen duniya domin murƙushe barazanar tsaro a 2026 – Tinubu
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta ƙara zurfafa haɗin gwiwa da ƙasashen yankin da na duniya a shekarar 2026 domin kawar da dukkan barazanar tsaro da ke barazana ga rayuka, dukiyoyi da kuma cikakken ikon ƙasar Nijeriya.

Shugaban ya bayyana hakan ne a jawabin saƙon sabuwar shekarar 2026 da ya gabatar ga ’yan Najeriya a yau Alhamis.

Tinubu ya ce tafarkin gyara ƙasar nan ba abu ne mai sauƙi ba, amma wajibi ne, yana mai jaddada cewa cigaban tattalin arziki ba zai yi armashi ba tare da tsaro da zaman lafiya ba.

Ya ce Nijeriya tana ci gaba da fuskantar barazanar ’yan ta’adda da masu aikata laifuffuka da ke ƙoƙarin dagula zaman lafiyar ƙasa, amma gwamnati na ɗaukar matakan da suka dace domin daƙile su.

Shugaban ya bayyana wasu hare-hare da aka kai kwanan nan tare da haɗin gwiwar abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa, ciki har da Amurka, domin raunana ƙungiyoyin ta’addanci.

A cewar sa, “A cikin haɗin gwiwa da abokan hulɗa na duniya, ciki har da Amurka, an ɗauki matakai masu ƙarfi kan wuraren ’yan ta’adda a wasu sassan Arewa-maso-yamma a ranar 24 ga Disamba.”

Ya ƙara da cewa rundunonin tsaro na ci gaba da kai farmaki kan sansanonin ’yan ta’adda da ’yan fashi a yankunan Arewa-maso-yamma da Arewa-maso-gabas.

Tinubu ya bayyana cewa a 2026 hukumomin tsaro da na leƙen asiri za su ƙara ƙarfafa musayar bayanai da daidaita ayyuka da abokan hulɗa na yankin da na duniya domin kawar da duk wata barazana ga tsaron ƙasa.

Ya sake jaddada ƙudirin Gwamnatin Tarayya na kare rayuka, dukiyoyi da cikakken ikon ƙasar Nijeriya.

Game da gyaran tsarin tsaro, shugaban ya nuna goyon bayan sa ga tsarin ’yan sanda na jihohi, tare da tanadin kariya da tsarin kula da masu tsaron dazuzzuka cikin tsari da ɗa’a ga doka.

A ɓangaren tattalin arziki, Tinubu ya ce sabuwar shekarar za ta kawo wani sabon babi na bunƙasar tattalin arziki mai faɗi, wanda zai shafi rayuwar talakawa kai-tsaye.

Ya bayyana cewa za a hanzarta aiwatar da shirin Renewed Hope Ward Development Programme da nufin shigar da aƙalla ’yan Nijeriya miliyan 10 cikin ayyukan samar da arziki.

A cewar sa, shirin zai bai wa aƙalla mutane 1,000 a kowace daga cikin unguwanni 8,809 na ƙasar nan damar samun aikin yi da dogaro da kai ta fannoni kamar noma, kasuwanci, sarrafa abinci da ma’adinai.

Shugaban ya kuma tabbatar da cewa dukkan manyan ayyukan more rayuwa da ake yi a halin yanzu za su ci gaba ba tare da tsaiko ba.

Tinubu ya buƙaci ’yan Nijeriya da su fahimci cewa gina ƙasa alhakin kowa ne, tare da ba da gudunmawar sa domin cimma manufofin 2026.

A ƙarshe, ya yi addu’ar samun zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali a ƙasar, yana mai fatan Allah ya kare ƙasa, ya kiyaye sojoji, tare da hallaka duk masu ƙoƙarin tayar da zaune tsaye.

Shugaban ya yi wa ’yan Nijeriya fatan samun sabuwar shekara mai albarka, zaman lafiya da cigaba.

Tags: Sabuwar ShekarasaƙoShugaba Bola Ahmed Tinubu
Previous Post

Tattalin arzikin Nijeriya ya ƙara ƙarfi a watan Disamba, yayin da malejin hadahadar kamfanoni da masana’antu ya kai maki 57.6 – CBN

Next Post

Isra’ila tana aiki kan wani shiri na tallafa wa Kiristocin Nijeriya, in ji Netanyahu

Related Posts

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura
Labarai

Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura

November 25, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa
Labarai

Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa

November 24, 2026
Next Post
Isra’ila tana aiki kan wani shiri na tallafa wa Kiristocin Nijeriya, in ji Netanyahu

Isra’ila tana aiki kan wani shiri na tallafa wa Kiristocin Nijeriya, in ji Netanyahu

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!