• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Tinubu ya yabi sojojin Nijeriya kan kare dimokiraɗiyya a Benin

Wakilin Mu by Wakilin Mu
December 7, 2025
in Labarai
A A
0
Tinubu ya yabi sojojin Nijeriya kan kare dimokiraɗiyya a Benin
NAF

NAF

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya jinjina wa rundunar sojin ƙasar bisa gaggawar da ta yi wajen amsa kiran gwamnatin Jamhuriyar Benin domin taimakawa wajen kare tsarin mulkin su na dimokiraɗiyya, bayan yunƙurin juyin mulki da aka yi a ƙasar a safiyar Lahadi.

A cewar fadar shugaban ƙasa, gwamnatin Benin ta aika wa Nijeriya da buƙatu biyu na gaggawa, ta hanyar Ma’aikatar Harkokin Wajen ƙasar, tana neman a turo da jiragen yaƙin saman Nijeriya domin ƙwace tasoshin da sojojin da suka yi juyin mulkin suka mamaye, ciki har da talbijin na ƙasa da kuma wani sansanin soja.

Nijeriya ta amsa wannan kira nan take, inda Shugaba Tinubu ya umarci rundunar sojin sama ta NAF ta shiga sararin samaniyar Benin domin kawar da barazanar.

Haka kuma gwamnatin Benin ta roƙi a tura ƙarin jiragen leƙen asiri da sojojin ƙasa na Nijeriya domin su taimaka masu a ayyukan tsaro da kariyar manyan cibiyoyin gwamnati a ƙarƙashin jagorancin hukumomin tsaron Benin.

Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Nijeriya, Janar Olufemi Oluyede, ya tabbatar da cewa an kammala dukkan buƙatun da Benin ta nema, ciki har da zuwan sojojin Nijeriya cikin ƙasar.

Yunƙurin juyin mulkin dai ya faru ne bayan wasu sojoji ƙarƙashin jagorancin Kanar Pascal Tigri suka mamaye gidan talbijin na ƙasar, inda suka bayyana cewa sun hamɓarar da gwamnatin Shugaba Patrice Talon tare da dakatar da muhimman hukumomin dimokiraɗiyya.

Sai dai da taimakon dakarun Nijeriya, jami’an gwamnati masu biyayya ga Shugaba Talon sun ƙwace tashar talbijin ɗin da sauran wuraren da aka mamaye, lamarin da ya kawo ƙarshen yunƙurin juyin mulkin.

Da yake martani bayan tabbatar da dawowar tsarin dimokiraɗiyya, Tinubu ya yaba wa sojojin Nijeriya bisa rawar da suka taka.

Ya ce: “A yau, rundunar sojin Nijeriya ta tsaya kai da fata wajen kare tsarin mulki a Jamhuriyar Benin bisa gayyatar gwamnatin ƙasar. Sun yi aiki bisa ƙa’idojin yarjejeniyar ECOWAS kan dimokiraɗiyya da kyakkyawan mulki.”

Ya ƙara da cewa Nijeriya za ta ci gaba da goyon bayan gwamnati da al’ummar Benin wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Tags: Benindimokiraɗiyyajuyin mulkiShugabaBolaTinubusojoji
Previous Post

Taron IILM na 35: Yadda CBN ya gudanar da taron kwamitin gudanarwar manyan bankunan ƙasashe takwas

Next Post

Amfani da ‘yan sa-kai a harkar tsaro yana ƙara yawaitar yaɗuwar ƙananan makamai a Nijeriya, cewar Kwankwaso

Related Posts

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura
Labarai

Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura

November 25, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa
Labarai

Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa

November 24, 2026
Next Post
Amfani da ‘yan sa-kai a harkar tsaro yana ƙara yawaitar yaɗuwar ƙananan makamai a Nijeriya, cewar Kwankwaso

Amfani da 'yan sa-kai a harkar tsaro yana ƙara yawaitar yaɗuwar ƙananan makamai a Nijeriya, cewar Kwankwaso

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!