Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bar Legas a yau, 28 ga Disamba, zuwa Turai, domin ci gaba da hutun sa na ƙarshen shekara, kafin tafiyar sa ta aiki zuwa Abu Dhabi a Ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE).
Wata sanarwa ga manema labarai da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya fitar ta ce Shugaban Ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan, ya gayyaci Tinubu domin halartar taron Abu Dhabi Sustainability Week (ADSW 2026), wanda za a gudanar a farkon watan Janairu a birnin Abu Dhabi.
Taron na tsawon mako guda ana shirya shi duk shekara, kuma yana haɗa shugabanni daga gwamnati, kasuwanci da al’umma domin tsara sabuwar hanyar cigaba mai ɗorewa.
Da taken, “The Nexus of Next: All Systems Go”, taron na ADSW zai haɗa buri da aiki ta fannonin ƙirƙira, kuɗi da mutane, tare da nuna yadda duniya za ta iya ci gaba gaba da gaba da ƙwarin gwiwa.
Shugaban Tinubu zai dawo gida bayan kammala taron.







