• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Sojoji sun ceto ‘yan mata 12 da aka sace a Borno

Wakilin Mu by Wakilin Mu
November 30, 2025
in Labarai
A A
0
Sojoji sun ceto ‘yan mata 12 da aka sace a Borno
'Yan matan tare da sojojin da suka ƙwato su

'Yan matan tare da sojojin da suka ƙwato su

Rundunar Sojojin Nijeriya ta ceto wasu ‘yan mata 12 da ‘yan Boko Haram/ISWAP suka sace a yankin Mussa da ke Ƙaramar Hukumar Askira/Uba, a Jihar Borno.

‘Yan matan, masu shekaru tsakanin 15 da 20, an sace su ne a ranar 23 ga Nuwamba yayin da suke aikin girbi a gonakin iyayen su.

Sanarwar rundunar ta ce an ceto su ne a jiya Asabar ta hanyar wani gagarumin samame na musamman da rundunar Operation Haɗin Kai ta ƙaddamar a kudancin Borno.

A cewar rundunar, an kwashe waɗanda aka ceto zuwa wata cibiyar tsaro ta musamman domin duba lafiyar su kafin a miƙa su ga iyayen su.

Wani sashe na ‘yan matan

Sunayen waɗanda aka ceton da shekarun su sun ne: Fatima Shaibu (17), Fatima Umaru (15), Hauwa Abubakar (18), Saliha Muhammed (15), Sadiya Umaru (17), Amira Babel (15), Zara Adamu (17), Nana Shaibu (15), Zainab Musa (18), Zainab Muhammed (17), Jamila Saidu (15) da Hauwa Hamidu (17).

Hedikwatar Tsaro ta yaba wa dakarun ta masu jajircewa bisa gaggawar ɗaukar matakin da ta yi, tare da nuna godiya ga jama’a da masu ba da bayanan sirri da suka taka rawar gani wajen ganin an kuɓutar da waɗanda aka sace.

Sojojin na ci gaba da farautar ragowar ’yan ISWAP a yankin domin hana sake kai hare-hare da kare rayukan fararen hula.

Rundunar ta kuma ƙara kira ga jama’a da su ci gaba da ba da sahihan bayanai da wuri domin taimaka wa yaƙi da ta’addanci a yankin.

Tags: Askira-UbaBornocetosace matasojoji
Previous Post

CBN ya umurci bankuna su janye tallace-tallace masu ɗauke da ninanci da yaudarar kwastomomi

Next Post

Yadda CBN ya ceto tattalin arzikin Nijeriya cikin shekaru biyu – Cardoso

Related Posts

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura
Labarai

Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura

November 25, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa
Labarai

Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa

November 24, 2026
Next Post
Yadda CBN ya ceto tattalin arzikin Nijeriya cikin shekaru biyu – Cardoso

Yadda CBN ya ceto tattalin arzikin Nijeriya cikin shekaru biyu - Cardoso

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!