• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya umurci bankuna su janye tallace-tallace masu ɗauke da ninanci da yaudarar kwastomomi

Wakilin Mu by Wakilin Mu
November 29, 2025
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
CBN ya tashi haiƙan: Malejin farashin kayayyaki ya ƙara yin ƙasa zuwa kashi 16.05, yayin da asusun kuɗaɗen waje ya kai dala biliyan 46.7
Babban Bankin Nijeriya (CBN)

Babban Bankin Nijeriya (CBN)

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya yi kakkausan gargaɗi tare da umurtar dukkan bankuna, bankunan asusun ‘walet’ na biyan kuɗi da sauran cibiyoyin hadahadar kuɗi da yake kula da su, da cewa su gaggauta janye duk wasu tallace-tallace ko wasu bayanai da ba su cika ƙa’idojin kare buƙatu da haƙƙin kwastomomi bisa tsarin ingantacciyar hanyar tallata kaya ba.

CBN ya bada wannan umurni a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Alhamis kuma Olubunmi Ayodele-Oni ya sanya wa hannu a madadin Daraktan Sashen Bin Doka na CBN.

Umurnin ya biyo bayan wani bincike na masana’antu da ya tabbatar da cewa akwai bambance-bambancen fassarar da cibiyoyi ke yi dangane da buƙatun bayyana bayani, gaskiya da ingantacciyar tallatawa bisa Ƙa’idodin Dokar Kare Mabuƙata ta 2019 da Jagororin Tallace-Tallace na 2000 ga Cibiyoyin Ajiya.

Babban Bankin ya ce binciken ya gano cewa har yanzu wasu cibiyoyi suna tallata bayanan da ke kauce fa’ida fiye da gaskiya, rashin bayyana muhimman bayanai, ɓoye haɗari ko amfani da bayanan kuɗi da ba a tantance ba.

CBN ya gargaɗi cewa irin waɗannan halaye na yaudarar kwastomomi suna ɓata gasa tsakanin bankuna da cibiyoyin kuɗi, kuma suna lalata amincin tsarin kuɗi.

Bankin ya jaddada cewa duk tallace-tallace dole ne su kasance na gaskiya masu ɗauke da cikakkun bayanai.

Sannan kuma ya haramta amfani da kalmomi masu kwatanta ninanci kai tsaye ko a kaikaice, misali, irin masu nuni da cewa “mu ne mafi”, “mun kowa”, ko kuma tallar da ke ɗauke ɓatanci ga wasu cibiyoyi.

Har yau dai, bankin ya haramta tallace-tallacen da ke amfani da tayin lashe kyauta da kaɗan-kaɗan ko zaɓen masu sa’a da sauran shirye-shiryen da ke tura mabuƙata su aukawa su shawarar zuba kuɗi ba tare da cikakkiyar fahimtar haɗarin da ke tattare da su ba.

A ƙarƙashin wannan sabuwar dokar bin tsare-tsaren, ya zama tilas bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi su tura cikakkiyar sanarwa ga CBN kafin a saki kowace talla ko wasu bayanan isar da saƙo.

Sanarwar ta ce: “Dole ne sanarwar ta ƙunshi tsawon lokacin tallar, cikakken abin da za a wallafa ko watsawa, mutanen da ake son tallar ta kai gare su da kuma yankunan da aka yi niyyar sakon ya kai, tare da tabbaci a rubuce mai ɗauke da cewa sashen bin doka da na shari’a sun amince.

“Haka kuma dole ne cibiyoyin su gabatar da hujja cewa samfurin da suke tallatawa ya samu amincewar CBN tun da farko.”

Bankin ya jaddada cewa wannan tsarin sanarwa ba yana nufin CBN ta amince da tallar ba, kuma har yanzu cibiyoyin kuɗi ne ke da cikakken alhakin tabbatar da bin doka da ƙa’idoji.

CBN ta umurci dukkan cibiyoyi su janye duk wata talla da ba ta cika ƙa’idoji ba nan take, tare da miƙa takardar tabbacin bin doka cikin kwanaki 30, wadda Shugaban Kamfani/Manajan Darakta, Babban Jami’in Bin Doka za su sanya wa hannu.

“Wannan takardar ta tabbatar da cewa dukkan tallace-tallace da dabarun yaɗa labarai na yanzu suna bin dokoki da ƙa’idodin da abin ya shafa,” inji sanarwar.

CBN ya kuma bayyana cewa daga watan Janairu 2026 zai gudanar da wani bincike na gaba domin tantance yadda bankuna da cibiyoyin hadahadar suka yi biyayya da umurnin.

“Za a ci tarar duk wata cibiyar da aka samu tana karya dokokin, bisa ga Dokar BOFIA ta shekarar 2020 da Ƙa’idodin Kare Haƙƙin Kwastomomi.”

CBN ya bayyana aniyar sa na ci gaba da inganta bin tsare-tsare na gaskiya, bayyananniyar hulɗa da gudanar da hulɗa a bayyane bisa kyakkyawar hanyar talla a tsarin kuɗi.

Tags: bankunaCBNkwastomomiyaudara
Previous Post

Cika Shekaru 25: Ministan Yaɗa Labarai ya jinjina wa tasirin ƙungiyar ActionAid cikin al’umma 

Next Post

Sojoji sun ceto ‘yan mata 12 da aka sace a Borno

Related Posts

Shirin daƙile harƙalla: Yadda CBN ke amfani da sashen bankaɗo kuɗaɗen da ake karkatarwa
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shirin daƙile harƙalla: Yadda CBN ke amfani da sashen bankaɗo kuɗaɗen da ake karkatarwa

May 3, 2026
Tinubu zai fara rangadin tsawon mako biyu zuwa Faransa, Kenya da Ruwanda
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu zai fara rangadin tsawon mako biyu zuwa Faransa, Kenya da Ruwanda

May 1, 2026
Himma dai CBN: Tinubu ya sheƙa wa Cardoso ruwan jinjina da yabo kan nasarorin sauye-sauyen tsarin kuɗi da shirin ƙara jarin bankuna
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Himma dai CBN: Tinubu ya sheƙa wa Cardoso ruwan jinjina da yabo kan nasarorin sauye-sauyen tsarin kuɗi da shirin ƙara jarin bankuna

May 1, 2026
Cikar wa’adin ƙarfafa jari: Yadda bankunan Nijeriya suka bazama tara Naira tiriliyan 4.6 a ƙoƙarin cika sharuɗɗan CBN
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Juyin Zamani: Yadda CBN ke ƙarfafa wa ɗalibai koyon ilmin sarrafa kuɗi, yayin da tattalin arziki ke sauyawa a zamanance 

April 30, 2026
Yadda asusun kuɗaɗen waje na Nijeriya zai cika maƙil, bayan CBN ya yi wa naira allurar ƙarin ƙarfin wujijjiga dala a tsakiyar kasuwa
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Yadda CBN ke ta ƙoƙarin daƙile malejin hauhawar farashi zuwa ƙasa da kashi 10 bisa 100

April 29, 2026
Gargaɗi, sharuɗɗa da wa’adin da CBN ya gindaya kan BVN don tsaurara matakan tsare kuɗaɗen kwastomomi a bankuna
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gargaɗi, sharuɗɗa da wa’adin da CBN ya gindaya kan BVN don tsaurara matakan tsare kuɗaɗen kwastomomi a bankuna

April 27, 2026
Next Post
Sojoji sun ceto ‘yan mata 12 da aka sace a Borno

Sojoji sun ceto 'yan mata 12 da aka sace a Borno

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!