Fatima Buhari, ‘yar marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ta bayyana dalilin da ya sa mahaifin ta ya kasa nesanta kan sa daga ɗan’uwan sa kuma tsohon abokin sa na dogon lokaci, Malam Mamman Daura, duk da cewa ana kukan tasirin Daura a mulkin sa.
Ta bayyana ra’ayin ta a cikin sabon littafin tarihin Buhari mai taken From Soldier to Statesman: The Legacy of Muhammadu Buhari, wanda Dakta Charles Omole, Darakta-Janar na Cibiyar Bincike kan Manufofin ‘Yan Sanda da Tsaro (Institute for Police and Security Policy Research (IPSPR), ya rubuta. An ƙaddamar da littafin a Abuja ranar Litinin.
A cewar Fatima, alaƙar da ke tsakanin Buhari da Mamman Daura ta wuce siyasa kawai, an gina ta ne bisa zumunci, abubuwan da suka sha tare, da amincewa da aka gina tsawon shekaru da dama; tun daga zamanin su a Fadar Dodan Barracks har zuwa shekarun Buhari a Fadar Shugaban Ƙasa.
Ta bayyana cewa dangantakar iyali ta kasance mai matuƙar ƙarfi, inda ta lura da cewa mahaifin Mamman Daura da na Buhari uwar su ɗaya.
“Mahaifin Mamman Daura da mahaifi na uwar ɗaya,” inji ta.
Fatima ta bayyana dangantakar a matsayin wadda kusanci da takaici suke tafiya tare.
Ta ce Buhari sau da dama yana sane da koke-koken da ake yi game da Mamman Daura da kuma rikice-rikicen da suke haifarwa, amma yana ganin yana da wahala ya yanke alaƙar sa da shi gaba ɗaya.

Ta ce: “Baba yakan faɗa mana da kan sa cewa ya yi masa kaza, ya yi masa kaza, amma har yanzu yana tare da shi.”
Littafin ya kuma bayyana cewa Mamman Daura ya ci gaba da kasancewa kusa da Buhari har lokacin da aka tsare shi bayan juyin mulkin soja na 1985.
Fatima ta ce, duk da cewa an hana ‘yan’uwa ganin Buhari a wancan lokaci, Daura yana da damar shiga a kai a kai.
“Ba a ba mu damar ganin sa ba. Mamman kaɗai ke da damar shiga. Ina ta tambayar kai na, ‘Me ya sa Mamman ne kullum a tsakanin Baba da iyali?’”
Ta ce amsar tambayar tana cikin nauyin zumunci mai ƙarfi, tarihin rayuwa da suka yi tare tsawon shekaru, godiya, da kuma tsananin biyayyar Buhari ga waɗanda ya amince da su.
Sai dai Fatima ta amince cewa wannan kusanci ya haifar da mummunan sakamako.
Ta ce wasu mutane sun yi amfani da rashin son Buhari na kunyatawa, cutarwa ko fallasa mutane a bainar jama’a.
Littafin ya kuma nuna cewa halayen Buhari na mutum ɗaya sun yi tasiri a kan shawarwarin sa.
Fatima ta ce yayin da yake ƙara tsufa da kuma ƙara addini, ya zama mai laushi da kuma taka-tsantsan wajen katse alaƙa da mutane.
“Yana fahimtar gungu-gungun alaƙa; iyaye, ma’aurata, tarihi, kuma ba ya son karya fata,” inji ta.
Ta ƙara da cewa idan Buhari ya amince maka, yana da matuƙar wahala ya janye wannan amincewar sai da hujja mai ƙarfi. Ko da akwai hujjoji, ta ce ya fi son gyara a asirce da gargaɗi a ɓoye maimakon kora a bainar jama’a.
“Kafin ya ankara, wannan mutum ya riga ya aikata munanan laifuka da yawa,” inji ta.
Ta ƙara da cewa ko da yake Buhari a wasu lokuta yana fuskantar mataimakan sa da tsauri, ba ya jin daɗin wulaƙanta mutane.







